← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 123

Sashe 36

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mana, Baba yaro ko shekaransa dari yana bukatan iyayensa su kula dashi, ku kula da ita dan Allah, ku taimakama yarku cus BP ta yayi high sosai, ku bata farin ciki, ku kauda mata damuwan and support her, BP yatashi yasa tai loosing control kanta tana tuki harta hada hatsari, hawan jini muguwan cuta ce da tashi daya takan dauki ran mutum, dan Allah akiyaye, babu maganin dayafi aiki kaman maganin iyaye a rayuwan yaransu, menene maganin nan danake magana akai? Shine support na iyaye da love da mantar da yaransu damuwa da bama yaran farin ciki da natsuwa……” Dr yaciga da advising Ammi da Baba sosai……Around 1:30 yashigo asibitin parking yayi yasauko yawuce ciki, ganin baiga Baba ko Ammi wajen ba yasa yayi wajen dakin da Hawwa keciki ya leka ta glass na kofan idanunta biyu amman idanun sun kankance sosai irin na mara lafiya tana kallon waje guda tai shiru tana tunani, daga ita sai dogon ringan jikinta ga gyalenta an rataya wajen bag hanger dake gefen wardrobe na dakin gashin gaban goshinta dukya kwanta luplup ansa bandage a goshinta hakama hannuwanta duk bandage wani kalan sonta da bala’in tausayinta ne ya mamayeshi kaman ya shiga ya karbe ciwon daga jikinta, hannunshi yakai yabude kofan gently yana shiga ciki, ahankali Hawwa ke juyo da kanta kadan da kadan dan har yanzu kanta na banging saidai ba kaman dazu ba so da kyar take juya kan kallo kofan dataji an bude tayi tahada idanu da Baban Yaseer daya shigo yana mata kallon tsantsan so kaman zai hadiyeta, faduwa gaban Hawwa yayi kaman taga dodo tashiga mikewa tana tashi daga kwance dasauri ya yunkuro zai taho yace “don’t move Hawwa ina zaki”? Da muryanta da baya fita sosai cikin rashin lafiya tace “karkazo nan!” Chak ya tsaya daidai tana tashi zaune da kyar idanunta har layi suke kanta yafara kwankwatsa sabida yanda ta tashi, dafe kanta tayi da hannunta da drip ke makale tana damtse idanunta cus her head is pounding kaman ana daka a turmi da kyar tace “kafita Baban Yaseer!” Cus bamata kaunan ganinshi arayuwanta, kallonta Baban Yaseer yake kaman yau yafara ganinta ahankali yace “Hawwa nafita kuma why? Nine fa? It’s Aliyu, Kinsan yanda nake cikin damuwa kuwa?” Ganin yanda yake wani irin kallonta zuwa kirjinta dan andan zage zip na bayan dogon rigan, tashin datayi yasa gaban rigan ya zazzago sama saman kirjinta na showing, da sauri tarike gaban rigan da hannu daya dayan hannun takai bayanta taja zip da mugu karfin hali Hawwa ta sauko da kafafunta daga gadon adan tsorace Baban Hawwa yakara yunkuro wa zai taho yace “ina zaki Hawwa sit please you’re not well, me kikeso ki dauka? I can give it to you”hannunta daya akai dayan ta daga ta nunashi tana haki tace “kafita I don’t want to see you! Stay away from me Baban Yaseer” yana kallonta gently and softly yace “har abada bazan taba ita staying away from you ba Hawwa” ganin yacigaba da kallonta yasa Hawwa ta diro daga gadon danta dauki gyalenta datagani a hanger kawai ta zube akasa babu karfi ajikinta ko digi kaman kafafunta basa aiki tai wani kara tana kama kanta da duka hannun biyu tace. “Kainaaa uhnnnnnn”Dagudu Baban Yaseer yayi wajenta without having a second thought sabida tsabagen yanda yarude kawai yakai hannunshi yadauki Hawwa dake kasa idanunta a kulle takama kanta da duka hannuwa biyun jin an dauketa yasa Hawwa tabude idanunta da kyar dan kadan suka hada ido da Baban Yaseer hawaye masu zafi ne suka fito daga idanunta cikin muryan da baya fita bamata da karfi sosai tace “Baban Yaseer kaji tausayina kafita daga rayuwana! Ka ijiyeni! Stop touching me, ka ijiyeni nace” tai maganan tana lumshe idanu ta rirrike kanta, yanda hawaye ke fita daga idanunta tana magana kasa kasa kaman yar baby ya kashema Baban Yaseer zuciyan he just wants to kiss her and hug her so damn tight, kofa yakalla ganin babu kowa dake tahowa yasa ahankali yashiga sauke fuskanshi zuwa daidai fuskan Hawwa he just love Hawwa and feels like kissing her baimasan meyake ba, fuskanshi na dab da sauka anata akai mahaukacin bugokofan dakin dayasa yadago kanshi da gudu Hawwa tabude jajayen idanunta da kyar suka kalli kofan suna hada idanu da Ni’ima data bugo kofan tana sanye da abaya idanunta sunyi matsiyacin ja tana kallon Baban Yaseer daya dauki Hawwa ajikinshi kaman yanda yake daukan su Yaseer da Yasmeen, adaidai lokacin kuma Baba da Ammi na zuwa wajen duk sukaci tura suka tsaya abayan Ni’ima duk suna kallon Baban Yaseer, yanda gaban Hawwa yahau bugawa ganin Ni’ima ta dauka kirjinta zai fashene da sauri ta shiga kokarin kwace kanta batama da karfin motsi abin gwanin ban tausayi tana kallon Ni’ima Baban Yaseer kuma yariketa gam ajikinshi yana kallon Ni’ima, wani kalan mosti fuskan Ni’ima yafara tana huci tace “ba kiss zakuyi ba”? Tayi mahaukacin ihu tana daukan kujeran datagani adakin tayi kansu tace “ka sumbace ta mana Aliyu…….” EPISODE Kyakkyawan baccin gagaran Khaleel yayi danko 30 minutes baikaiba ahankali yabude idanunshi yana juyowa daga rub da cikin dayayi yana kallon saman dakin baimasan meke damunshi ba, normally yakamata yayi bacci har zuwa 4 na yamma but yakasa baccin tunanin yarinyar chan kawai yake, kaman her sick spirit na kiransa, hannunshi yadaga yakalla da Hawwa ta ciza lumshe idanu kawai yayi yabude sannan yatashi zaune yasauka daga gadon, boxer yacire ya yar awajen yawuce abinsa naked yafada bathroom yayi wanka yafito yawuce walk in closet dinshi dake kama dawani exquisite boutique, shiryawa yayi yazaro Balmain monogram print flowing shirt dakeda kalan black print din kuma white yasaka, yadauko dogon denim wando na Diesel yasaka daya zauna ajikinshi da kyau dasdas, agogonshi yaciro from drawer na designers watch dinshi, yacire Furlan Marri yasaka dayama hannunshi kyau, yadan juya yakalli showglass na takalmansa kaman shago yasa hannu yaciro wani suede flat takalmi na Birkenstock Boston, sannan yadau turarukanshi yashiga fesawa yadauki brush yana taje kansa ya shimfada dadduma yayi sallan azahar sannan yamike yabude kofa yafito yasauka kasa, chan falo yayi yana kallon agogon hannunshi is 1:30 ba kowa afalo probably Mommy ta kwanta ko tana spa nasu ana mata massage, kofa yawuce aka budemai yafita wajen black Mercedes Maybach S class dinshi yayi dake kyalli tsabagen kyau da kudi, da sauri security nashi suka taho wajen yakalli Salman dake budemai motan yace “when did you come back?” Dasauri yace “not quite long Sir everything is sorted babu wani matsala motanta I called auto shop sunzo sun dauka har an fara gyaransa” yatsine fuska yayi kadan baice kome ba ya shiga bayan motan ya zauna, Salman ya maida kofan yarufe yakoma gaba yashiga ya zauna driver shima na shiga mopol dinshi ma haka, anatse yace “hospital” Dasauri driver yace “yes sir” yatada motan suka fita yana kallon hanya chan yace “music” waka aka samai yafarabi yanadan shaking kai yadaga wayanshi yayi selfie yasa a instagram story nashi hankalinshi kwance.*Kansu Ni’ima tayi da plastic chair data dauka dasauri Baban Yaseer yajuya yana sauke Hawwa agadon yajuyo yasa hannu da zafi zai karbe kujeran ta zame tai gefenshi zata rafkama Hawwa dake kallon Ni’ima completely heart broken Baban Yaseer yabude hannuwanshi ya tsaya agaban Hawwa, Ni’ima tace “kama rungumeta idan zakayi amman saina halakata, saina halakata wlh, Allah ya kasheki ya dauki ranki sai inga wazakaso Aliyu? Inaso naga ko zaka bita kabari kuyi soyayya, ba sumbatar juna kukeso kuyi ba kuka ganni kuka wayance? Ka tashi agabana” hannu daya Baban Yaseer yasa ya fizge kujeran daga hannunta yana kokarin ijiye chair a gefe tabi gefenshi zatayi kan Hawwa taji an riketa gam juyowa tayi daidai Ammi na dauketa da mari jikake tasss! Hawwa ta zabura tana kokarin mikewa ganin yanda Ammi ta zubamata mari but takasa tashi, Ni’ima ta dafe kuncinta tana kallon Ammi da jan idanu, Ammi tace “kika kara maganan banza anan saina sake daukeki da wani marin shashasha” Ammi takalli Baban Yaseer dake tsaye yana kare Hawwa cikeda fushi tace “tashi agaban yarinya na bar wajen nan, tashi nace!” ba musu yatashi ahankali yakoma wajen kofa ya tsaya ranshi in yayi dubu yabaci sabida abinda Ni’ima keyi, Ni’ima takalli Ammi idanunta jajir har lokacin kallon Ammi take tace “kika mareni Ammi? Ko uwata bata taba bari naba saike”?Ammi na kallonta jin maganganun datake rai abace tace “saisa ni nake tayata bawa diyarta tarbiya, kika karamin gara gara anan saina sake daukeki dawani marin, you’re very, very and very stupid Ni’ima hauka kikeso kiyi sabida namiji? Eh?” Shigowa Baba yayi zuwa wajen ya tsaya kusada Ammi babu alamun wasa akan fuskanshi yace “meke faruwa Zainab”? Ni’ima Ammi ta nuna tace “Malam Ni’ima tana daya daga cikin dalilan dayasa Hawwa kenan wajen” azuciye Ni’ima tace “menayi? Nakira yarku na yanke alaka da ita, naja mata layi, bansonta arayuwana dayake mayya ce, bakar mayya mara zuciya ce ita wacce tai kwantai haka ta dinga bina tanajan gwuiwowinta akasa tana rirrikeni tana kuka tana karna rabuda ita, nikuma na tattake hannuwan banzan nawuce nayi tafitata” sosai Baban Yaseer ke kallonta hakama Baba da Ammi yanda take magana kaman ba Ni’ima ba, can a sweet person turn monster over night? Sabida namiji? Ni’ima tace “mijina nawane kadai wlh, ba best friend ba ko kanwata ce saina jamata layi wlh, kugayama yarku tafita daga harkan mijina” nuna Baban Yaseer Ammi tayi tace “ga mijin naki nan ai shiya kawo kanshi nan, dau abinki kubar nan” cikeda rashin kunya tace “eh zan dauki abuna amman saina gama, yar iskan yarku kokarin sumbatan mijina take, mara kamun kai da natsuwa, Hawwa zata iyama maza fyade sabida tsabar bukat……” tsawa Ammi daka mata tace “Ni’ima!” Rai abace sosai tace “nasan waye Y’ata! Jedai ki bincike mijin naki, munsan kalan tarbiyan da muka bata” ganin Ni’ima zatai magana tabi Ammi da chachan baki yasa Baba yakalli Baban Yaseer strictly yace “Aliyu dauki matarka kutafi, mungode Allah saka da alkhairi” cikeda tsantsan rashin kunya Ni’ima tace “ba dole kace ka gode ba anci kudin mijina an koshi, yazo yabiya kudin asibiti da kudin magani, mayu kawai kwadayayyu masu neman kai da yars……” fizgota Baban Yaseer yayi yajuyo da ita tai facing nashi ganin abin nata yazama hauka yadaga hannu zai kwasa mata mari Baba yace “kul!”EPISODE
Chapter 36 · 0% Book details