← Book details Fulanin Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 25

Sashe 21

Fulanin Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga ranar Ahmed yazama wani iri gashi nan dae, ga joda ga dad dinsu, dole Mahmud yadauko hafsa yaxo sa ita asibity, bakaramun tashin hankali tashiga ba yanda taga abbansu baya koda motsi ne " kusan wata uku ana fama dole aka dawo gida Ahmed yace lallae baza'a fita waje da shiba se maganin sa yakare na wata hudu, dole badan kowa ya soba ya hakura, abdallah ma tuni yadawo gida , hjy da amina ne ke kula dashi yanxu kuma sun daina sedai idan Ahmed ko abdallah ko Mahmud da yanxu yazo shine zai canza masa kayan su suke yimasa wanka sann kuma su wanke masa kashi da fitsari , joda ma itada hafsa agida suke wuni kullum saboda dad su suke ragema si abdallah ayki,

Hjy tashigo dakin tasame bakowa a hankali takalli dad, tayi yar dariya sann tace se yaushe zaka mutu ne " rayuwarka batada wani amfani aduniya oxygen dinda yake bakinsa tajawo zata cire se taji anbude ganbu, dasauri tajuya Ahmed yashigo aykuwa kyallen dake gefen kansa tajawo tana dafa masa goshinsa , Ahmed yace sannu da kokari hjy, hjy tace yauwa Ahmed Allah yabasa lfy ameen " dakin ta taje takira amina tace ke ayki zan saki akan mahaifinki, amina tace dad kuma dayake a kwance wani ayki za'a Mar

Hjy tace inaso kisaka pillow ki ida mun shi, ma'ana ki karasa gawar, dasauri amina tajuyo what? mamma anya zaki shiga aljanna kuwa? Wlh ko kiyashi bana iya kashe wa bare mutum kuma dad dina hava mama, hjy tace shikenan zancireki asahun yayana sann kisani babu ni banu ke " amina tafashe da kuka hava mama yazaki mun baki, ni nama fara zargin cewa kece kika hadda sa masa ciyon

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 1⃣0⃣5⃣
Hjy tace kwarai dagaske nice nan, amina tashiga girgiza mata kai tana kuka, hjy tabude wadrop tajanyo mata wata doguwar riga tabata tace irinta joda tasaka kisaka irinta se dare idan kin tabbatar da bata dakin sann kitabbatar wani yagan shigar ki kokuma fito warki adakin , umarni ne ba shawara ba, amina taci kuka kamar ranta zai fita daga gurin tafara nadamar kasancewa yar hjy

Dare yayi su hafsa sunyi sallar isha itada joda, joda tawuce dakin Gwaggo hafsa ma tayi dakinta dake gidan, amina dake labe tawuce harda hada jiki sukayi da hafsa, hafsa tace ke joda lfy wann saurin haka , amina dataki juyowa tadaga mata kai, sann tashige dakin,

tadade tana kuka sann tace kayi hakuri dad wlh ba laifi na bane hjy ce tasakani, tana kai nan tadauko pillow ta aza masa aykuwa yafara Shure2 har dae yadena motsi tana ganin haka tafita aguje, ba'a Fi minti uku ba Sega joda tashigo dakin, pillow din datagani Akansa yabata mamaki hannun ta takai zata dauke Sega hafsa tashigo , ido tazare sann tace joda mezan gani haka

Joda tace hafsa haka nasamesa wlh, hafsa tayo Gunsa dasauri ta dafa girjinsa taji baya motsi, dasauri tajanyo joda tana dukanta joda tashiga kwala ihu, macuciya azzalimi ki rasa dame zaki saka mana se wann " Ahmed yashigo dakin dasauri , dakyar yasamu ya kwace joda a hannun hafsa, sann ya wanketa da mari, bakida hankali ne zaki kasheta ne ma tayi miki, hafsa cikin muryar kuka tace Ahmed! Ta kashe mana dad da idona nasameta tana danne sa da pillow

Ahmed yace what yajuyo gun joda yana jijjigata joda tell me gaskiya ne abunda tace , joda kam kasa mgn tayi sema kukan datake yi, Ahmed yakwanketa da mari sann yayi ball da ita yaje gun dad dinsu yaduba shi, ajiyar zuciya yayi ganin akwai sauran rayuwa agunsa amma ba lallae bane ya tashi danko yayi nisa , Hjy da amina suka shigo dakin hjy tace lfy nake jin hayaniya, Ahmed yace bakomai, hafsa tace hjy joda joda zata kashe mana dad , Ahmed yace daga yau kar wanda yakara shigowa dakinsa gwaggo itace zata cigaba da zama dashi har satinsa uku su cika sa'annan muwuce Egypt dashi

Hjy tace gawar za'a zauna da ita, ? Ahmed yace bai mutuba daransa , hjy tace what? Ahmed kansa seda yajuyo yana kallonta sann ta basar tace Alhmdllh bakar aniyarki ta biki, ana haka Sega Mahmud da abdallah sun shigo aykuwa dasauri taje ta rungume abdallah tana son kagan joda koh dayanxu ta kashe dad dinku , abdallah yace me, Mahmud kamar ya? nan ta zayyane musu komai,

abdallah yakalli joda yace joda yaushe kika canza, Dan ya aura miki dansa bakyaso shine zakiyi kokarin kaisa lafira kin ban kunya ,Mahmud yabanka mata harara yace butulu munafuka, joda taje dasauri tarike masa kafa hava ya Mahmud kafi kowa sanin waye ni wlh ahaka nasamesa, hafsa ta turata dakarfi tace karki sake taba mun miji tinda ke bakisan muhimmancin auren dayake kanki ba ........

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 1⃣0⃣6⃣
joda tace karku mun irin wann judge din wlh tallahi bani bace, abdallah yace kedai kika sani, ana haka Sega wani yadanna bell din parlor hafsa taje ta karbo sako envelop ne kamar hotuna ne aciki akace tabawa Ahmed, bata duba ba tabawa Ahmed yace menene joda tace cewa akayi nabaka, Ahmed yabude abunda yagani yasaka shi shock dakyar yakai karshen hotunan noooo yafada acikin lion voice dinshi yacakumo wuyan joda idonsa jajir ya dinga buga kanta da bango dakyar Mahmud da abdallah suka kwache ta

Hotu nan suka dauko suna dubawa innalillahi wa'inna ilai'hir raji'un naji sun fada Mahmud yace I hate you joda I hate you, abdallah yace I hate you too, hafsa ma data gan hotunan tace hate you again fasiqa kawai, dakyar tadaga hannunta tajanyo daya daga cikin hotunan, hotonta ne tana sanye da towel hannunta ajikin wani kato bakyan gani, Ahmed yace me wann gardin yafini da shi miye amfanin......hawaye nagani suna kwarara a idon Ahmed abunda bantaba ganiba

Hafsa tace wlh wlh bazaki kara kwana agidann ba ke koma abakin gate dinn kika sake lekowa sena saka anmiki Dan banzan Duka, hafsa tace oya Ahmed kasaketa kuma uku, Ahmed ya girgiza kanshi am sorry hafsa amma babu saki acikin aurenmu, sedai kuma kisani yanuna joda banyarda da wann cikin ba kije kinemo ubansa, joda ko motsi batayi gata nan dae haka

hafsa tajata tafita da ita har gate tamata korarar Kare amina abun duniya ya isheta, tasan wann ma makircin uwarta da mansura ne " gwaggo bakaramun tashin hankali tashiga ba tayi kuka kamar me lokacin dataji lbrn hafsa tace gwaggo kina nan amatsayin uwarmu kanwar mahaifiyarmu baxamu kikiba Dan yarki tamana laifi gwaggo kam da bataga hotunan ba Sam baxata yarda ba,

Daga ranar rayuwar joda ta lalace, haka zatayi ta zuwa gidan hafsa kullum tin safe har marece amma baza'a barta shiga ba tayi sintirin zuwa gurin Mahmud shima ko kallonta bayayi khalthum ma ta guje ta, gwaggo tace bata son ganinta " amina ce kawai yarinyar datake jin sanyi agurin ta tana taimaka wa joda batareda sanin kowaba, dad yafara samun sauki saboda yanda gwaggo ke kula dashi har yafara bude bakinsa dakanshi , mansura tafito daga wanka Sega joda tafito itama rike da cup ta tsiyayo vita milk

mansura ta kwace ta zubar, sann tace baki isa kici abun dadi ina agidann ba ana haka Sega Ahmed yaxo, tsawa yadaka wa joda, ke Dan ubanki banga ya miki cewa idan nakara ganinki a parlor dinn sena karya kiba, joda tajuya cike da kwalla tashige dakinta tafada kan gado tana kuka, kwana take sallah yini take sallah tana kaiwa Allah kukanta akan wann ibtila'in daya sameta......

Muje zuwa 🎄
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 💕

🎄 FULANIN DAJI 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄
🎄 🎄
🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 1⃣0⃣7⃣
Kwanakin sunja , watanni sun tafi cikin joda yagirma wata takwas wanda yayi girma kamar yan hudu ne aciki dakyar take tashi, joda duk tafita hayyacinta, gwaggo kuwa itake cigaba da kula da dad wanda sukayi 2month Egypt baiji sauki ba dole suka hakura suka dawo gida , hjy kam tafita har kasa se sha'aninta take , amina kuwa kullum adakin take wuni sekuka take gwaggo zatayi ta lallashinta har tayi shiru

Khalthum nagani da abdallah sun fito super market sunyo siyayya, kai daganinsu kaga masoya, joda zaune a parlor tafito daure da zani se vest saboda duka rigunanta sunyi mata kadan, agwaluma take sha tana hawaye, Ahmed yayi sallama amma Sam bata jiba, ido yabita dasu duk damuwa datake ciki bata hanata yin kyau ba cikin ya karbeta sosae, wani abu yaji lokacin daya kae dubansa ga boobs dinta wanda suka kara girma da tsayi , kamshin turarensa taji hakan yabata tabbacin shine tana juyowa yayi sauri yakauda kansa , dakyar da cizon lips ta daga tana ta nishi daki ran wai wai

Gabansa taci sann tace zanje hospital anjima 2dyz danka baya motsi, mari yawanke ta dashi, kana yace so nawa zangaya miki cewa kidena dan ganta danki da jinina , to bara kiji tin wuri ki sake tunani kije kinemo ubansa Dan wlh baxan masa suna ba, joda tadaga kafada tace it's of to you, zamana agidann saboda nareni abunda ke cikina ne kasani bantaba son abunda ke cikinaba kasancewar sa jininka, saboda bana sonka, ina haife shi zan bar maka shi sann inyi tafi yata baxaku sake ganina ba

Zakiyi nemana ko da a mafarki ne saboda kubani sedai lokaci yakure muku, tana kai nan ta juya tawuce har tabude dakinta sekuma tajuyo, tace Ahmed! abunda bantaba jiba joda takira sunan Ahmed, wlh wlh jininka ne danka ne ko yarka, ban yiwa dad din hafsa komai, hannu tadaga sama tace ya rabbi kada ka karbi rayuwa ta baka nuna mun wanda yakulla mun wann sharrin ba, ya Allah kada ka karbi rayuwa ta baka nuna mun nadamar wadann bayi na kaba wadanda kasa ta rufe ma ido suka manta waye joda suka manta kyawawan halayenta suka manta dacewa bincike shine gaba before a yanke hukunci
Chapter 21 · 0% Book details