Sashe 59
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
me? What did I tell you about that girl ranan nan? Ni da mahaifinki nan mun gayamiki Ni’ima bata kaunarki kona miskala zarratin, ta tsaneki, kukanta kukan mazuru ne, kukan karyane da yaudara, so tabiyoki jiya office kika bari tazo, kinsan cewa Ni’ima ta dauki wayanki a sace ta kwashi number mijinki?” Hawwa dake dafe da kuncinta tana kallon Ammi da mamaki tabude baki in disbelief, tace “Ammi karya yamiki kawai ya tsani Ni’ima ne” “kinci mai garinku Hawwa kaniyanki” Baba yamata dakuwa yatsunshi kaman zasu shiga kwayan idanun Hawwa yace “mijinki kike kirada makaryaci”? Sauka kanta tayi kasa ahankali, Ammi tace “ta aikama Ibrahim sako cewa DIG oganki, Abraham da duk duka samarinki dasuka gudu jikinki kike basu suna amfani dake” dawani irin sauri Hawwa takalli Ammi, Ammi tace “tayi amfani da wayan masu bara jiya at exactly 2:15 ta tura” shiru Hawwa tayi basu wani dade da rabuwa ba aka tura sakon, Ammi tace “he tracked the number masu bara sukai kwatancen ta da motarta you are lucky bai sakeki ba Allah yaga zuciyanki yabaki miji mai sonki da tsaya miki haka” Ammi ta nuna kanta tace “idan har ni Ammin ki Zainabu na kai mahaifiyarki na isa dake, dagayau namiki iyaka da Ni’ima baki ba ita! Ko wayanta kika kara dauka ban yafemiki ba Hawwa!” Sosai Hawwa ke kallon Ammi, Baba yace “nima idan na isa nakuma kai matsayin mahaifi agareki namiki iyaka da Ni’ima har abada! Ni’ima bata kaunarki! Ta tsaneki, bakin ciki take dake, idan Ni’ima tasami hanyar kasheki zata kasheki Hawwa, dan haka bassss! Bassss! Enough! Bake ba ita, da raina bazan bude idanu inga kawa na neman kashema y’ata auren da ba’a riga an kai daki ba, tundadai an baki hutu awajen aiki dagayau na ijiye dokan kada ki kara fita daga gidan nan unless shi mijin naki ne yazo yanaso yafita dake, sa hijabi muje gidansu Ni’ima Zainabu”.EPISODE Koo kadan jikin Hawwa ba karfi jin abubuwan da su Baba suka fadi, dafe katifa tayi tazauna ahankali tai shiruuu tana tunani, duka abubuwan da Ni’ima tamata abaya she kind of give her excuse sabida Aliyu duk shi yaja da sauransu, so tasan ba kowa ya iya handling kishi ba, kuma tasan yanda Ni’ima ke mugun son Aliyu, so tamata excuse dudda she goes as far as tana zagin iyayenta tana tonamata asiri, but this! Yaushe ta dauki wayanta harta dauki number Khaleel dabatai saving ba? Takasa yarda still, kodai Khaleel sheri yayi mata da karya sabida ya tsaneta? Sai kawai ta tashi da sauri ta dauki wayanta takira Abraham ringing daya ya dauka tace “Abraham I remember kataba cewa kasa wani invincible CCTV camera an office dina right?” Dasauri yace “yes Miss Hawwa” ahankali tace “can you send me footage na jiya at about 1Pm zuwa 2pm” Dasauri yace “sure give me 3mins” ta katse wayan ta zauna tana kada kafa she really don’t wanna believe Ni’ima did all this dasu Baba suka fadi noo! Ni’ima tai nadaman everything datayi abaya, she’s a changed person, kishin Aliyu yasa tayi all those things ada.3min basu cikaba Abraham yaturo mata video ta watsapp dasuri tashiga downloading yana gamawa tabude dasauri tashiga kallo gabanta na mugun faduwa tana cewa kanta No No Ni’ima can’t do this to her, aiko saiga Ni’ima na daukan wayanta tana daukan number tana kallon kofa atsorace, wani irin runtse idanu Hawwa tayi murya araunane dake cikeda mamaki tace “Ni’ima!” Ijiyan zuciya ta sauke ta fuzar da iska mai dumu ta ijiye wayan a gefe, she’s really hurt dudda bataga text dinba but for Ammi to slap her this hard that means she said alot tabata mata suna, dole Khaleel yaji ba dadi zaiga tana crucifying nashi on something da itama tanayi, fuzar da iska tayi bataso tayi kuka akan Ni’ima yau but zuciyanta namata wani iri kaman ma idan tai kuka zaifi rage mata zafin dayake mata yanzu.Hawwa na zaune a wajen idanunta sunyi ja almost 1hr dafitan su Baba da Ammi taji ana bude kofanta dasauri tadago kai, ganin Khaleel again saida gabanta yafadi da sauri taboye wayan dake hannunta na video akasan bedsheet sabida karya ga video, yana shigowa babu wata wata kawai yazo inda take zaune tana kallonshi, hannunshi yasa yakamata yadagata yajata turjewa tayi tace “stop touching me ina zaka kaini kuma”? Cikin bacin rai Khaleel yace “i want to show you wacece wacce kikai considering as true friend” kawai yajata takalmi tasaka sukai waje takasa kwace hannunta Salman yabude musu bayan mota ita tafara shiga sannan shima ya shiga aka rufe motan aka ja, to her biggest suprise hanyar office nata taga sunyi, dasauri takalleshi tace “ina zaka kaini?” Banza yamata yaki amsata har office nasu, parking yayi yana rikeda hannunta suka wuce ciki har zuwa office na DIG kai tsaye Khaleel yabude office din batare dayama yi knocking ba, DIG Hawwa tagani tareda Abraham duk zaune, DIG na ganinshi da sauri DIG yatashi yace “Mr Ibrahim I……” hannu Khaleel yadagamai strictly yace “did you bring her here yes or no?” Rai abace DIG yace “not just she duk ma wani wanda ke gidansu cus I will never take this defamatory statement likely” yakalli Abraham yace “bring everyone in” wucewa yayi yafita chan saiga wasu manyan yan sanda guda biyu sun shigo da Mama da Ammi sai Baba da Ni’ima dake sanye da doguwan rigan atampa dukansu sunyi zuru zuru dan duk suna zaune suna magana agida wasu yan sanda sukazo sukace ana inviting nasu to police station dukansu haka suka taho, Baba na ganin Khaleel da Hawwa yace “Ibrahima me kukeyi anan? Munje gidansu yarinyar nan ana cikin magana saiga yan sanda akace muzo chaji opis” ahankali Khaleel yace “nina turasu Baba” hannun Hawwa yasaki gently yasa hannu ya karbi karafunan Baba ya zaunar dashi a kujeran wajen yakalli Ammi yace “Mom sit” zuwa Ammi tayi ta zauna, gaban Mama dana Ni’ima suka shiga bugawa especially gaban Ni’ima dabatasan meke faruwa ba gabanta sai fadi yake cus su Baba dasukazo cewa sukayiwa Mama basuson yarta tareda Hawwa basuce komiba, kawai faduwa gabanta yake dudda bata kawo text messages na jiyaba dan batajin za’a iya gano ita bane, Hawwa takalla cikin makirci tace “Best is everything okay? Why did you call us here”? Wani daci Khaleel yaji aranshi yanda take kiran matarsa wani best azafafe yace “wlh kika amsa that beast sai ranki yabaci” yafadama Hawwa dake kallon Ni’ima jikinta yagama sanyi da Ni’ima sosai, faduwa gaban Niima yayi itama Hawwa tadauke kai kawai Ammi saitaji wani son Khaleel ya lullubeta.Anatse DIG yakalli daya daga cikin yar sandan mata dake taredasu Mama, ba zato ba tsammani Ni’ima taji saukan bulalaaa akafanta dayasa kawai ta zube akasa tace “wayyooo Allah na” dasauri Hawwa ta juyo jin karan bulala da dukan Ni’ima, Yar sandan tace “mai laifi kneeling yakeyi ba tsayuwa ko zama ba a police station” rawa jikin Mama yafara dasauri ta duke itama kusa da yarta, DIG yakalli Ni’ima da kafafunta ke bari sabida zafin wayan inji yace “kece Ni’ima?” Gyadamai kai Ni’ima tayi tace “eh yallabai nice” gyadamata kai yayi yace “an shigo da karanki office dina daga Mr Ibrahim akan kinyi defaming matarsa, dakuma ni, da yaron aiki na” yanuna Abraham dake tsaye ransa abace yana kallon Ni’ima, DIG yace “No body ya isa yabata min suna, idan kowa na dakin nan yabarki ni bazan barki ba!” Faduwa sosai gaban Ni’ima yake tace “yallabai bantaba ganin ka bama, saidai wanchan na sansa ta dalilin Hawwa amman me dalilina dazaisa nabata maka suna wani sherin aka kulla min ne? Best something yafaru ne”? “stop calling matana da Best!” Khaleel yafada aharzuke kowa ya kalleshi har Hawwa dasauri dan kaman zai rufe Ni’ima da duka, DIG yace “calm down Mr Ibrahim” rike kansa Khaleel yayi kirjinshi na tafarfasa yayi punching air, DIG yace “jiya wuraren 2:16 kin tura sakonni marasa dadi zuwa wayan Mr Ibrahim”? Faduwa sosai gaban Ni’ima yayi ta zaro idanu tareda dafa kirjinta Mama na kallonta hankalinta atashe Ni’ima tace “Yallabai an ina zan sami number sa har na turamai sako? Ni kuma? Sheri akamin” Dan murmushi DIG yayi yakalli Abraham yace “play the first evidence” saramai yayi yace “yes sir”.EPISODE Wucewa Abraham yayi yana connecting laptop nashi to office television sai kawai ga video Ni’ima sanda take kwashe numbers daga wayan Hawwa, Hawwa na kokarin shigowa ta ijiye wayan da gudu, Mama tace “na shiga uku na lalace Ni’imaaaa” yanda kirjin Ni’ima ke rawa zaka dauka an sokashi da electricity ne, Hawwa ta tsareta da idanu just looking at reaction dinta, Ni’ima da sauri ta kalleta tace “Bes…..Hawwa I can always take anything daga wayanki, baki tabamin shamaki da wayanki ba, kaman yanda ban miki da nawa ba, ba lallai number Khaleel na dauka ba ai, abinda na kwafe daban fa number Ammi na dauka inaso namata sako na bada hakuri naga bata hakura ba” Baba yace “shegen karya kaman bokanya! Yau za’ayi maganin ki” DIG yadagama Baba hannu Ammi tace “kai shiru Malam” Baba yace “raina sosuwa yake ne Zainabu Amman nayi” DIG yace “bring in the second evidence” fita yan sandan sukayi chan sai gasu sun shigo da beggars din nan su biyar duk jikin su na rawa, Ni’ima jikinta yafara bari sosai data gansu, Hawwa kawai saitaji Hawaye yazo idanunta zuciyanta ya tsinke ganin reaction na Ni’ima so ita ta tura text din, DIG yace “zaku iya nunamin acikin dakin nan matar datazo tayi amfani da wayanku jiya bayan karfe biyu” dawani irin sauri dukansu sukai wajen Ni’ima dake susunnar dakai suna cewa “gata nan gatanan itace tabamu dubu biyar bayan tagama” DIG yace “fita dasu a sallamesu” sutafi ficewa dasu akayi.Ni’ima jikinta yahau rawa, in her wildest dream bata taba tunani abinda tayi jiya will backfire like this ba before 24hrs like this is just 11 na safe, tadauka ma dazu dasu Ammi sukazo sunzo suce an fasa auren, Khaleel ya saki Hawwa ne fa, sai kuma taji suna magana kan arabata da Hawwa. Dasauri Ni’ima tashiga jan guiwa tafashe da kuka tana zuwa wajejen da Hawwa take tace “Hawwa wait I can explain, wlh wlh sherin shedan ne kuma harda naji haushi dakika ki kiramin Baban Yaseer…………” Tasssss! Aka dauketa da mari da saida ta kwanta flat