Sashe 5
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ya ce ,"Zaki aure ni Zainab, kina so na."? Jitai zuciyar ta tai wani irin bugawar tsoro "Ni dai ina son ki , amma kiyi tunani." Ya tashi ya shiga cikin d'akinshi , Zainab tana bin shi da kallo "Me ya sa yaya Mahmud yake mini haka , duk abin dake ranshi kawai fad'a mini yake ko kunya." Zainab tai maganar tana mamaki tare da sake kallon kofar d'akinshi Kiran Harun ne ya katse mata tunani, ta tashi ta shige d'akinta, kai tsaye kan gado ta fad'a ta cigaba da waya dashi. A halin yanzu Alaji Idris ya yi azumi guda 58 yana zaune a falo shida Hajjiya suna hira "Wato Hajjiya kinga a kwana a tashi na kusan kammala azumi na , Allah ne abin godiya." Hajjiya tai murmushi tana cewa, "Wallahi kuwa Alaji ai wata rana sai labari." "Wallahi Hajjiya na yi dace da samunki a matata , duk wanda bai samu mace kamar ke ba , to abin tausayi ne ." Dariya Hajjiya tai tana cewa, "Alaji ke nan ai ni ce na yi dacen miji wallahi , ni dai fatana Allah ya barni da kai." Alaji Idris ya zaro mata idanu yana cewa, "A barki dawa? ai ko Allah bazai barni ba , sai dai kiji wufff na mutu ." Ya karasa maganar yana dariya Ita ma Hajjiya dariya tai tana cewa, "To ai shi ke nan kowa na haka ne . To amma Alaji me zai hana kasha ruwa muje kauye a gaidasu , domin mun kwana biyu bamu je ba ." Alaji Idris ya ce ,"Eh gaskiya ne wannan in sha Allah zamu je kuwa ." ..... Yanzu karfe 12 na dare , sai yanzu Uncle Yahaha ya tashi a bacci daga d'akin Fa'iza, yana tashi a firgice ya sakko daga kan gadon , Fa'iza dake kan kujeara sauri tai ta tashi tana kallonshi da cewa ,"Lafiya kuma ." Ajiyar zuciya ya yi , sannan ya ce ,"Bansan zan yi bacci haka ba , ga shi dare ya yi , tafiya zan yi gaskiya. " Ganin yana kokarin sa takalmi Fa'iza da sauri tasha gabanshi tana cewa, "Haba Yahaha dan Allah wanne irin tafiya kuma bayan dare ya yi haka kawai ka bari saida safe ." Ganin yadda take kwarkwasa ya sa yasha jinin jikinshi , ya fara mata magana cikin nutsuwa. "Haba dai safiya , na bar kakata a gida ita kadai, kuma ban sanar mata zan kwana a waje ba , ni ban ta'ba kwana a hotel ba , kuma bugu da kari da mace ." Shagwa'ba ta fara tana bubbuga kafafunta a kasa tare da girgiza jiki, "Ni gaskiya ka zauna ." Shi kuma banza Uncle ya koma gado ya zauna jabar , "To shi ke nan na fasa tafiya , amma da sassafe zan tafi." Wani dad'i ya kashe Fa'iza a tsaye ta karasa ta d'auko masa abinci . Bayan ya gama cin abincin na wajen wasu mintina . Fa'iza ta tashi ta jawo akwatinta rigar jikinta ta fara kokarin cirewa hakan ya sa uncle Yahaya saurin kauda kai ya kalli fuskar gado . dariya ta yi tana kallonshi , tsat ta cire doguwar rigar , sannan tasa wacce bata kai wacce ta cire arziki ba , gadon ta hau ta zauna tana kallon Uncle Uncle Yahaya yaji wani yarrr ,"Haba mene nasa irin wannan kayan kuma." Dariya tai tana cewa, "Baby bana san yarinta , sai ka ce ba wani mara ilmi." Hard'o wuyanshi tai tana cewa, "Wallahi ina san ka Yahaya aure nake son mu yi." Duk ya rasa yadda zai da ita jikinshi ya fara rawa "To shi ke nan naji sake ni." Fa'iza ta sake shi tana murmushi Lokacin da safiya tai , su Uncle Yahaya harda yin wanka sannan ya tafi gida wajen kakarshi domin ita kadai yake da ita. Yana fita wayar fa'iza ta fara ringin tsaki taja sannan ta d'auki kiran . "Yaya haka haba my baby zaki tafiya baki sanar dani ba , me ya sa ." Daga can bangaren aka fad'a Tsaki Fa'iza tai tai tana cewa, "Dole idan zani waje sai ka sani ne ." Daga dayan bangaren cikin mamaki ya sake cewa ,"Kai Fa'iza ni ne fa , Abdul Salim ne ." Dariya ta kwashe da ita tana sake tuntsurawa tana cewa dashi ,"To kana tunanin muryarka zata buya ne ,koba komai ai na yi saving numbobinka nasan kuma kai ne ." Ya yi ajiyar zuciya tare da cewa ,"OK yaushe zaki dawo to." Gaskiya ba yanzu zan dawo ba , domin babu kud'i a hannuna kuma ina san zan se wasu abubuwan in taho dasu ." Abdul Salim ya yi murmushi yana fadin ,"Zan turo miki dubu dari ki yi hakuri da ita." Fa'iza ta ce ,"Shi ke nan to ina jira ." Abdul ya ce ,"To ko dai siyayyar aurenmu zaki fara ne." Fa'iza tai tsaki tana cewa, "Wanne irin aure kuma , ni dai kasa min kud'in , sauran maganar sai na dawo." Ya ce ,"To ba komai I love you. " Ya kashe wayar . Shi Abdul Salim haifaffen dan legos ne da yake da gata , kuma dan masu fad'e aji dan manya, Yana son ya auri Fa'iza, bai taba lalata da ita ba , amma Fa'iza ba sonshi take ba , ya yi mata komai hatta gidan da take ciki a can shi ne ya siya , Saidai ba cikakken hankali gare shi ba , yana shaye-shaye , Kuma baya barin duk wanda ya zo masa da rainin wayo. Harun ne zaune shi da Zainab a restaurant Tun da ya sa idanunshi cikin nata bai cire ba , sai tunani yake kala-kala Shin Zainab kuwa zata ba shi kanta , ko kuma maganar aure zai je da ita , to amma yasan Mahmud ba zai bari ba , hakan ya sa kawai yake jin gara ya yaudareta kamar yadda ya saba yiwa sauran 'yan mata. Tom ni dai comment din na PC , share, like ........... Gubar Rayuwata