← Book details Fulanin Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 25

Sashe 10

Fulanin Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsa taji tausayin ta tazo tajanyota zuwa kujerun dasuke zaune khalthum kuwa mezatayi inba dariya, at kinga masoyinki koh? Joda tafashe da kuka se hafsa ke lallashinta, duk abunda ake visa idon Ahmed da Mahmud Wanda yagama kuluwa , mansura kuwa se murmushi take na mugunta, haka taron yakasance Ahmed yazuba dala kamar ruwa haka yake barin kudi agurin Mahmud ma ba baya ba,

Hafsa tace kuzo muyi wa amarya da ango liki, joda tace wah ay wlh dana zuba musu kudi na gwara na zubasu a shadda, khalthum tace kyaleta hafsa kishi take ,joda tace tupp Allah sauwake inyi kishin wancan mai mugun halin , hafsa tace nidai yayana bayada mugun hali kema Dan kinki kwantar da hankalinki ne " joda tace nace dai bazaniba sekun dawo dole suka kyaleta sukaje suna yimusu liki,

Wucewarsu keda wuya Sega wani yazo yaxauna baby tin dazu nake neman tayadda zan sameki mugaisa , joda tadago tace lfy? Yace lfyr ce dai wlh kawai kimun kuma ina sonki in bazaki damuba muje filin rawa, joda tace amma wlh kai bakada kunya nizaka cewa muje filin rawa namaka kama da mai rawa ne iye , Mahmud yaxo wucewa yagansu dasauri yadawo baya, yace kai malam lfy? Yaron yace lfy qlw bros dama naganta ina sone, Mahmud yace itakuma bata gayamaka cewa ansaka muna rana ba, joda tadago tana kallonshi yace to maxa kabar nan gurin wann matata ce, yaron yabashi hakuri sann yawuce

Mahmud yaja hannun ta yace zo muje gurin rawa joda tace a'a ya Mahmud ni ban iya rawa ba , Mahmud yace sekuma kinje dole, haka sukaje yasakata dole tayiwa amarya da ango liki, Ahmed se bin ta da harara yake mansura na mamakin yanda yarinyar tahadu amma Sam bata gaban Ahmed duk yan matan gurin babu wacca tafita yayan masu kudin gurin da kowa , dayake khalthum ce ta gyara ta, khalthum akwai duniya ci dason wanka

Mahmud yace kiyi rawa mana se in miki liki , joda tace kunya nakeji ya Mahmud bantaba rawa ba ni banma iya irin wann ba, Mahmud yace shikenan toki Dan taka, haka kuwa akayi yafara mata liki, abdallah na hango su nashi kishin ya motsa shima yaxo yana mata likin kudi, aykuwa se abun yazama kishi dollars, aykuwa mai kidi yakoma kansu yana xuba kirari joda kuwa duk ta tsargu

Hankalin kowa yadawo kansu, Ahmed yarungume hannuwa yana kallonsu khalthum da hafsa sukayi jugum suna kallo, sukuwa sunki daina mata liki duk da barawa take ba, hafsa taje gurin mai kidi tace yasaka musu kidin FULANI, aykuwa Sega joda tafara motsawa duk Wanda yake FULANI agurin seda yaje filin rawar saboda yanda suke Jin kidan ajikin su...........

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 7⃣7⃣
Joda tafara wani irin rawa yanda kidin ke tafiya haka rawar ta ke tafiya kowa yakoma kallonta hafsa takalli khalthum ashe ta iya rawa jita kamar macijiya, kowa yamatsa yabata guri Mahmud ya cigaba da liki hakama abdallah, gumi se karyemata yake amma taki bari shikuma mai kidi yakara da busar FULANI, nan joda tafara ajujuwa har takai gurin Ahmed anan tafada kanshi tareda rungumesa da hannu bibbiyu, hafsa tace yayi dae2 khalthum tace yo naga soyy,

sun dade ahaka sann Ahmed yadago fuskar ta yaga idonta arufe Jan ta yayi yanda take rungume ajikinsa har mota, abdallah ya dinga ja dabaya yana dana sanin abunda yayi, mansura tabiyosa dear ina zaka ay seka bari hafsa ta maidata gida, Ahmed yace noo kikoma ina xua, gudun yamata wulankanci cikin kawayenta yasaka takoma, Mahmud yaxo yace man......baikarasa ba Ahmed yasaka hannu agabanshi batareda yajuyo ba yace enough enough Mahmud,

yana kai nan yasa kai yawuce cikin motarshi ya ajiyeta yazagaya yatada motar se gida haka ya rungume ta tamkar jaririya, se dakinshi ya shimfideta kan gado sann yadauko mata ruwan sanyi yabata tasha tareda wani kyalle yagoge mata fuskarta, ar u ok? Naji yafada joda ta girgiza masa kai, sekuma tasamasa kuka, Ahmed kam shiru yayi yana kallonta can yace kinsan Allah Zane ki zanyi

Yanxun Dan bakida mutunci kikaje karti suka tasaki a tsakiya suna tabaki wann yatava boobs wann yataba hibs , kowa na kallonku, joda tace na shiga uku ni wlh bawanda yatabani acikinsu, Ahmed yace yimun shiru munafuka dama ay haka kikeso , ke baki San hukuncin aure ba koh " joda tace toni ay bana son auren ,Ahmed yadaka mata tsawa zanci ubanki wayake son auren daga an taimaka miki akayi, joda tace toni nagode da taimakon, Ahmed yace keee wlh zakici ubanki yanxu get out b4 nabata miki rai shegiya mai fuskar agwagwa ," nikuma asea nace ay fuskarku daya ehe 😏

Fita tayi takoma dakinsu, gwaggo tace au har kun dawo inasu khalthum da hafsa, joda tace basu dawoba, seni kadai, gwaggo tace ke kuma ana zaune qlw sekika yanke jiki kika dawo gida, joda tace toni nadawo ne ay yayan hafsa ne ya maidani gida, gwaggo tace tsakaninku baruwana, joda tafashe da kuka ni wlh an cuceni kawai baza'a bawa mutun Wanda yakeso ba mezanyi da wann Dan bakin rai, gwaggo tace kyaji dashi in ni nacuceki toki gayawa Allah inyaso seya saka miki, joda ta zunbure baki tayi cikin dakin

Tellphone tajanyo takira doctor bayan sun gaisa, yace toh ganinan xua nadai san abunda kike jira, joda tayi murmushi yauwa likita kagane, bara nayi sallah kafun kaxo , sallah tayi sann tasake wanka sabuwar atanpa tasaka ta cikin kayan bikin super ce tamata kyau sosae sann tasaka gyale kalar atanpar se takalmi flate, gwaggo sallah take saboda haka ta lallaba tawuce batareda taganta ba , tana kai gate yana fakawa da mota kawai tashige, suka tada hanya , wakar flavour yasaka mata mai taken vewrifull" joda najin dadin wakar sedan mamin take dikda bata iyaba , har suka kai wani gida mai kyau, yakalleta yanaga jikinki yafara bari zakiga queen of beauty " joda tace uhm..Muje dai , shi yabude gate din abunda yabawa joda mamaki kenan sann suka shiga

Karamun gida ne amma yahadu komai naciki sabo ne " binsa kawai take itakam bataga alamun wani mutum agidan ba, joda tace nikam bakowa ne agidan, yace bana son azarbabi fah muje dae, wani daki suka shiga se kamshin sababbin kaya yake , yace tazauna yakira mata matar tasa joda tazauna cike da kaguwa, ba'a Fi minti uku ba se gashi yadawo da drink yana sha yace dubo nan joda ya nuna mata mirror wakika gani, yarinyar nan tafiki kyau luk at pinky lips dinta bakinta kamar cokalin tea gashin ta har gadon baya komai nata enough ina kewar ganinta nanda shekara daya , joda tajuya tarufe idonta, da hannuwanta, likita yace hakika joda so yawuce afadesa da fatar baki ina sonki joda tin randa nafara ganin ki, joda kam kasa tsayuwa tayi aranta tace shikuma wann nasa style din daban yake..........

Muje zuwa 🎄
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 💕

🎄 FULANIN DAJI 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄
🎄 🎄
🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 7⃣7⃣
Haka suka dawo gida Zancen namata yawo akai, kowannensu da abunda yake sakawa aranshi, joda na tunanin makomarta shikuma yana tunanin karta ki karban soyyr shi, joda tace nikam likita se yaushe zanga fuskar ka? Dasauri yataka burki seda ta tsorata, yace no joda bayanxu ba lokaci baiyi ba , joda tace towae mekake boyewa ne acikin wann fuskar, yace bakomai joda mamaki ne kawai aciki dakuma tsoro,

Joda tace tsoro kuma kamar ya? Yace eh tsoro nasan idan kika gan fuskar nan komai ma zai iya faruwa idan ki kaga hallitar da Allah yamun wann dalilin ne yasaka nake saka face mark nafi son kiso zuciya ta sama da fuskar nan tawa ganinta bayada wani amfani Watakila ma idan kika ganta bazaki sake yarda ko hanya ta hada mu ba, joda , kam dole ta hakura ,

yana ajiyeta Sega su hafsa dasauri joda tashige gida batareda sun ganta ba, tayi shiru kamar mai bacci, koda su kazo tana bacci khalthum tasha dariya sann suka fita, wanka tayi sann tasake wasu kaya , tana cikin shiri segasu sundawo , hafsa tace muje gurin kae amarya, joda tace wah zaije kai amarya din. hafsa tace tome ne aciki Dan kinje, joda tace Allah sauwake mun naje kaima wani mugun amarya toni waema miye ruwana dasu nifa danke nake xua bikin nan hafsa

Hafsa tace ollrt yanxun ma kije danni okey, joda tace wlh ba inda zanje kubace mun dagani, khalthum tace muje hafsa kar mu rasa motar hawa mudae baza'a bamu lbr ba, joda tace safe journey. khalthum tace oho dai kedai kishi ne kurum bazaki iya ganin mijinki dawa ta ba amatsayin matarshi, joda taadauko filo ta jefa mata sann tafashe da kuka dasauri suka bar dakin

Gwaggo tace to lfy sarkin kuka, joda tace ni wlh ki musu mgn sudena tsokanata wae daga nace bana xua shine wae ina kishin yayan hafsa ne " gwaggo tace yo dama meke cinki inba kishi ba, joda takara fashewa da kuka tana bubbuga kafa , ko Dan kwali bata saka ba tafito waje tayi hanyar garden tana kuka, bayan wani window ta tsaya tana kuka tana zance ita kadai, kamshin tirare taji dasauri tadago taga waye fararen kafafun sa ta zubawa ido sann tayi sama light din wurin yaki kae ga fuskarsa amma dae tasan abdallah ne sbd shiyake saka irin wann kayan

Dagudu taje tayi hugging dinshi tana kuka, ya abdallah shikenan kahakura dani, Dan Allah mugu du daga gidann, bana son yayan hafsa natsanesa kamar yanda yatsaneni, sekuma tasaka kuka, tareda kara kankame shi, shiru taji yayi a hankali ta sakesa, tana son ganin wani yanayi yake ciki , amma fuskar shi bama ita yake kallo ba kujera tajawo tahau yanda tsawonsu zaizo daya , na shiga uku tafada 🙆🏻 tareda zare ido " Ahmed yakura mata idonsa masu ban tsoro fuskar nan ba annuri acikinta , yasaceki kugudu yafada acikin lion voice dinshi? Wato ke yar iska tantiriya koh har kinsan saurayi ya daukeki kugudu domin kuji dadin aykata masha'a
Chapter 10 · 0% Book details