Sashe 33
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kafin yakarasa maganan yaji kukan mutane dayawa, Baffa yace “ya sunan asibitin”? Ahankali Khaleel yace “Leadway” “to mungode gamunan zuwa, mu muna zaria zankira Babanta yanzu zai taho”Baba na zaune a kofar gida yaga number Ammi na kiranshi kin dauka yayi chan saiga number mijinta Baffa hakan yasa yadauka yana kokarin mai sallama Baffa yace “Malam yanzun nan aka kiramu da number Hawwa” faduwa gaban Baba yayi sosai bana wasaba yace “Hawwa, Hawwa? Batajin dadi ai taje asibitin su Ni’ima” Baffa yace “wanda yakiramu yace tayi hatsari amman ka kwantar da hankalinka tana asibitin Leadway nan aka kaita katashi kaje ana neman yan uwanta na jini badai musan me ake ciki ba” salati Baba yafara yana sallallami baima tsaya yakarajin wani bayani da Baffa keyiba da sauri yamike yakoma ciki yana salati kaman wanda ya haukace duka kudadensa dabaya kashewa ya tattaro yafito yana salati kawai. “Innalillahi wa Innailaihi Raji’un, Ya Allah Hawwa na, Ya Allah y’ata, marainiyata Ya Allah, Innalillahi Wa Innailaihi raji’un, Allahuma ajirni fi musibati, Lahaula walaquwata illabillahil aliyul azeem” salati kawai Baba yake ko kallon Umma dake tambayanshi lafiya baiyiba yafito luckily saiga keken daya sauke mutane zai juya taresa Baba yayi yashiga yafadamai sunan asibitin yashiga still salati yake.A gate na asibitin aka sauke Baba ya shigo baya hayyacinsa dauriya kawai yake irin na maza da crutches nashi yake dungurawa yana hoping yana shiga yana kallon asibitin da tunda yazo duniya baitaba ganin asibiti mai kyau irinsa ba yana kara tsorata yana addu’a Allah yarufa musu asiri, Khaleel na tsaye a reception din yana waya Baba yashiga kiciniyar turo Glassdoor dakeda karfi da aka rubuta push ajiki, tsabagen yanda baida karfi kuma yarude baisan sanda karfenshi ya turgude yafita daga hannunshi ba Baba yafadi tim karafunan ma na zubewa dan takalminshi na kafa daya dayake sawa shima yafita yayi tsalle zuwa wani waje, dasauri Khaleel dake waya yadago jin kara ganin tsoho mai kafa daya yafadi hakama crutches nasa yasa dasauri yacire wayan daga kunnenshi yayi wajen kafin others suzo yarigasu yabude kofan yafita da sauri, one thing about him tun yana yaro yanada tausayin masu nakasu any disabled person have a special place a zuciyan Khaleel.Ahankali yaduka agaban Baba yakai hannayenshi yakama kafadan Baba da jikinshi ke rawa yana ambaton Allah har lokacin sama, cikeda tausayi yace “sorry” tsayuwa yayi da kyau yana jingina da bango yana kallon fuskan Khaleel dahar ya duka yana kwasanmai crutches din yataso yabashi da sauri, ahankali yace “sorry, are you hurt anywhere”? Yashiga duba Baba yana kakkabemai gaban riganshi yasake komawa yadaukomai slippers nashi wari daya ya duka gabanshi ya ijiyemai Baba yasaka, Khaleel yasake tasowa for the first time yayi hausa ganin kaman mutumin bai gane turenci ba yace “kaji ciwo? Akwai inda kema zafi?” Girgizamai kai Baba yayi yace “thank you Allah maka albarka babu inda kemin ciwo y’ata ne dai ke ciwo” Kaman zaiyi kuka yace “kirana akai y’ata Hawwa tayi hatsari tana asibitin nan ko kasan inda ake tambaya? Ni wama yakawota nan? Bamuda kudin biyan irin wannan asibitin, Innalillahi wa Innailaihi raji’un Allah karufamini asiri” Baba yana maganan yana kalle kalle he’s just distabilize, ahankali yasa hannu yamai pushing door din, Baba yasake kallonshi yace “nagode kaji” yashiga ciki Khaleel yabishi, sannan yamai pointing dakin da Hawwa take ciki yace “kaduba wanchan dakin” dasauri Baba ya kalli Khaleel saikuma ahankali yace “nagode ko yaro ya sunanka”? Dan kyafkyafta idanu Khaleel tayi sau biyu yakai hannunshi ya shafa kanshi kaman mara gaskiya ahankali yace “Ibrahim Khaleel” ahankali Baba yace “nagode Allah maka albarka Ibrahima bari naje” gyadamai kai Khaleel yayi ahankali Baba yawuce Khaleel yabishi da kallo saikuma yawuce yafita dasauri.Baba na kaiwa wajen dakin ya hango Hawwa kwance ga bandage a goshinta da hannunta shima ansa bandage ga ciwo a lips dinta sosai an samata drip kala uku all at once bude dakin yayi yashiga yana salati da sallallami yarike hannun Hawwa kawai saiya fashe da kuka yama kasa magana, shigowa dakin akayi wata nurse ce tace “sannu Sir kaine mahaifinta”? Dagowa Baba yayi yana share hawaye yace “eh” tace “Baba muna bukatan information nata dakuma signature” ijiyan zuciya Baba yasauke yana karban takardan gabanshi na faduwa yace “toh Allah karufamana asibiti nawane duka abubuwan nan? Nawa zamu biya?” Dan murmushi nurse din tayi tace “karka damu Baba bawan Allah daya kawota yabiya kudin komi tatas” Dasauri Baba yace “ohh Allah waye shi? Yana ina nagode mai”? Murmushi nurse din tayi tace “ai naganku tare just now kuna magana awajen kofa” baki Baba yarike yace “Ibrahima? Yanzu shine daman amman shine bai sanar dani ba kuma harda nunamin dakin, to Allah yamai albarka, Allah yarabashi da iyayenshi lpy, bari nayimai godiya sainazo na cike” yamika mata paper zai tashi dasauri tace “yatafi ai” yadai ijiye wayanta da jakanta dani, ijiyan zuciya Baba yasauke saikuma ya shiga rubutu, tass Baba yayi komi yabata tafita chan takawomai wayan Hawwa da jakanta Baba ya karba yana tofamata addu’a, Ammi tashiga kiranshi dagawa yayi Ammi na kuka sosai tace “Malam kakai wajen Hawwan yaya take”? kaman ba Baba ba yace “ya isa ya isa dena kuka gatanan dai Alhamdulillah banga likitan tukunna ba amman ance convulsion tayi a mota harta jawo hatsari wani bawan Allah yakawota asibiti yabita kudin komi” cikeda damuwa Ammi tace “Alhamdulillah Alhamdulilah nima ina hanya” Baba yace “Allah yakawoku lpy” wayanshi Baba yadauka yashiga kiran Ni’ima ya sanar da Ita kawarta tai hatsari amman baya shiga hakan yasa ya nemi number Baban Yaseer yakira ringing daya yadaga anatse yace “Baba barka da warhaka” cikeda damuwa Baba yace “Aliyu Hawwa tayi accident gatanan a asibiti rai a hannun Allah” yanda zuciyan Baban Yaseer yabuga yakusan fitowa yace “wat?! Baba Hawwa tayi hatsari!”?