← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 123

Sashe 48

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dake kallonta tace “Ammi wlh dan shaye shaye ne babu abinda bayasha, banda haka ga auri saki ya maida mata kaman riguna yacire wannan yagaji yasaka sabuwa, Baba ni koshine namijin karshe aduniyan nan bazan aureshi ba na tsaneshi, bantaba haduwa da wanda na irinsa ba, ko kadan baimin ba, kucemai banyin auren, Baba bazan zauna dashi ba” kallon Ammi Baba yayi, Ammi ma takalli Baba hankali tashe Baba yace “Zainabu anya Hawwa ita kadaine?” Dasauri Hawwa tace “Baba nataba maka karya ne? Baba wlh Khaleel dan giya ne ga auri saki ni bazan taba yarda da auren nan ba gaskiya cus shi ba mijin aure bane” sosai Ammi ke kallonta saikuma ta kalli Baba tace “Malam gobe muje wajen malamin dakamin magana muma Hawwa ruqiya” turus Hawwa ta tsaya tana kallon Ammi jin maganan datayi wai basuji metake fada musu bane?Baba ya jinjina kai yace “ba shakka” saikuma yakalli Hawwa dake kallonsu yace “Hawwa bakiso kiyi aure ne kin fiso kiyita zaman gida kawayenki na cimiki mutunci akan mazajensu”? Dafekai Hawwa tayi ganin Baba da Ammi basu fahimcetaba sun dauko magana daban, kaman zata fashe da kuka tace “Baba baku fahimce ni ba, bawai auren ne banaso ba, wanda kuka auramin ne ba mijin aure ba, Baba bakuyi bincike akanshi ba” da dan masifa Baba yace “ke kinyi bincike akan shi ne?” Shiru Hawwa tayi saikuma ta girgiza kai alamun a’a, cikeda da dan masifa Baba yace “sau nawa duka duka kikaje gidansu aikin Noor da aka kiraku?” Ahankali tace “sau biyu” dadan masifa Baba yace “mutumin da sau biyu kika hadu dashi shine zaki dingamai kazafi haka kinsan menene dan giya kuwa?” Yakalli Ammi yace “Zainabu tsakaninki da Allah zaki fadi badan ni ba bakuma dan Hawwa ba, kifadi iyakan gaskiyan ki har zuciya Khaleel yamiki kama da dan giya?” Anatse Ammi ta girgizakai tace “Hawwa ko kadan Ibrahim baiyi kama da dan giya ba, muna ganin yara masu shaye shaye munsani, tundaga kan halayyansu, mu’amalan su, yanayin magana da yanayin bakinsu ana ganewa Khaleel ba dan giya bane” dafe goshi Hawwa tayi ranta yayi masifan baci, Baba yace “kikace yana auri saki Ibrahima yasanar dani tun yana yaro dan shekara ashirin da hudu mahaifiyarshi kemai aure, duk yasaki matan ciki harda mahaifiyar Noor, baitaba neman aure da kanshi ba sai akanki daya ganki yaji kuma yanaso, sabida yayi auri saki ada baya nufin zaiyi dake ke zakiyi abinda za’a sakeki ne? Ga mahaifiyarki anan zata koyardake yanda ake tattalin miji da sauransu”baki Hawwa tasaki idanunta na tsatso hawaye tana kallon Baba dake kare Khaleel kaman irin yayi shekara da shekaru dayasan shi yace “na natsu da natsuwar Ibrahima! Na yaba da hankalinsa da kyauta da sauransu, abinda na lura akan yaron shine yaro ne mai shagwaba wanda daga gani iyayensa sun sangartasa koda kin aureshi abarayin ne zaki iya samin matsala dashi sabida yasaba kome yakeso yana samu, wanda rayuwan nan babu wani bawa da baida aibu, inada nawa kinada naki mamanki nada nata bature yace nobody is perfect” Ammi tace “kwarai” Baba yakalleta sai kuma ya tausasa murya yace “Hawwa agabana aka cimiki mutunci aka zageki aka goranta miki sabida bakida aure kin zaci ina farin ciki da hakan?” Yayi shiru yanuna Ammi yace “an zageta, an zageni, an zagi tarbiyan damuka miki, aka goranta mini, aka kira diyata da tai kwantai, aka miki kazafi, kin dauka ina farinciki da hakan?” Jikin Hawwa sanyi yafara yi, anatse Baba yace “danabar dakin nan jiri ya debeni zan fadi Ibrahima yatareni” Baba yawani kalli saman dakin hawaye na gangaromai daga idanu kaman mai tuna abubuwa da dama yace “Ibrahima ya kamani, yarikeni ajikinsa kaman daman ya sanni daga wani waje, yakaini daki yabani kulawa da agaji na gaggawa, cikin tattausan lafazi yace Baba kadena damuwa zan auri Hawwa!” Sai kawai Baba yafashe da kuka sosai yace “ko yaran cikina basu tabamin hallaccin da Ibrahima yayimini ba, ya fitar dani kunya, yanunamin soyyaya haka yanunama yata, yakawo iyayensa aka daura aure, wani awaje ya sharemin hawaye sai kene yanzu Ina sanar dake namiki aure zaki watsamin kasa a idanu” Baba yafashe da kuka sosai Ammi ta taso ganin da gaske Baba kuka yake tace “Malam dan Allah kayakuri abin baikai ga hakaba ya isa ya isa” Hawwa Baba yanuna yace “Zainab yarinyar nan tasan yanda nake sonta kuwa? Ita kadai nake gani natuna Aisha matata ita kadai, amman maisa Hawwa ke wahalar dani tana bani ciwon kai” wlh at first Ammi tadauka Baba just lie lie cry yake but sosai Baba ke kuka, Hawwa tazo bakin gadon ahankali tadafa kafan Baba tace “Baba dan Allah kayakuri bahaka nake nufi ba dan Allah”Fashewa da kuka Baba yayi yace “Zainab kinsan shekara nawa rabona danai bacci? Wlh tunda Hawwa takai shekara ashirin da biyar batai aure ba daga ranan har zuwa ana gobe zatai hatsari bantaba kwana gari yawaye ban tashi inyi salla inama yarinyar nan addu’a tayi aure tasami miji nagani ba, bana bacci bana iya runtsawa tunanin Hawwa nake, sai ranan da aka daura mata aure shekaran jiya shine nai bacci sai asuba natashi da jiya dakuma yau in 4yrs ina abu daya sai ranaku ukun nan na iya bacci sabida na aurar da ita” dasauri Ammi itama tace “Malam meyayi zafi haka? Dan Allah kayakuri ya isa” takalli Hawwa dake kukan bakin ciki ganin abinda Baba keyi sabida dan iskan Khaleel tace “Hawwa I know concerns naki, tunda ba kisan kai Ibrahim yake ba, ko saida yara, ko fashi, ke kaddarama yana shaye shayen ke ba matarsa bace? Ai mata Allah yabasu power da suna iya gyara mazajensu from bad to good, banda haka bayan Baba yazo damaganan na jera kwana biyu a asibiti ina alwala nayi raka’a biyu nayi du’aul istikhara wlh naji na natsu da Khaleel and it’s a sign auren ku zaiyi albarka, Hawwa koma meke damunki dake hanaki aure fight it this time, karki bari shedan yayi nasara akanki, auren nan yanda aka daura an daura kenan har abada kibar zancen rabawa” baki Hawwa tabude zatai magana Baba yadaga mata hannu.EPISODE Cikin bacin rai Baba yace “idan kalma mara kyau zaki fadi akan Ibrahima na kiyi shiru kada ki fada don yana sosamin rai” shiru Hawwa tayi batasan me Khaleel yamusu ba especially Baba imagine ma harda Ammi, dukansu biyun basu yarda da itaba, just for peace Baba yadena kukan nan zata yarda tai shiru amman tai alkawari saita nunama su Baba waye Khaleel she will bring evidence and everything dan kome za’ayi ayi she will never ever accept yaron Pops din nan amatsayin mijinta ba!. “Hawwa kinji abinda muke fada miki?” Kallon Ammi tayi fuskanta ta share tass da bayan hannu ta kalli Baba tareda kakalo murmushin dole tace “naji shikenan na yarda babu komi” wani kayataccen murmushi Baba yayi yana share fuskanshi sai kawai ya rungumeta kaman zai cinyeta yace “nagode Hawwa, banso na tursasaki kiyi abu, nagode dakika yarda” sakinta yayi yace “cikin kudin sadakin nawa kike bukata nabaki inaso naba Ammin ki sauran asayo miki kome kikeso Ibrahim yace sati uku on 24th ne taron biki” wani abu Hawwa taji ya tsayamata awuya amman dai ta gyadamusu kai Baba yace “zamu fara shirin biki wannan gwal din kuma nida Aminu zamuje banki gobe mu boyemiki, yanzu gayamin nawa kikeso a kudin?” Ahankali tace “banson komi Baba kuyi abinda yadace inada dan kudi ai ni” Baba yace “to shikenan zan dauki ko miliyan goma ne nasai miki filaye kisami kaddara sauran kudin ayi kayan aure dasu da gara” Ammi tace “zanje Zaria jibi nadan shiryo nadawo saimu fara shirye shirye bakama hannun yaro afito da anko sabida kowa yasami dinki tunda lokaci ya kuro” Hawwa kawai tai shiru tana kallon Baba da Ammi dake planning sosai zuciyanta na kuna tana durama Khaleel ashar kirjinta na radadi kaman zata kama da wuta cus tasan auren is nothing but a game.Har tai bacci tabarsu awajen planning bikinta Ammi da Baba suke wlh ko Baba ne amaryan sai haka. wuraren 3 na dare ta farka tareda taba wayanta tadan haska Ramla ne ke kusada ita tana bacci, sai Ammi a bakin gadon ta dayan edge din, kankame jikinta Hawwa tayi abin yataso mata what is wrong with her? She’s on MP fa though tagama da asuban nan zatai wanka tafara salla, haushin kanta ta shiga ji sabida tunawa da yanda Ni’ima use this feelings against her, iska ta fuzar ahankali ta zame ta sauka kasa sai kawai ta sulale ta kwanta akasan tiles din dakeda sanyi, kusan 20mins tana ahaka kafin yasoma lafawa bacci ya kwasheta anan wajen, cikin bacci taji ana kiran sunanta da sauri tabude ido Ammi ce ta kunna wutan dakin tace “badai Ramla ta turoki kika fado kasa ba?” Danne kunyan datakeji tayi tace “Ammi nakan fado kasa haka wani zubin” Ammi tace “ahh lallai sannu iyayen bacci mara kan gado, idan zaki wanka yanzu nasa ruwa a wuta bayau zaki fara salla ba?” Gyadama Ammi kai tayi ta tashi tana cire kaya Ammi tahau dadduma ta kabbarta salla wucewa tayi tafice Ammi tajuyo wlh tunda ta farka Ammi ta farka sabida ijiyan zuciyan dataketa saukewa abinda yatasheta kenan, saikuma sauka datayi kasa aranta Ammi tace “kodai tama Baba magana ne ayi bikin next week akaita kawai”.Dawowa dakin tayi tazauna gaban madubi tana kallon kanta dayayi tsufa ahankali tace “anjima zanje saloon” tuna zancen Baba ya auramata Khaleel sai kawai taji ranta yabaci kwafa tayi she has plan she will show Baba waye Khaleel she will get evidence, saita nunama yaron nan ita ba kalan sauran matan daya saba aure bane, she don’t want him so bazata taba zaman auren nan ba, 3weeks is morethan enough for her to show Baba evidence kan waye Khaleel even if it means nemo all matan daya aura adah.Wani simple riga da skirt tasaka tadauki dadduma ya shimfida itama tai salla suka idar ta gaida Ammi, Ammi tace “yajikin?” Ahankali tace “lpy lau” murmushi tamata “zanje zaria nataho damai gyaran jiki, dakin chan da akasa tarkace Baba yace yau duk zaisa afitar dasu a gyara tsaf anan za’a dinga tara abubuwan ki da za’a siyo mai gyaran ta sauka anan, saikuma inaso ki gayamin wani kalan kayan kitchen kikeso?”Ita abinma dariya yadan bata sai
Chapter 48 · 0% Book details