Sashe 49
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawai ta tashi tace “duk wanda kika saya Ammi, bari nai aikin office yau zani saloon gobe nakeso nakoma aiki” Ammi tabita da kallo tace “okay”Wuraren 11 Baba yashigo yana kwalamata kira tana cikin shiryawa itada Ramla datace zata bita dasauri ta taho kofa, wani key mai kyau na benz yace “gashi mijinki ya aiko miki da motansa wai kidinga hawa naki har yanzu ba’a gama gyarawa ba tai condemn” key tadan harara kadan tace “da keke zamu ai Baba ba nisa saloon din” sarai yasan halin yarsa watsamata mugun kallo yayi yace “mijinki yabada umarni kihau tasa motar ke kice keke zaki hau? Hawwa kinsan hukuncin wacce batama mijinta biyayya tarbiyan dana miki kenan? Wlh zan cimiki mutunci fa” Kaman zata kurma ihu ta hadiye abu awuya tasa hannu ta amsa tace “yakuri” murmushi Baba yamata yace “ko Kefa yar albarka yanada kyau mata tadinga bin umarnin miji tafi ganin haske arayuwanta” komawa ciki Hawwa tayi ta zauna turus akan gado ranta dukya baci Ammi tace “uwarfada tashi kuwuce kutafi kafin na sabamiki” mikewa tayi ahankali tadauki black veil na abaya dake jikinta dogo mai kyau ta daura aka tadauki wayanta da handbag Ramla ta fesa turare sannan suka fito, motar na kofar gida wata mahaukaciyan 2024 Benz ce grey, ga ledojin duk ajikin car seats din daga gani kasan sabuwa ce motar har kyalli take, Baba yace “kunfito wuce kutafi” sake hadiye abu tayi awuyanta tawuce Ramla tabita taje zata bude motan tasake tsayawa turus tadan kalli Baba ganin ita yake kallo yasa ahankali tabude motan ta shiga ahankali kaman bataso ta zauna Ramla ka tashigo tace “wowwww Ya Hawwa sabuwar mota ce kal wlh Ya Ibrahim naji dake” mugun kallon da Hawwa tamata yasa taja bakinta tai gum, ganin taki tada motar yasa Baba yadaga murya yace “kuna jiran wani ne? Ko injin ya mutu ne azo aturaku”? Ahankali Hawwa ta tadamotan kaman bataso sannan taja motan ahankali sukabar anguwan motan dadi Ya Allah! Wato better thing money kill am, steering wheel din kaman oil sabida yanda yake juyuwa ta dadi ba irin nataba da kaman tana dambe ba, wayanta ne yashiga ringing tahau kan hanya batare tadauka idanunta kan hanya takai wayan takai kunnenta batare data kallaba cikin murya mai dadi tace “hello” strictly taji muryanshi that sounds kaman yanzu yake farkawa daga bacci yace “da permission din waye kika fita?” Dawani irin sauri Hawwa tazare wayan daga kunnenta number ne kuma Truecaller ta bai fadamata waye ba kashe wayan tayi taidan tsaki ta ijiye Ramla ta kalleta ringing wayan yashiga yi taki kallon wayan ma Ramla tace “Ya Hawwa ana kiranki” ahankali tace “share” har sukakai saloon din kiranta yake, kashema wayan tayi daga baya gabaki daya suka shiga saloon din batason tai kitso kar kanta yayi ciwo kawai tsifa da wanke kan da blow drying shiko aka mata cikin 1hour aka gama tabiya kudi suka fito Khaleel tagani zaune kan bonnet na motanta yadaura kafa daya kan daya dagashi sai short na rick owens nude more like milk, da armani polo mai kyau maroon ga pcap akanshi milk shima dayamai kyau crocs ne akafanshi duk wanda zaiga Khaleel saiya juyo yakara kallonshi cus baimayi kama da Nigerians ba kaman irin black black American people din nan ma har yanda yake dressing, Ramla ta washe baki ganinshi tama wuce Ya Hawwa ta taho wajenshi da gudu tace “Ya Ibrahim ina yini kazo” murmushi kadan yamata yace “Hi Ramla kema kinyi saloon da wanchan yarinyar nan ne”? Yanuna Hawwa dake tahowa sarai tajishi takuma shaka but ta daure sabida Ramla, akunyace Ramla tace “ni yau kwanan kitsona uku saisa banyiba, Ya Hawwa na rako kawai” zuwa wajen Hawwa tayi azuciye zata wucesu tabude mota karaf taji an rike mata hannu kafin tai magana kawai Khaleel ya fizgota jikinshi da shegen zafin nama, kafin tasake magana taji hannunshi cikin nata ya karbe key motan ya wurgama Salman ya chabe yace “take Ramla shopping then home Salam, I want to talk to my wife privately!” Kawai ya kankame Hawwa ajikinshi yana turata baya kunya kawai yarufe Hawwa na masifa, ga Ramla data saki ido baki hanci tana kallon abinda Khaleel kemata, ga jama’a, ga su securities dinshi, she had no choice haka ya dinga turuwanmai har jikin motanshi yakaita yabude kofa yamata rumfa agabanta kaman zaiyi hugging nata yakalleta yace “get in” zatai magana yace “i will kiss and touch you all over kikamin gardama!” Runtse idanu Hawwa tayi ta tabbatar Ramla taji maganan wlh harsu Salman da kowama, kaman zata shige kasa, da kyar tabude idanunta Ramla tadan kalla dahar ta shige gaba abinta tana mata bye tana washe baki na murna da farinciki, da sauri kawai ta juya ta shige without saying a word, shima yashige yana rufo kofan motan yace “let’s go” Aharzuke Hawwa ta kalleshi tace “wai is something wrong with you? How dare you touch me like that a public?” Hannu yasa yazare pcap na kanshi yakalleta babu wasa kan fuskanshi yace “duk randa kika kara fita without kin sanar dani sai ranki yabaci I forgive this one but next one I won’t” tsayawa Hawwa tayi tana kallon ikon Allah abinma sai yasa tai dariyan takaici tace “ikon Rabbi! Auren da Baba yamin dakaine yasa kake wani takama kana feeling kaman u own me?” Kallonta Khaleel yayi baice komiba hakan yasake pushing Hawwa to the wall, tace “guess wat nariga nama kaina alkawari before this 3weeks I will expose who you are to my family! I trust Baba da kanshi zai raba auren nan daya mana I will prove to them cewa you are nothing but a womanizer sai aure aure kaman ayu ga shaye shaye da party BfF din dujal, I’m Hawwa! I can never settle for less! I want a man dayaci sunanshi man not yaro! I want a responsible man not Pops boy! I want a man that shoulder responsibilities not wanda ake shouldering responsibility shi! Ni da kai are two world apart trust me you need plenty years to get to world din danake, so forget kayi abin nan waishi daurin aure but Hawwa can never ever be yours” wani juya idanu Khaleel yamata kaman zaiyi bacci yayi shiru chan yace “feel free! Do whatever you want! Khaleel yariga ya sameki! Dudda kina chan world dinki but without stress na mika hannu na ciroki daga world din nakawoki my own world dakika tsana so much Kululuwa, matar dujal bff” dasauri tawani yunkuro kaman zata dakeshi tace “nace kadaina kirana sunannan!” Murmushi kadan yamata yace “to Yar Sanda!” Wani irin runtse idanu tayi kaman zata dakeshi cus he’s pushing her yayi murmushi kadan baice mata komi ba, afadace tace “ina zaka kaini? Ba hanyan gidanmu bane nan ba?” Dan kanshi ya sosa yana kallonta kaman yanda take kallonshi murya chan ciki yace “we are going to hotel!” Mummunan gaban Hawwa yayi.EPISODE Gidan Mama Jin parking mota a kofar gida yasa Mama dake kokarin shanya zani a igiya tace “waye yazo duka duka ko awa daya cikakke Ni’ima batayi da fita ba yo ko Aliyu ne”? Tana fadin haka tacire hannunta daga kan zanin datake kokarin shanyawa daga igiya tai wajen gate din nasu tana kokarin bude kofan aka turo Ni’ima ke shigowa ga fararen uniform nata ajikinta sai abaya asama dayake abude, ga wani katon envelope a hannunta sai jaka da wayanta da car key a hannunta idanunta sunyi jajir ga ruwa ruwa ma kaman tai kuka, faduwa gaban Mama yayi rass dasauri tace “lafiya naganki gida? Bayanzunan kika tafi aiki ba sai dare zaki dawo? Yanaga kaman kinyi kuka Meya faru”? Envelope din hannunta tadaura akan hannun Mama tawuce tazauna gaban dakalin dakinsu kawai tafashe da kuka mai ciwo da zafi, Mama ta kalleta saikuma hannunta yashiga rawa sosai ta bude envelope din da sauri ta zaro paper ciki ta yarda envelope din akasa ta iya karatu tadanyi makaranta bakinta har rawa yake tace “lICENCE REVOKED LETTER FRON NMCN” takasa karanta surutun data gani sai kawai ta taho wajen Ni’ima tace “ke meke faruwa fadamin bazan iya karatun nan ba tell me” da kyar harshenta har karyewa yake tace “NMCN shine Nurses and midwifery council of Nigeria, sune suka aikomin da letter nan ta asibitin mu wai Leadway hospital sun turamusu video evidence of ni Nurse Ni’ima nazo hospital ina threatening patient nasu da murder, they saw everything a video, and I’ve caused lot of unrest among other patients, some even had panic attack due to tantrums dina, so according to code of conduct Nurses represent life, hope, not threat and fear, plus attempt murder danayi dan haka sunyi revoking licence dina” bakin Mama bari yashiga yi sosai tace “m….me….menene revoking license Ni’ima? Yimin bayani dalla dalla ke” fashewa da kuka sosai Ni’ima tayi mai ciwo, cikin kukan tace “Mama revoking license yana nufin bazan kara iya practicing nursing a any government hospital ko any accredited private hospital ba, Mama infact any registered hospital bazan taba ita aiki dasu ba saidai irin banzayen local quack hospital wanda gwamnati batasan dasu ba ko da zamansu, kuma till further notice sukace babuma ranan dawomin da licence dina, asibitin mu kuma they fire me wai zan bata musu suna” hannu Mama tadaura aka tana kallon Ni’ima data fashe da kuka sosai cus she love her job tanason nursing, it has always been her dream to become a nurse, so taking her license jitayi kaman batada wani purpose kuma, kaman part of her is gone” share hawaye tayi tana huci tace “Mama kuma duk sabida Hawwa ne, nasan ita tasa asibitin suka bata footage din ta tura ma NMCN intentionally Mama, Leadway hospital have no idea ni nurse ce, sannan basusan dawani asibiti nake aiki ba, Mama aikin Hawwa ne wlh, tanada connection din, she did all of this to get back to me” takalli Mama tana huci tace “Mama I will make Hawwa pay for everything datamin wlh tundaga kan rabani da mijina, Mama sainaga bayan Hawwa! Yanda narasa Aliyu narasa soyayyan sa yadinga gayamin ya tsaneni, sannan yanzu narasa aikina, I will make Hawwa loose everything also! Mama na tsani Hawwa! She’s a curse arayuwana Mama! Nima saina zama curse arayuwanta” Mama na kallonta tace “to yanzu yazakiyi eh Ni’ima? Bakida