← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 27

Sashe 27

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ajiyar zuciya ta takaici Harun ya yi sannan ya ce ," Bari kawai Sa"id , ina cikin wani hali. "

Shima doctor ajiyar zuciya ya yi yana cewa, "Meke damunka haka dan Allah."

"Abokina ka ga ina fama da ciwuka da bansan daga ina suke ba , domin ka ga ina ciwon kunne."

Dactor , ya ce ,"Eh tabbas ga shi na ga yana ruwa."

Harun ya cigaba da cewa ,"Ciwon ciki , kasala , kai hatta futsarina ya canja , dama kuwa HIV ba bakuwata ba ce ."

Da mamaki abokinshi ya ce ,"Kana nufin kana da ita Harun wa'iyazubillah."
Harun ya had'e rai yana cewa, "Ka ga ni dai bana san wani iyayi kawai ka bani magani."
Murmushi Dactor ya yi yana cewa, "Gashi ma ko gaisawa bami ba , amma bari na kira nurse ummi taje ta raka ka a yi maka gwaji , shi kuma kunnen naka gaskiya sai ranar da dactor ya zo."
Harun ya ce ,"Okay ."
Likitan ya d'auki waya ya kira nurse sannan ya durkusa yana rubutu a cikin takarda lokaci guda kuma yana cewa, "Idan ka je a kai maka sai ka dawo mu yi hira kafin result din ya fito."
Yana rufe baki Ummi tana turo kofa ta shigo
Wani shegen kallo Harun ya zuba mata , sakamakon yadda ta shigo wani sindi-sindin da wani karamin hijabi
Had'iye yawu ya yi yanayin shi duk ya canja
Sa'id ya bata takardar yana cewa, "Ummi ki kai shi a dubashi bako na ne , idan result ya fito sai ki kawo min ."
"Okay sir ." Shi ne abin data fad'a
Tana fita Harun yabi bayanta , harda hard'ewa da tuntu'be yana tafiya , yadda ya ga ta ba shi baya tana tafiya yaji kamar ya yi abin da ya saba , domin ta matukar shiga ranshi a wannan yanayi
Jitai an sa hannu ana shafa mata baya cikin wani salo , hakan ya sa taji wani yarrrr ta juyo cikin tsananin mamaki da tashin hankali
Harun ta gani yana mata wani murmushi, hakan ya sake fusatata
"Kutumar uba .Kai wanne irin d'an iska ne wawa shasha ."
"Allah ya baki hakuri." Ya yi magana yana duban da hange karta tara masa mutane
"Allah wadaran jahili irin ka , baza ka gama da duniya lafiya ba wallahi Allah ya isa. Wallahi ba da ban doctor Sa" id bane ya had'a ni da kai sai ka ga abin da zan maka ".
Ta buga wani tsaki tare da harara ta cigaba da tafiya
Ana yiwa Harun wannan gwaji ya koma wajen doctor kamar yadda ya ce
" Sannu Harun ." In ji abokinshi
"To ya kake ya kwanaki ai wallahi na yi zaton zaka dawo da kakin soji."
Harun ya ce ,"Ina ta lafiyata ina wani maganar kakin sojoji , wallahi kunne na kamar , kaiii ina shan wahala dactor. "
"To Allah ya sauwake yanzu ya ake ciki ne ."?
Cewar dactor Sa'id
Harun ya gyara zama yana cewa," Yawwa ni abin dake damuna ma wallahi Yahaya ne , domin na jima banajin shi , ga shi har na dawo an ce wai ya tafi legos. ". Ya karasa maganar cikin tsananin son jin Sa'id ya yi magna a kai
Sa'id ya ce ," Allah sarki Yahaya , ai wallahi bamu da labarin shi tunda ya tafi legos, bamu san halin da yake ciki ba ."
Cikin damuwa Harun ya ce ,"Gaskiya ya kamata mu san halin da yake ciki doctor. "
Sa'id ya ce ,"Insha Allah zan sa a bincika mana legos din , domin akwai wani abokinshi Shu'ai bu."
A lokacin Ummi ta shigo ta mikawa dactor result din Harun
Yayin da ta zo fita ya sake 'kura mata idanu ta jefeshi da wata harara ta fita
Bayan ya bude sakamakon ya tabbatar wa Harun yana d'auke da ciwon hanta
Amma Harun bai damu ba , sai da doctor ya tabbatar masa ciwon hantarshi mai tsanani da muni ne , domin a kan mutuwa lokaci guda ko kuma hantar mutum ta dan'kare waje daya.
Sannan ne hankalin Harun ya yi matukar tashin gaske , nan ya nemi matakan kula d kanshi da magunguna ,bayan ya koma gida ma dai jikin nashi ya sake matsawa sosai musamman ciwon kunnenshi da yake fitar da ruwa mai warin gaske , iyayenshi suna matukar iya yinsu domin samun lafiyarshi amma har yau Allah bai yadda ba .
Haka anan cikin gidan yari Sahid rayuwa ta juya masa baya , ya matukar yin nadama yadda ya kula ba shi da wani gata , mahaifinshi babu , mahaifiyar shi bata tare dashi ga kuma wannan ciwon kafar da a halin yanzu zuwa anjuma za a yanketa , innalillahi wa innailaihir raji'un
Baya jin dadin rayuwarshi ko kadan a halin yanzu. Allah ka yi mana da kyau
A yanzu zainab da Mahmud ranar biki kawai ake jira , domin tuni an yi shiri tsaf dukkan family suna ta murna da wannan had'i .
Haka farin ciki a gurin su baba anje , komai ya komai daidai ba su da wata damuwa , Umar yana tare dasu ga dukkan abin da ya taso musu , domin ya sadaukar da rayuwarshi ga Kalisa , sai dai muce Allah ya jikan wanda suka rasu , muma kuma Allah ya....
Matukar ciwo Harun yake ciki, yana tabbatar wa kanshi wannan yanayi da ya tsinta kanshi sa'bon Allah ne da ya ringa aikatawa, sai dai a halin yanzu Harun ya matukar shan jiki
Wannan ciwon kunne , matukar wari, ruwa kuwa ba dare ba rana , sai ya tafi ya fara jin sauki sai komai ya sake lalacewa, ya ringa sunbatu ke nan har yake sanar da iyayensa irin abin da ya aikata a kano , ya ce musu alhaki ne ke bibiyarshi, su dena nemar masa magani .
Sun matukar koka sosai dajin halin yaron nasu , sai dai dukkan inda aka ji mai magani ana nemawa Harun , amma har yau ba a dace ba , ko da ya tafi sai ciwon ya dawo , har da kanshi ya gane mutane gudunshi suke saboda wannan wari da yake cutar dasu.
Babban abin da ya sake girgiza shi yadda doctor Sa'id ya tabbatar masa da mutuwar wulakancin da Uncl
e Yahaya ya yi abin ya sake d'aga masa hankali da jin tsoron duniya.
Wata mata ce dumur mur da ita zaune a falo tana wasa da 'yarta wacce bata wuce shekara biyu ba
Matar tana jin an kwankwaso kofar falon ta tashi ta bude
Mijinta ne ya dawo daga wajen aiki , nan ta tarbeshi ya karaso ciki yana d'aukar 'yar tashi yana mata wasa
Matar tashi ya kallah yana cewa, "Faiza wannan babyn tamu fa ta yi wayo , a gaskiya ya kamata a yi maka 'kani."
Ohhhh ni ko na ce ashe faiza ce da mijinta , iko sai Allah
Cikin wata kissa ta kalleshi tana amsar babyn ta aje ta gefe , kana ta rungumo mijin nata tana cewa, "Ai ni kai nake jira , duk sanda ka shirya."
Yadda yaji yanayin ya masa dadi ya sa ya fara sunbatar Fa'iza , ita ko ta sake kankameshi tana.......
Ooooooohh nan mata da miji ne , kowa ya basu guri , daman Fa'iza yaya a baya , bare yanzu me dalili .
Ni ko na ce Alhamdulillah ala kulli halin , anan na kawo karshen wannan kaggagen labari mai suna GUBAR RAYUWATA
Abin da mukai daidai Allah ya amfana
Abin da ya faru sakamakon karancin ilmi ina fatan Allah ya haskakan anan gaba
Ni Fatima Abdallah kano
(Autar marubuta)
Ina mika godiya ga masoyana masu comments, like da kuma sharing Allah ya saka muku ya cika muradan ku.
A kan haka nake muku albishir da sabon labari mai suna
FATIMA
DA
ZARAH. Wanda ya samu tsarawa da shiryawa daga gareni .
Anan zan barku tare da dukkan wani fatan alheri
07040805269
Autar marubuta
Times New Roman
Times Ne
w Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
9e752b9c58e3498f992b3c6bfc539243
Chapter 27 · 0% Book details