Sashe 20
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
abin dana ba ta na karba , dama taimakonta zan na aura , tana karuwa waya san cutukan dake jikinta .Ai yanzu na gane Allah ya yaye mini wahala." Fa'iza duk ta rasa inda yake mata dadi ta kasa cewa komai Abdul ya mika musu wannan kwadon gidan yana cewa "Rufe min gidana mu tafi." "Kai Abdul akwai wani gardi fa a gidan kamar bacci yake ma." Wani a gefenshi ya yi maganar yana nuna gidan Abdul da ranshi ya yi matukar baci ya kallesu yana cewa "To uban me ya sa bai fito ba ku koroshi tunda ba gidanshi ba ne ." Kamar suna rige -rige suka fada Cikin gidan kai tsaye sukai dakin Uncle duk yabi ya tsure ganinsu a kanshi "Ba yin Allah lafiya ." Uncle ya yi maganar yana kallonsu daga kwance "Tashi ka fita dan uwarka , kwarto kawai . Ita ma kwartuwar taka mun am she gidan mu." Haka Uncle taji an fada , ba tare da ya gane wane ya yi maganar ba . "Dan Allah ku yi hakuri, wallahi cutar barin jiki gare ni bana iya tashi." Ba tare da sun ce komai ba suka dauko shi su su hudu , biyu sun rike hannaye , biyu sun rike kafafu . Haka suka fito suka wurgo Uncle waje "Kan uban can dama har yau wannan yana nan , to Allah ya kuma tonaki ." Abdul ya karasa maganar yana kallon Uncle da yaji wurgi yana kwance a kasa Suka rufe gidan suka hau mota sukai tafiyarsu . Cikin mummunan takaici Fa'iza ta fara tattara kayan da aka watso mata , waje guda ta had'a su tana kallon tare da tunanin sauran kayan dake ciki, a cikin ranta ta lissafa yadda zata dauki kayan a hannunta ba tare dasun mata yawa ba . A lokacin kuma hankalinta ya kai ga uncle yahaya da yake zararar da hawaye . Wanda sa'ilin ta kuma kula da yadda gari ke rugugi sakamakon had'owar hadari . Had'e rai ta yi tana kallon Uncle tare da matsawa kusa dashi tana cewa "Ni zan tafi , domin babu inda nake dashi bare na je dakai ."