Sashe 18
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hankalin ka ya kwanta ." Ta yi maganar lokacin data sha gabanshi Mahmud dakatawa ya yi yana fuskantarta, wanda wannan lokacin ne da ya dubi idanunta ya san taci matukar kuka, amma ba tare da ya bayyana mata ya gane ba ya fara cewa "Eh kam na ji dadi , tun da yanzu bakya cikin hadari irin na Harun." Ya karasa maganar yana korawa da ruwan jarkar dake hannunshi . Wata sabuwar 'kufula Zainab ttaa sake yi da jin hakan "Ka rabani da farin cikina , kasa dady ya mareni , kasa yayana Ahmad ya dena kulani , wallahi kai masifa ne , dan Allah ka koma garin ku kai ma ka yi rayuwarka haba ." Cikin bacin rai Zainab ta karasa maganar Mutuwar tsaye ya yi shi kuwa Mahmud, mamaki ya cikashi da jin wannan zance na Zainab, komai yaji ya sire masa , wai shi ne masifa "Zainab na yi miki gata .Amma sam ba za ki gane hakan ba yanzu, ni yayanki ne , ko ba komai ban can can ci wannan kalaman naki ba ." Bai jira komai daga gareta ba , domin shi ma ba iya abin dake bakinsa ba ke nan , amma ya wuce ya tafi, ya barta a gun , . Zuciyar shi cikin kuna da tunanin irin maganar data fadaa masa ya fara shirya kayanshi a jaka, babu bata lokaci ya shirya tsaf , sannan ya fita domin yin sallama da mutanen gida . A lokacin Hajjiya tana shirya break fast , ya fito , mamaki ya cikata , haka data sanar da Alaji Kabiru, shi ma . uzururruka ya basu sosai wanda ya kirkiro , sannan suka barshi ya tafi bayan ya karya , Ahmad ya hau mota ya rakashi zuwa......... Abdul ne yake kwala sallama gidan Fa'iza , Ni ko na ce ashe yana da hankali irin haka har baya fada mata gida Suna kwance tare da Uncle Yahyah a cikin bargo , da jin sallamar Uncle yaja dogon tsaki tare da sakinta daga rungumar da ya yi mata ."Yi hakuri baby , kasan Abdul ba hankali gare shi ba bari naje. " Ta sakko daga gadon tare da daukar kaya zata ,sa kawai ta fasa ta aje tasa wani dogon farin hijab ta fita Yana tsaye rai a bace , yana ganin ta ya fara masifa "Ni fa tunda wannan dan uwannaki ya zo bana ganewa , me ya ke faruwa ."? A jiyar zuciya ta yi cikin murya mai dadi tana cewa" Haba baby tun yaushe wai ya tafi ne. " Wani dadi Abdul Salim yaji ya rufe shi tare da nuna yadda yaji dadin maganar ya fara magana , "A gaskiya Fa'iz a na matsu mu yi aure , ko ba komai ki dena zama haka domin kinsan ina son ki." Ya aje maganar yana kallon cikin idanunta. A jiyar zuciya ta yi , kana ta fara cewa , "Na sani Abdul, amma fa banajin za a bari ka aure ni , sannan kuma...." Yadda ya dakatar da ita da maganar ne ya sa ta yi shiru tana saurararsa "Haba waye ya isa , ai duk fadin legos...." Shiru ya yi ,wanda a lokacin ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa ,sakamakon kiran da ya shigo masa . Yana kara wayar a kunnen shi bai fi wasu sakanni ba , sannan ya aje cikin gaggawa yana cewa da Fa'iza "Bari na je , zan kira ki mu ci gaba da magana." Ba tare da ya jira jin wani abu daga Fa'iza ba ya tafi hakan ya sa Fa'iza ta koma ciki , tana shiga dakin ta cire hijab din dake jikinta, kana ta zauna bakin gado , ya yin da uncle yahaya yake zuba mata kallo , lokaci guda kuma yana kai hannu jikinta . "Gaskiya akwai matsala." Fa'iza ta fada tana ture hannun Uncle a jikinta "Mene kuma ."? Uncle ya yi maganar da takaicin yadda ta hana shi abin da yake yi . Ba tare da ta jira ba ta fara da cewa " Wannan gidan , gidan Abdul ne , sannan aure yake so mu yi , bansan mene zan yi ba ." Had'e rai ya yi Uncle yana cewa "Aure kuma da wannan. To ni kuma fa."? " Nima shi ne abin dake damuna ai , ya zan yi."? Fa'iza ta fada tana kallon uncle "Fa'iza sanin kan ki ne bani da kud'i , bani da gida ke ce kike ciyar dani. Amma wallahi ko kin auri wannan Abdul din , to har gida zan na biyo ki . Gara ma karki fara kisa Allah ya konamu." Dariya Fa'iza ta kwashe da ita tana cewa, "Kana nufin yanzu kai Allah ba zai kona ka ba Yahaya , ka sabawa Allah ba mace daya ka nema ba fa." "Ki bar Wannan maganar, ai Allah mai gafara ne, kawai ki fada masa ni zaki aura in sha Allah ba zan baki kunya ba ." Fa'iza ta kalli Uncle yahaya tana cewa " Kar fa wallahi ka ci amanata Yahaya." Ta'be baki ya yi Sannan ya ce "Ni da ke mutu karaba Fa'iza." Ya jawota jikinshi lokacin da ya gama maganar. Yadda Fa'iza taji dadin yanayin ya sa ta fara cewa "Amma kasan kana da HIV ko." Rassss . Abin da Uncle ya ji ke nan a zuciyar shi , ya cireta a jikinsa yana cewa "Amma wasa ki ke koh."? Tintsirewa ta yi tana muguwar dariya lokaci guda kuma cikin dariyar ta fara magana " Sannu san banza , ka yi irin Wannan shanawar sannan ka tsira ko. To wallahi cutar HIV ta wajen shekara biyu , kuma ko matan kano din ma da kaje gunsu ai suna da ita . Kawai ka shirya muje asubiti asan matsayin taka , shi ne kawai ." Cikin dariya ta karasa maganar. Tashi tsaye ya yi cikin tashin hankali yana kallon Fa'iza "Fa'iza bana san irin wannan wasan wallahi, ki dena har duniya ta tashi babu ni ba wannan cutar." Ganin yadda Fa'iza ta lura dashi dari bisa dari bai yadda yana da Hiv ba ta tashi tsaye. "Haba dan Allah sai ka ce wani yaro , HIV ai ruwan dare ce , to wallahi kana da ita sannu dan san banza." Cikin tsaki da harara ta aje maganar, tare da juya masa baya tana zama bakin gadon . Timmmmm, abin da taji ke nan wanda hankalinta ya bata fad'uwa ce . Cikin sauri ta juyo , ai kuwa sai ga Uncle Yahaya a kasa kamar matacce . Da firgici ta yi kanshi tana jijjigashi tana kiran sunan shi . Yadda ta ga alamun kamar ya mutu ne ya sa ta tashi , ta sanya kaya riga da wando , sannan tasa hijab ta fita neman taimako. Koda ta fita babu kowa a wajen , domin anguwa ce bata mutane ba , sa 'a ta ci Allah ya kawo wani mai napep sannan ta kira shi , suka dauki uncle suka tafi asubiti. Tare da dukkan tashin hankali, Fa'iza domin tunaninta Uncle Yahaya ya mutu kawai , to idan Uncle ya mutu Allah ya jikanshi , dama kowa na haka ne. A halin yanzu Likitoci suna kan Kalisa domin tunda garin Allah ya waye suma basu samu damar ganinta ba , abin dai ba a cewa komai . Baba Garba ya musu waya cewa ya taho da million biyu , yana hanya, haka suma akwai wasu kudaden da suka samu daga al'uma . Bayan likitocin sun fito tare da dukkan tashin hankali su Umar suka tambayi jikinta nata. Yadda doctor ta tabbatar musu ba mutuwa tai ba wani sashi daga zuciyar su ya yi fari . "To zamu iya shiga gurinta."? Nabila ta tambayi Aisha likita " Me zai hana. " Ta bata amsa , hakan ya sa suka shige baki dayansu . Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa dactor Aisha, tana sharewa amma sun ki dena kwararowa "Da kun san matakin jiwonta , duk wannan kwarin gwiwar ba za ku same shi ba , ta ya zan fara fada muku wannan bayan kun kasa fitar da ita." Aisha ta karasa maganar tana dena kallon kofar dakin Kalisa tare da tafiya tana share hawaye. Cuta ba mutuwa ba ce . Share and comment.......................... Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) No editing _________________________________________ Page 33 & 34 Ba yadda Fa'iza ta iya da Uncle, gida suka dawo bayan likita ya tabbatar mata da ciwon barin jiki ne ya kamashi wato paralysis. Ta shiga rudani tun a asubitin, bata da kudin jinyarshi ya sa ta dawo gida , wani abin takaicin da yake damunta tun a asubiti ya fara bata aiki , domin wata gudawa da yake yi abin ba a magana , haka bayan ta dawo gida bai fasa ba , amma likita ya bata magunguna duk da haka abin bai lafa ba , yau ta sha bacin rai . Ido ta zuba musu tana kowanne su, yadda abin ya basu mamaki rabon da manyan idanunta su bude irin haka tun tana da lafiya "Kalisa ki daure ki ci abinci yaufa kwana biyu baki ci komai ba." Baba anje ta yi maganar tana rike hannun Kalisa. "Ku yi hakuri, na wahalar daku." Kalisa ta fada da kyer "Sahid ya ci amanar dady ." Kalisa ta kuma fada "Yi hakuri Kalisa da Wannan maganar, baba garba ya taho da kud'i yana hanya." Kalisa ta yi murmushi Umar ne ya ce "Dan ma yau juma'a ne da tuni ya karaso." Yadda Kalisa take wani mike mike ya sa duk hankalinsu ya tashi Da sauri Nabila ta kira Aisha, koda aka kirata kawai a jikinta ta ji Kalisa mutuwa za tai tana karasowa tare da wasu nurse aka fara buga mata iska tana haki Kalisa tana wahala tana jan wani numfashi tana mikewa wata doguwar ajiyar zuciya taja , sannan tai shiru , hakan ya sa suka dena buga mata iskar Doctor Aisha ta cire dukkan masu machine da aka sanyawa Kalisa. Yana yin yadda suka ga tashin hankali a fuskar dactor ya sa duk suka tsure . babu wanda ya iya tambaya wanne hali ne Kalisa ke ciki , duk da taja malullubi ta rufe fuskarta ,sai da doctor Aisha ta juyo ta kallesu tare da girgiza musu kai