Sashe 25
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
_________________________________________
Page 43 & 44
Anan kuma cikin kotu an yi zama na farko tare da karanta irin tuhumar da ake wa Sahid, amma ya'ki yadda da wannan tuhuma , yana sanar da kotu babu wata cin amana da zai iya aikatawa ko handuma ,wanda har zata yi sanadin mutuwar Kalisa.
Jibril da babarshi ko kotun ba su halatta ba , haka alkali ya d'age shari'ar zuwa wani lokaci, tare da ba da belin Sahid.
Hauwa ce kwance kan kafar Hajjiya.
Hajjiya ta ce ,"Wai yaushe ne Abdallaah zai dawo daga Germany zamanshi ne fa ya sa bikin ku har yau ba rana. "
Hauwa ta yi Murmushi tana cewa, "Ai momy ya kusan dawowa, shi ma ya damu ya dawo fa."
Hajjiya ta ce ,"Ai gara dai ayi -ayi a wuce gun."
Hauwa ta ce ,"Yawwa momy kinga ashe wannan yaron Harun, wanda abokina Mahmud ya yi magana a kan shi , har Surayya yaje gunta."
Hajjiya ta yi dariya tana cewa, "Tabbb amma wannan yaro ko d'anbanza, yanzu shi ina Mahmud din."
Hauwa ta ce ,"Ba ya nan , amma ya ce idan ya shigo gari zai zo ya gaida Dady."
Hajjiya ta ce ,"To Allah ya kawo shi."
A halin yanzu kowa yana ta magana masu gulma da yamad'd'i suna ta yi cewa Maryam yar Malam na lado ta yi cikin shege , daga wanda zasu zagi ta da iyayenta sai masu Allah ya kyauta da fatan shiriya.......
Musamman yadda abin ya yi tsamari da suka koma asubiti aka tabbatar musu tana da cuta mai karya garkuwar jiki , nan malam hankalin shi ya sake tashi , haka suma almajiran malam duk abin bai yi musu dadi ba.
Haka ita ma Zainab ta sami wannan labarin, kuma an tabbatar mata da Harun shi ne wanda ya aikata mata wannan abu.
Zainab ta shiga wani hali tana ta kuka , yayin data tuna Lokacin da Mahmud yake shirin rabata da Harun take masa wani kallo, har ya kai ta wulakantashi , haka ta ringa kuka tsawon yini guda tana nadama .
A Yanzu babu wanda take son ji da gani idan ba Mahmud ba , amma yadda ta ga ba ta da damar , ya sa hankalinta ya sake tashi , cikin kuka ta nufi wajen Hajjiya ta sanar da ita komai kuma ta roketa da ta 'kar'bo mata wayarta wajen Alaji.......
"Umma yau ne za a zaman kotu na biyu." Jibril ya sanar da mahaifiyar shi
cikin mummunan 'bacin rai ta kalleshi tana cewa, "To mene."?
" Ba komai. " Ya ba ta amsa
"Ni tsakanina da Sahid kawai Allah ne zai mana hisabi , idan ma kotu ta sake shi ya dawo gidan nan ya ci gaba da zama , amman a ranar gobe akwai tsaiwa tsakanina dashi da mahaifin sa."
Jibril ya yi ajiyar zuciya yana jinjina dajin tsoron maganar mahaifiyar tasu."
Anan cikin kotu Lauyoyi sai musayar hujjoji suke , domin lauyan Sahid ya yi iya yinshi , har ya ke son gamsar da kotu cewa Sahid sam ba mai laifi ba ne bai kuma aikata wannan tuhuma da ake
masa ba .
Nan Lauyansu Jafar ya fara sanar da kotu manyan shaidu da kotu ta gamsu dasu , daga karshe haka Sahid ya rasa ta cewa har ya amsa tuhumar, yayin da lauyanshi bai iya kare shi ba .
Daga karshe lauyansu Umar ya nemi kotu data umarci Sahid da ya fito da dukkan dukiya da kadarori mallakin wannan marayu har wanda ya kashe ya fita birtaniya ,
Sannan lauyan ya mikawa kotu adadin kudade da kadarori da Sahid ya zaune."
Bayan alkali ya gamsu ya sanarwa da Sahid umarnin kawo wannan kadarori a zaman kotu na gaba........
Ana tashi daga zaman kotu Sahid asubiti ya wuce sakamakon ciwon kafarshi ,
Umar dai yana can , amma duk sanda akai zaman kotun yana bibiyar yaji yadda aka tsaya , wannan babbar shari'ar har gidan radio ake saurara..
"Malam wannan wacce irin rayuwa ce na shiga uku malam."
Mahaifiyar Maryam take fada cikin kuka yayin da take rike da gawar Maryam a hannunta .
"Malam Maryam ta rasu ta bar mana duniyar , ina zansa kaina , wallahi bazan yafewa wannan yaron ba , ya Allah ka ga yadda ya yi mana..." Ba tare data karasa maganar ba ta sake rushewa da kuka mai matukar gwanin ban tausayi .
Malam na lado shi ma baisan lokacin da wasu hawaye suka zu'bo masa ba , ya kalli gawar Maryam yana cewa, "Na yafe miki Maryam."
Ya yi sauri ya fita waje yana kuka .
Zainab hankalinta ya kuma matukar tashi sosai dajin labarin mutuwar kawarta Maryam, aiko cikin radadi da nadama ta dauki wayarta ta kira Mahmud amma bai dauka ba kira uku ta yi amma tana shiga ba tare da ya d'auka ba.
Ta jefar da wayar gefe cikin kuka tana cewa, "Ya yi fishi dani, ba laifin ka ba ne dole ka tsaneni." Ta sake fashewa da kuka tana cewa
"Na juya maka ba ya na cutar da kai,na cancanci duk wani hukunci yaya Mahmud.wallahi yanzu na yi nadama."
Ta sake 'kan'kame fulo tana kuka
kimanin minti biyar tana kuka tana tunanin Mahmud ta ji wayarta ta fara ringin
Cikin jajayen idanunta na kuka da dake ganin dishi-dishi taja wo wayar
Yadda idanunta suka nuna mata tai saurin share hawayen tana tashi zaune
"Yaya Mahmud." Ta fad'a da mamakin ganin kiranshi
Ta kara wayar a kunne tare da sallama
Bayan Mahmud ya amsa ta ce ,"Yaya fishi kake yi dani koh , dan Allah ka yi hakuri ka yafe min."
Wata karamar dariyar shi taji a can kasa kafin ya ce ,"Haba 'kanwata ni ban yi fishi dake ba , domin babu abin da kika min."
Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce ,"Dan Allah yayana ka yafe min , nasan na yi maka ba daidai ba lokuta da yawa.".......
Ba tare data karasa maganar ba ya dakatar da ita yana cewa, "Hmmm Zainab ke nan to na yafe miki."
"To yaushe zaka zo."?
Ta yi tambayar tana ajiyar zuciya
Mahmud ya ce ," Zuwa kuma , ai gaskiya ba ranar zuwa domin ayyuka sun min yawan."
Cikin muryar shagwa'ba Zainab ta ce ,"Auu baka da lokacin masoyiyarka."
Mahmud yaji wani zummm da shaukin yadda ya yi maganar ya ce ,"Ai masoyiyar ba ta sona, har yau, hakan ya sa na mance da ita."
Zainab ta fara kukan shagwa'ba da yake jin sautin sa yana masa dadi tana cewa, "Wai Yaya ka dena sona koh."
Mahmud ya yi dariya sannan ya ce ,"Ina kika ta'ba jin Yaya ya ce ba ya son kanwarshi , ai har abada bazan dena san ki ba Zainab. "
Zainab ta ji dadin maganar matukar gaske cikin shaukin soyayyar shi ta ce ,"To idan haka ne ka zo kano ina jiranka. "
"Gaskiya babu lokacin Zainab."
Ya fad'a kai tsaye
"To gaskiya ni idan baka zo ba a cikin satin nan na yi fushi kuma rijiya zan fad'a."
Mahmud dariya ya kuma yi mata yana cewa, "Kanwatyna zan zo kinji na yi alkawari, amma ina Harun yake."
Wani yarrrr ta ji da kiran sunan Harun , baki daya sai ta koma sabon yanayi mara dadi .................
"Tun da Maryam ta rasu malam dai kun ga ba shi da lafiya,kuma hakan ya tsayar mana da karatu , gashi malam bai d'au mataki a kan shi wannan mutumin ba."
Wani daga cikin almajiran malam na lado mai suna Garzali yana karantawa sauran gardawan su uku abokan karatun shi .
Wani mai suna Allaro ne ya ce ,"Ai wallahi ko ni bazan yafe masa ba ."
Nazifi ne ya kalli Musa yana cewa, "Kaji su , to ai ba ido zamu zuba ba , tun da aunty Maryam ta rasu shi wanda ya kashe tan ma ko gaisuwa bai zo ba ."
Garzali ya ce ,"Ai wallahi da munsan inda zamu ganshi sai ya gane ba shi da hankali, sai mun masa shegen duka wallahi. "
Musa ya ce ,"Allah sarki aunty Maryam. Allah ya sa kin huta Allah ya jikanki ."..
Harun yana jin jita jitar Allah ya yi wa Maryam rasuwa sai dai bai yadda ba domin bai samu tabbaci ba .
Malam na lado ne kwance a daki cikin zazzabi
Matarshi ta zauna kusa dashi tana cewa, "Malam yanzu babu abin da zaka yi wa wannan yaron Haruna , kai fa malami ne ko yanzu yana daga d'aki zaka iya kashe shi , amma ka ki aikata komai akai , ka ki daukar mana fansa ."
Ta yi maganar cikin ciwo da matukar damuwar rashin 'yar ta .
Share, comment and like ................................
Gubar Rayuwata
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)