Sashe 7
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akai ko zuciya ko ciki ba, she mostly target legs and hands, da gudu ta shige cikin container yarinyar Hawwa tagani tana kuka sosai tana ihu ta kankame kunnenta sabida karan bomb ga wuta data gani, ahankali Hawwa ta duka gabanta tasa yatsanta akan lips nata tace “shiiiiiiu I’m fairy Angel Anty I come to rescue you from bad guys,, dena kuka” juya mata baya tayi tace “hop on my back, hau baya” takai yatsunta biyu tana taba wuyan Hayatu ganin yana numfashi yasa tashiga kiransa “Hayatu Hayatu, wake up” ahankali Noor tahau bayanta ta kankameta, dasauri Hawwa ta tashi she will come back for Hayatu, Noor first fitowa tayi ahankali goye da Noor ganinsu yasa Khaleel yatashi yataho wajen su da sauri yazo ta bayanta yana murmushi sosai looking and sounding so emotional ganin little baby shi that looks so scared and terrified a bayan Hawwa yace “Noory” dasauri yarinyar tace “Dadyyyyy” karban ta yake shirin yi daya daga cikin criminals din data harba a kafa dake wajen yadauki sandan dake wajen yadaga zai bugama Khaleel dake kokarin karbe Noor daga bayanta, karaf Hawwa tagani dawani irin sauri tai pushing Khaleel yafadi a side nata sandan ya sameta a hannu da karfi ya yagi skin nata sai jini, kafa tasa ta daki kan thug din ya sume dasauri Khaleel yatashi yana kallon hannunta da jini yabata hannun rigan already yace “you are bleeding” ahankali tace “it’s fine, leave Noor help me pick Hayatu” gyadamata kai yayi tawuce dajin goye da Noor neman Abraham taganshi a sume akasa, dagashi tayi sukai mota tasashi abaya tasauke Noor ta sata a baya itama daidai Khaleel na zuwa da Hayatu a sheme ya ijiyesa abaya yasa hannu ya dauki Noor ya kankame ajikinshi yarufe kofan baya yadawo gaba yashiga ya zauna Hawwa taja motan da mugun gudu tana calling DIG office waya for backup. “I repeat my team are down, goons are also down seriously injured calling for backup, code 22028IV” Khaleel ya kankame Noor data kankameshi dukansu suna kallon Hawwa dake tuki around 11 nadare tana magana har saida DIG yadaga wayan dan da farko voicemail ne, ahankali Khaleel yakalli hannunta dudda baya ganin ciwon but hannun riganta was bloody.Kusan around 1:13AM na tsakar dare sukakai gidan sharp sharp aka bude musu gate cus DIG yarıga ya sanar da zuwansu, tun kafin su karasa tsakar compound din Excellency da Momy da mutanensu ke tsaitsaye suna jiransu, tun kafin tai parking Excellency da Momy suka shiga gudu suna tahowa wajen motan, tana parking mota Excellency yabude gaba Mommy tafashe da kuka tana kallon Noor datai bacci yarinyar ta rame tace “look at my Noor oh no no” takai hannunta tana karban Noor daga hannun Khaleel, shikuma Excellency yasa hannu yana fito dashi Khaleel yasauko yace “Dad did you call her Dr”? Dasauri yace “yes yes everything is set, yana clinic” Mommy tashiga shafa Khaleel da hannu daya tace “hope babu abinda yasameka Khaleely na welcome Alhamdulillah, babu abinda yasame ka”? girgiza mata kai yayi ahankali, Hawwa tadan matso taja kofan motan duk suka juyo suka kalleta takoma driving sit, Excellency yace “you guys did a great job Miss Hawwa welldone, dare yayi kuzauna anan zuwa safiya” calmly and politely tace “my team are down zan kaisu clinic dinmu” dasauri Excellency yace “ai da kin bari Dr ya gansu anan we have clinic anan” anatse tace “DIG yariga yace na kaisu clinic dinmu” dan ijiyan zuciya Excellency yace “okay but drive safe, bari nakara muku mopol su biku for extra security is night” dan gyadamai kai tayi cus batason ta kara gardama tai reverse da motan sannan tai kwana hakanan Khaleel samin kanshi da kallonta yayi daidai tana figar motan da gudu Excellency yace “ayi gudu a sannu” Khaleel yajuya ahankali yayi ciki.EPISODE Har clinic dinsu ta kaisu tajuya zata wuce Abraham daya bude idanu cikeda ciwon kai yace “kefa i think you need to see Doctor kema” yayi maganan yana kallon hannunta, yatsine fuska tayi takalli hannun tace “no I’m fine is not that serious, office zanje nacire vest din nan na wuce gida” tayi maganan tawuce tafita da sauri, office nata taje tadauko jakanta tafito tazo parking space nasu tashiga motarta kiran corolla na 2006, taja motan sannan taciro wayanta tai dialing number da tai saving da Best N, ringing daya ta daga ahankali tace “kina clinic dinku ne? Wannan dakika dauka u must be on night duty, kina nan”? Daga ta dayan bangaren wata murya mai dadi tace “yes inanan but inadai shirin tafiya around 5 nadau permission, kaman kina driving me kikayi da kikakai ware haka an office? Anyways just come I know u will tell me, Yau kwana nawa bamu hadu ba? Please come ko 1minutes ne kiganni” dan murmushi kadan Hawwa tayi tace “bribe me” dasauri tace “I will not beat Yasmeen da Yaseer all through this month I promise” murmushi Hawwa tayi sosai tace “good girl” dan tsuki tayi tace “you’re just lucky I’ve missed you ne da dagake har yaran naki nayi biji biji daku” tabe baki tayi tace “shege kafasa sabida kinga ina gate, barima najuya” da sauri tace “yakuri mana Hawwa” dan dariya kadan tayi tashigo asibitin tai parking motanta tadanyi jimm sannan tabude tafito tafara tafiya tawuce ciki, direct wani office tawuce daidai takai hannu zata bude aka rigata budewa wata mata ce aciki fara ce tsawonsu daya da Hawwa kawai dai tafi Hawwa jiki ne saidai itama bawai irin kiba sosai din nan ba ne kawai dai tadan ciko ne, tana sanye da kayan nurses dark blue riga da wando, wani irin rungume Hawwa tayi da sauri tace “oyoyoooo” “asssshh Ni’ima My Hand” Hawwa tafada ahankali dayasa Ni’ima ta saketa da sauri takalli hannun tace “wat happened to your hand kikaji ciwo haka eh?” Dasauri tajata suka shiga office din ta maida kofan tarufe tawuce ta daurata akan kujera tana kwaso abubuwan dressing tace “wat happened ya akayi kikaji ciwo?” Dan yatsine fuska Hawwa tayi tace “banmasan tayaya naji ciwon ba ni karan kaina Best, na manta” zama Ni’ima tayi akujeran dake facing nata takama hannun tana wankewa da ruwan spirit tace “I thought we had agreement cewa bazaki dinga involving kanki in field work ba saidai office work” ahankali Hawwa tace “and it has always been like that, koda naje field ma bana shiga aikinsu, yau ne kawai and its circumstances saisa but ai I’m fine ba zafi sosai ma ciwon” kallonta Ni’ima take fuskanta duk ya nuna damuwa da rashin jin dadi hakan yasa Hawwa tace “common I’m fine it’s just a scratch” anatse Ni’ima tace “da inada wata kawa daban damu ba, but you’re all I got tun ina yar yarinya” murmushi Hawwa tayi tace “tun zamanın primary school” ahankali Ni’ima tace “please take care of yourself kinji Hawwa” gyadamata kai Hawwa tayi tana dan yarfe hannu da style cus shegen zafi yake mata and bataso Ni’ima tagane ta damu, hannun Ni’ima ta karba tadauki wata paper daga kan table tashiga fifita mata ciwon tana kallon ciwon ahankali tace “Hawwa I was never against kinason ki zama police sabida I know yanda kikeson justice, da kare hakkin dan adam but deep down Allah yasani banason aikin, my worst fear arayuwana shine wani nawa wanda nakeso yazama soja ko dan sanda cus I always believe mutum yazama police ko soja kaman ya yanki automatic ticket na mutuwa ne” taidan shiru tace “dakika fadamin anyi promoting naki bayan kinyi solving that kidnapping case an saki under special kidnapping task force u are not even in shi asalin police station I was happy, very happy sabida i know talent dinki is identifying, profiling criminals and knowing criminal minds kina taimakawa wajen kamasu da relating dasu da gane abinda zasuyi ko suke shirin yi, understanding zukatansu nasan that is basicially your work ba aikin dazakije filin daga ba kina combat da maza ba” dan murmushi kadan Hawwa tayi tace “kai Best is just a scratch kike surutan nan randa za’a kawo miki ni kiciremin bullet f…..” “Hawwa!” Ni’ima takirata adan fusace tace “will you stop joking around I’m serious, Hawwa I will always support you kinsani but not in this” tanuna ciwon hannunta tace “kodai kidena zuwa filin daga and stick to office paper work helping to solve crime behind the mask ko kibar aikin” Dasauri Hawwa ta kalleta, hawaye taruwa yayi a idanun Ni’ima tace “akanme kina mace zaki dinga fada da maza duk abi ajijjimiki ciwo amiki tabo ajiki” dan turomata baki Hawwa tayi looking damn sexy tace “ni bance kimin kuka ba sarkin kuka, I swear Ni’ima circumstance yasa dole na shiga field, shima ciwon is a mistake, don’t forget I got training fa a police academy, na iya fada, nasan how to attack and how to defend myself, I can shoot and so much more, this was just a mistake trust me and I promise you bazan kara barin kaina naji ciwo ba” gyadamata kai Ni’ima tayi tadauki tissue tana goge idanunta kar hawayen su fito, Hawwa tai dan murmushi cikeda tsokana tace “yan Nigeria da ganin mace musulma police as wani abu hmmmm” ballamata harara Ni’ima tayi dayasa tai shiru tasa hannunta a lips, Ni’ima ta karbi hannunta tacigaba da fifitawa cikeda masifa tace “naga kin kara jima kanki ciwo kiga abinda zan miki wlh” dariya sosai Hawwa tayi tana cire hannunta dagakan lips cikeda tsokana tace “I’m sorry Maman Hawwa” zabura Ni’ima tayi da sauri Hawwa ta tashi tana dariya tayi gadon office din tahau tana zare gyalenta ta ijiye a gefe tasa kanta akan filo tana sauke ijiyan zuciyan gajiya, shiku ne akanta dayayi mata kyau gashinta so black ga tsayi, tasaka stud gold earring dan karami dashi tace “bari nai bacci kadan, kitasheni by 5 natafi gida” ta lumshe idanu Ni’ima ta kalleta saikuma takoma ta zauna.EPISODE Tabuga tagumi, a girl is a girl and will always be a girl, while a Man is a man kawai, daga gani kasan tagaji bacci kawai take.Ahankali Hawwa ke bude idanu ta saukesu kan agogon dakin ganin 7 yasa da sauri ta tashi zaune babu kowa a office din, ahankali ta sauka daga gado tawuce bayi bata wani dade ba tafito daidai Ni’ima na shigowa tace “kin tashi”?