← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

, shi ya sa na yadda har yake rabata , tabbas dole ya bar Zainab kuma zan sameta . Abin mamaki yana nan da halinsa." Ahmad dai abin ya taba shi sosai ya ba shi mamaki Anan kuwa cikin hotel Fa'iza da Uncle Yahaya sai wanda ya gani tana kwance jikinsa yana shafa kanta tare da cewa ,"Ni dai na shiga uku , idan kin tafi gobe ya zan yi." Dariya Fa'iza tai tana fad'in ,"Wallahi ka shirya mu tafi tare , domin ni wallahi bana iya zaman kano ta ishe ni , dama soyayyarka na zo nema kuma na samu." Uncle Yahaya ya ce ,"Kin samu kuwa , domin ni duk bana ganin wasu mata sai ke Ina matukar son ki baby." Fa'iza ta tashi zaune tana masa wani irin kallo . Yanayin kallon ya sa yaji...... Laila tana matukar cikin damuwa da rashin kulawar uncle Yahaya, ga shi ita ba waya gareta ba , zaune ta ke ta yi tagumi cikin falon gidansu hawaye fal cikin idanunta tana tambayar kanta ,"Wai shin Uncle me ya sa haka , wallahi zuciya ta , ta damu da kai sosai , me ya sa nake kaunar ka haka , ya Allah ka dawo da Uncle gare ni." Daga wajen gida taji karar motar shigowar barrister Adam , wato mahaifinta hakan ya sa ta sami nutsuwa. Washe gari da safe Fa'iza ta koma legos, Uncle Yahaya dai ko kadan bai ji dadi ba , yana komawa gida ya sami kakarshi cikin mugun yanayi na zazzabi, wanda dole sai da suka tafi asubiti. Yau kwana guda ke nan da rashinsu Alaji Idris, duk rayuwar su babu dadi, babu farin ciki , mutane suna girgiza idan suka ji wannan zancen mutuwa, haka Umar abin ya taba shi sosai , musamman ganin Kalisa cikin yanayi mara kyau. Haka Sahid da mahaifinsa malam Aminu abin ya bige su . Tom ni Fatima Abdallaah kano Ina sanar daku akwai masu yawo suna 'bata mata suna wato ana bud'e group na batsa na iskanci ana dora novels din mu jikin wannan link ana share. zaki shiga d nufin samun novels, tom sai ki ga ba haka ba dan haka muna sanar d ku ba mu bane ba kuma zamu yafewa wanda suke shirin 'bata mn suna ba A kiyaye A ranar yau kakar Uncle Yahaya ta rasu , tabbas ya ci kuka sosai , haka aka shirya daluban makarantar DR .D.D suka je gaisuwa. Allah ya jikan musulmi Harun yana matukar takaici da abin da Mahmud ya yi masa amma babban farin cikin da yake samu Zainab sam bata yadda ba , hakan ya ke faranta masa rai . Sun zana jarabawarsu , wanda hadda Umar Ahmad ya sami Zainab ya mata fad'a sosai a kan Harun, ta ga bacin ran sa , wanda sai da ya yi niyyar sanar da Alaji Kabiru mahaifinsu , amma Mahmud ya ce kar ya sanar dashi tukun zata gyara . Yadda Zainab take ganin Mahmud ya shiga tsakaninta da Ahmad ya sa ta dena kulashi , tana matukar jin haushinsa, kuma ta sanar masa ba za ta rabu da Harun ba. Yau an gabatar da addu'ar bakwai ta su Alaji, mutanen kauye sun zo da matukar yawansu, wajen yamma kuwa kowa ya watse in ka cire mutanen anguwa dake shigowa jefi-jjefi su yi gaisuwa Iyalan Garba ne shirye tsaf sun fito harabar gidan, Kalisa ce ta kalli Garba tana cewa ,"Dan Allah Baba Garba kai ma tafiyar za kai , ka bar mu , ai muna jin dadin zama dakai." Nabila ce ta ce ,"Haka ne wallahi mun jin sauki idan kana nan." Baba anje da Jafar basu ce komai ba dai , face tsayawa suna sauraron abin da kowa yake fad'a cikin kasalalliyar murya da rashin kwarin gwiwa Garba ya fara magana "To ya zami da mutuwa, ta tozarta mu babu yadda muka iya , kuma ni ba kud'i ne gare ni ba , zamana daku wahala zai ja , gatana Alaji ne , kuma yanzu babu shi , mota ta an sace Allah bai nufi ya canza mini ba , ya rasu , bani da komai , gara na koma kauyen zan fi nutsuwa." Ya aje maganar cikin rauni d'aga kai ya yi yana sake cewa ,"Duk abin da ya taso da kuke da bukatata , ku kirani." Baba anje ya kalla yana cewa, "Dan Allah Baba, kiyi hakurin zama da ...." Baba anje dakatar dashi tai tana cewa, "Haba Garba , yaran nan sun zama amana a gare ni , babu yadda na iya , Alaji da Hajjiya sun wuce haka , kuma ta su ta yi kyau , sai dai mu ce Allah ya jikansu da rahma ya kuma sa mu dace mu ma ." Matar Garba ce ta ce ,"Ameen ya Allah. " Haka su kai sallama da juna Garba ya tafi . A yanzu dai Uncle Yahaya sai Allah, domin tun tafiyar Fa'iza ya haukace da neman mata , lokacin da ba ya goyawa Harun ba ya a kan hakan fad'a suke , amma yanzu Uncle Yahaya sanda Harun ya kirashi ya masa gaisuwar kakarshi , yake ba shi labarin yadda yake fantamawa da karuwai , Allah ya sa mu dace Yau Laila tana cikin farin ciki ta yi wa Uncle Yahaya kalamai wanda ba ta taba masa ba , ta tabbatar wa kanta Uncle zai sakko daga yajin da ya yi mata , hakan ya sa ta tafi makaranta cikin kwarin gwiwa. Cikin zumudinta ta aikawa da uncle wannan wasika mai matukar dadi da kwantar da hankali har Khadija na tsokanarta yau uncle zai susuce dariya laila ta yi tana cewa, "Zuciyata tare data Uncle take bugawa da zarar ya barni to zata tarwatse." Dariya Khadija tai mata tana cewa, "An fa kusa tashi ga shi Uncle bai kiraki ba." A lokacin ta ji karar kararrawar makaranta, Laila ta 'bata rai tana cewa, "Aikin banza , wai ina Uncle ya shiga." Khadija tashi tai ta dauki Jakarta tana cewa, "Wallahi ba zan jiraki ba, indai sai kin tsaya wajen shi ." Laila ganin Khadija zata tafi ta barta ya sa ta fasa ganin Uncle ba dan taso ba , Cikin matukar bacin rai Uncle ya koma gida "Wannan yarinyar ni zata wani rubuta wa kalamai , to ni yanzu har akwai yarinyar da zan tsaya ina soyayya da ita , Allah ya kaimu gobe , zata gane kuskurenta kuwa , ga mata nan wacce nake so ita zan samu , zan yi maganinki." Kiran wayar Fa'iza ne ya sa ya sarara da maganar ya dauki kiran. Har dare ya yi Laila da matukar shaukin Uncle ta kwanta A washe gari da safe ta shirya cikin uniform din makaranta ta tafi Sakamakon yau talata d'alubai suna ta mamaki da aka ce su fito assembly, shi kan shi shugab n makaranta duk sun fito da sauran malamai haka Laila ta ringa amfani da wannan damar tana hango Uncle Yahaya tana kallonshi tana jin dadi .Sai dai shi Ko ta tata ba ya yi , sai dai ma idan ka kula kana iya ganin tsantsar rashin mutunci a idanunsa . A lokacin Uncle Yahaya ya fara magana cikin muryarsa mai dadi ga kunnen Laila. "A yau cikin wannan makaranta." Uncle ya fara magana yana kallon malamai da d'alubai . Washhh Allah na kuna sa ina dena typing da rashin like d comments wallahi Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta)
Chapter 8 · 0% Book details