Sashe 105
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba, but yana sonki, yace zai chanza saiki jawosa jiki, da kulawa da kyautata ma juna harya chanza, change is not easy, it takes patient, but Hawwa kalli kalan halin dakikeyi, Hawwa zagi harda mari, harda mari Ya Allah!”Kai abun nama Ammi wani kalan ciwo da baxama ta iya bayani ba, she can’t believe Hawwa can do all this abubuwa to this poor boy, sabida taga yaron ajebota ne ko menene, dan talaka ai da yanzu an kirasu ance suzo su dauki gawanta dan wlh saiyaci uban ubanta ta mareshi, Ammi ta shiga share hawaye, noooo she can’t forgive Hawwa just yet, wlh bazata iya yafema yarinyar nan yanzu ba, amman tadaure tace “mahaifinshi na sonki but wlh yaji abinda kikema dansa ko yaji kinkaimai d’a kotu he will hate you for life Hawwa! Hawwa da kotu har gwara kisa mu iyaye mu karban miki saki ba kisa mutum a kotu ba! Duba da kalan gidansu, da mukamin Baban sa dayake dan siyasa kuma dan kasuwa!” Ammi tabuga kirjinta crying sosai tana kallon Hawwa tace “jinake kaman ni kikama abubuwan dakikama Khaleel Hawwa, it will take time kafin na yafe miki Hawwa, wlh kuwa I can’t forgive you just now sabida kin nunamin I’m not your mother and bankai mother awajen ki ba” kuka Hawwa keyi mai tsuma jiki Ammi ta fuzar da iska tace “jiya mijinki na asibiti tun safe baida lafiya!” Dasauri Hawwa takalli Ammi, Ammi tace “I am sure idan cancer bata kashesa ba kece babban cancer dazata kasheshi but ba komi kinma kanki, Alhamdulillah kin nemi saki kafin ki kashe dan mutane yarabu dake, anyways Babanki shine ke tareda mijinki a hospital tun jiya yauma sun koma sai anjima” Ammi ta sunkuci jakanta tai kofa dasauri Hawwa tarike Ammi tace “Ammi meya sami mijina eh Ammi”? fizge hannunta Ammi tayi azuciye tace “cikani kafin zuciya ta debeni namiki jina jina wlh shegiya mai kan kwakwa, yarinyar sai taurin kai kaman daga zamanin fir’auna tazo sakeni!” Ammi tamata tsawa dayasa Hawwa tasaketa da gudu Ammi tafice fuuuuu ranta abace.Kirjin Hawwa wani kalan bugawa yake Khaleel was sick? Har Baba natare dashi a asibiti? Innalillahi wani asibiti? Which hospital is he using? Tunanin hospital nasu yasa tafara hawa staircase taje sama dakinta tashiga ta kwabe hijabi ta wanke fuskanta tafito tashiga closet atampa tasaka diguwan riga tadauki veils da handbag kirjinta harwani bugawa yakeyi tana kiran sunayen Allah hankalinta yayi mummunan tashi no wonder jiya taga baya iyacin abinci sosai tadauka fadan dasukeyi.Fitowa tayi diguwan rigan yamata kyau tayi kofa tafice tawuce wajen mota tashiga taja tabar gidan.Khaleel na zaune cikin mota he’s very weak they just drop Baba agida suka dauko hanyar gidansu wayanshi ya shiga ringing ganin Mom ne saida yadanji wani iri he hopes batasan baida lafiya ba ahankali yace “Salman did you tell Mom banda lpy?” Dasauri yace “nooo” daukan wayan yayi kafin yayi magana Mom tace “My Baby na kana ina banganka both jiya da yau ba though jiya nasan bamanan muma where are you?” Ahankali yace “gani ahanya zan dawo gida”Dasauri Mom tace “tom idan kazo i want to see you be fast” murya cha. Kasa yace “okay” gıda suka shiga around 5 yana kallon motan da babu da yasan Hawwa batanan kenan wani kalan ijiyan zuciya yasauke aka budemai mota yafito yana tsayawa da kyau ganin Mom tsaye gaban study nata tana kallonshi wucewa yayi yashiga lift yayi sama yana ganinta yace “ina Noor?”Ahankali tace “tana tareda lesson tutor nata come” Mom takama hannunshi suka shiga office nata Khaleel yaga wani security wanda bai sani ba sanye da suit yadauke kai ya zauna Mom itama ta zauna kan kujeran dake facing nashi tace “Leely na I want to tell you something but inaso ka fahimce ni” tadan sauke ijiyan zuciya tace “dazaka auri Hawwa I forced Salman yagayamin everything he knows about Hawwa, and nima on my own nai finding info akanta cus I want to know wace zaka aura this is wat I always do nasan who is coming into my Son’s life” Khaleel yayi shiru yana kallon Mom yana hade fuska gani maganan is about Hawwa, yace “okay naji and? Why did you call me here Mom”? Dan ijiyan zuciya Mom ta sauke tace “2days ago ko 3days ne ma naga Hawwa tafita in the night sanye da uniform this guy is my private security agent, he works for me privately ganin is late I had to call him yabi Hawwa duk inda zata just for her safety, so yabita yakuma biyoku har kuka dawo gida so ni I forget to tell him he should discontinue the mission, so this is abinda yakawomin just now” Momy tadauki some pictures dake kan table nata that are close tamikama Khaleel ahankali ya karba yana kallo Baban Yasser yagani tsaye jikin motanshi da Hawwa ta dauka tafita dashi jiya ita Hawwa na cikin motan zaune, ga pictures din dahar glass na motan yarike yana leka Hawwa, numfashin Khaleel hargitsewa yashigayi yanabin hotunan yana dubawa one by one Mom cikeda makirci tace “I know very well ance mutumin chan tsohon saurayinta ne I know everything my question is what is she doing with him a Shari’a court? Although nasan ita yar sanda ne but metaje yi a shari’a court? Khaleel duk matan dazan auro maka suka shigo gidan nan basa kara fita saika sakesu to avoid sumaje su hada jiki da wasu mazan, is Hawwa cheating on you da aurent……..” “Mommmmmm!” Khaleel yayi ihu yana buga table na Mommy yanunata da yatsa yace “I know who my wife is! Don’t presume anything akan matana! My wife is special! My wife is a woman that guide her chastity! My wife is decent! She’s not a bad wild girls kalan wanda kike auromin! Hawwa can never do this! Idan ma sun hadu and so?” Yayi shiru cikin fushi yace “kada ki karasawa wani yabi matana ko abincika min mata I don’t appreciate that Mom! And I condemn such behavior! I trust my wife Mom okay!” Yayi maganan yana yaga hotunan ya watsar akasan wajen yawuce yafita daga office din Mom yawuce kasa numfashinsa baya fitowa da kyau yawuce flat dinsu dasauri……EPISODE Harcikin hospital nasu Hawwa ta shiga hankalinta tashe luckily taga Dr daya taba attending to her da sauri tai wajenshi tace “excuse me Dr please where is my husband Dr Khaleel?” Dasauri yace “ahh Madam ai he just left not quite long” gyadamai kai tayi tajuya tafice tashiga mota taja ana kiran magrib tashigo gidan tai parking daidai Khaleel na fitowa sanye dawata milk jallabiya mai bala’in kyau yabi motan da kallo dasauri ta sauko suna hada ido yadauke kai kaman baimasan wacece Hawwa aduniya ba, faduwa gaban Hawwa yayi bata taba ganin that kind of look a idanun Khaleel ba, dasauri tai gabanshi tana kokarin mai magana kawai yawuceta as if she’s a ghost, kaman baisanma wacece Hawwa ba, ko baima gantaba, dasauri Hawwa tajuya takalleshi gabanta na faduwa sosai saida taga shiganshi masallaci ta iya daga kafa ta wuce daki zama tayi akan kujera a falo taciro wayanta tana dafe kanta dake ciwo tacire wayan daga flight mode tai dialing number dazu luckily aka dauka muryan matan ne ahankali Hawwa tace “good evening Ma, please inaso na withdrawing divorce danai filing is Hawwa” shiru matan tayi chan tace “Alhamdulillah! Kin kyauta kwarai cus kinason mijinki just kuyi solving problem naku try communication is therapy for couples” ahankali Hawwa tace “thank you Ma” ta katse wayan tabar wayan awajen tawuce sama dantai salla.Khaleel na idar da salla yashigo dakin ya maida kofa yarufe yana kallon wayan Hawwa dake vibrating akan kujera wucewa yayi wajen wayan yasa hannu yadauka cus yana haka yana daukan wayanta, besides ya dauka Baba ne cus yabar wayanshi a daki yatafi mosque yakira yaji yajikinshi, ko Ammi saiyaga number ne ba suna, tsayawa yayi bai dauka ba dan koshi baya daukan unknown numbers maisa zai dauki nata, wayan na katsewa number yashiga kira again ya katse yashiga kira again 5calls number yayi duk a hannun Khaleel sai kawai yadauki wayanshi ya dauki number yasa a true caller yaga Aliyu ga hoton Baban Yaseer ajiki, numfashin Khaleel tsayawa yayi chak, yabude calls nata yanabi sai yaga tayi waya da number for about 6minutes 15seconds! Baban Yaseer yasake kira wayan na hannun Khaleel hannunshi rawa yashigayi da kyar ya ijiye mata wayanta inda ya dauka yayi staircase yafara hawa daidai Hawwa na fitowa daga dakin ta kalleshi amman wlh kaman Khaleel baiji alamun mutum bama ko kallon inda take baiyiba, kawai Hawwa taji tanama shakkan yimai yajiki,ta tsaya tabishi da kallo yabude kofa ya shiga ciki ya maida kofan yarufe, kuka Hawwa taji yazomata ganin kaman Khaleel ya tsaneta all of a sudden, kaman yahakura da ita, sai kawai taji takasa motsi dukawa tayi ta zauna awajen sai ta buga tagumi from the look on his face she’s scared to approach him wlh.Dakinta koma tai sallan isha’i ta kwanta akan dadduma tana sauke ijiyan zuciya duniyayamata zafi wlh ga mahaukacin kewan Khaleel tanayi ga cikinta na ciwo itadai kawai tanude idanu sabida kofan falo dataji ana budewa tagane asuba tayi.Salla ta lallaba tayi tanajin kaman zazzabi yakamata ga maranta kawai yana mata ciwo saida tai wanka tai salla tasauka kasa taje kitchen ta zubar da komi data dafa jiya she’s regretting da jiya tabama securities na gidan tea kawia tayi ta soya chips da egg takawo dinning daidai yana shigowa tajuyo ta kalleshi dasauri yayi wani irin kyau yana sanye da brown jallabiya amman kaman baisan tana falo ba ko kallo inda take baiyiba yawuce yafara Hawwa staircase bakin Hawwa nadan rawa tace “uhmm….zan…zan….dan fita zanje wajen Ammi tana gidanmu tazo jiya” “suit yourself” yafadi not sounding good not sounding bad Hawwa taji hankalinta yatashi, this is not Khaleel! Ba haka yakeba, sai kawai itama takoma sama tashiga shiryawa taje tagayama Ammi ta tayata bashi hakuri, abaya tasaka black da gyale tasaka flat shoe tadauki bag, she needs Ammi takoya mata tayaya zata bama Khaleel hakuri, sannan adaidaita su.Fitowa tayi takalli dakinshi tashiga sauka kasa tadauki wayanta data manta dashi akan kujera, 20miss calls tagani da sauri ta shiga wayan taga duka number Baban Yaseer ne baci ranta yayi cikin kunkuni