← Book details Fulanin Daji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 25

Sashe 17

Fulanin Daji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gamawa yakirata joda zo naga jikinki, Dan kwalinta yacire yana taba gashinta yaga ma kamar yafi da tsawo sann yafi jikinta da kallo bawata matsala, yace meyasa baki gayawa kowa ba, joda tace sunce zasu ballani idan nagaya wa wani sekuma tafashe da kuka, Ahmed yarungume ta yana shafa bayanta it's ok kinji..............

Muje zuwa 🎄
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 💕

🎄 FULANIN DAJI 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄
🎄 🎄
🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 9⃣5⃣
Ahmed yaje yaga dad yamasa magana kan cewa ran Friday joda zata tare gidanta baya bukatar komai shi zaizo yadauki abunshi da dare, dad yayi matukar murna dajin hakan, shima yaje yasamu gwaggo yamata bayani, itama din murna tayi sosae daga ranar aka shiga gyaran joda ana tirka mata kayan fruits, hjybinta kuwa gyaran jiki take mata kafun kwana shidan suzo sekunga yanda joda tadawo abun sewanda yagani skin dinta kamar zai fashe idan kataba

Joda tasamu khalthum tayi mata bayani, khalthum tace aykuwa yafi ma seki kara wanasa , khalthum a ranta tace lallae joda bakida wayo kafun 5 month din yakoya miki yanda zaki soshi , ni hakan ma yayi mun ina sonki da, Ahmed kodan ki gyara masa zama kamar yanda kika gyarawa abdallah nasa

Angama hada komai tsaf dad yakira joda yayi mata nasiha kamar haka , joda ina son kirekemun dana amana kamar yanda nabasa umarnin yarike ki amana nagayama sa tabbas idan yacuceki tokuwa ban yafe masa ba , inaso kiyi amfani da iliminki da tarbiyar dakika samu kigyaramun wasu halaye na Ahmed, tinda kika gyara abdallah Ahmed baxai miki wuya ba , ki daure kiyi ibadar aure kisamu aljanna iyayenki ma zasu samu

Banda fitsara da shashanci dukda nasan wann bahalin ki bane idan kika iya Ahmed bayada wuyar zama, ki kama kanki daga matarsa karki shiga lamuranta inso samu ma kada ki hada hanya da ita seta kama dole , allah yabaku zaman lfy da zuri'a dayyaba ameen " dakyar aka banbare joda daga jikin gwaggo, ita kuka gwaggo hawaye, gwaggo takasa mata wata nasiha kawai tace mata Allah yabaku zaman lfy yakauda shedan azamanku ameen

Tin da Ahmed yatada mota takara wani ihu kuka take kamar me, Ahmed baice da ita komai ba, har suka kai gidan yafito itakuma taki fitowa zagayowa yayi , yabude ganbu yajawo hannunta sukayi cikin gidan , kwance take kan kafadarsa tana kuka har suka kai dakinta yabude mata " suka shiga yanuna mata komai hadda lefen ta agurin sak irin na mansura babu banbanci , dakinta kam ko makiyin Allah yagani yasan anhadu se kamshi yake joda tafada kan gado tacigava da kukanta

Ahmed yace mata shikam seda safe, aykuwa ta taso dasauri ni kadai zan zauna anan ni wlh tsoro nakeji, Ahmed yace to sokike in kwana adakinki koya? Joda tace eh kokuma nabika adakinka, Ahmed yace yo na banu muje din . dakinshi sukaje takwanta shi kam toilet yaje yayi wanka yasauya kaya sann yasha coffee. se yakwanta, joda na karshe Ahmed na farkon gado haka sukayi baccin su , anfara kiran asuba Ahmed ya farka koda yaduba joda tadawo ajikinsa ta lafe masa kamar mage aransa yace wann yarinyar kodai mage ce iyakaci kenan wann shegen son jikin nata

A hankali yasaketa ajikinsa yaje yayi wanka yayi brush yawuce masallaci yabarta tana bacci, koda yadawo yasameta kan sallaya tana karatun al qur'ani, tana juyowa tace ina kwana yayan hafsa, Ahmed yace lfy lau kn tashi lfy joda tace lau , bayan ta ida karatu tace yayan hafsa ina ne kitchen in hada mana breakfast, Ahmed yace no an yafe miki kibari se zuwa gaba kadan............

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 9⃣6⃣
Su hafsa andawo hutu, taji dadin wann lbrn wai joda ana gidan Ahmed, gun khalthum taje suka yo inda joda, Sallama sukayi mansura na falo tana kallo, kallon banxa tamusu sann ta cigaba da kallonta, hafsa tace anty mansura ina wuni, mansura tace yana gidanku daban wuniba da zaki ganni anan, khalthum taja hannun hafsa sukayi sama,

mansura tace gidan ubanwa zakuje khalthum tace gidan uban mai tambaya, mansura tazaburo dakarfi, hafsa tace Dan Allah anty kiyi hakuri, khalthum bata sauraretaba tayi ciki, mansura takoma dakinta tacigava da hutawarta ba sallah bare salati Ihu joda tadauka ganin su hafsa duk tarude tama rasa abunda zatayi aykuwa tashiga jibgo musu abunci pizza da kaji se lemuka,

hafsa tace iye sukike ci ne " joda tace eh wai baya bari inyi girki ni bantaba sauka kasa ba tin randa naxo gidann, khalthum tace kenan baku taba haduwa da fitsararriyar amaryarki ba , joda tace aifah ina side dina ina Jin motsinta some time, hafsa tace ay haka yafi, joda tace nifa inaga bata san da zuwa na gidann ba yanda nakejin tana waya da karti datasan ina nan dole tarage wani abu " hafsa tace uhm..allah ya kyauta

Fira sukasha sosai se kusan mgrb sann suka fito joda tahada musu kayan make up na cikin lefen ta. hafsa tace a'a baxamu karba ba, joda tabata fuska to mezanyi dasu sunmin yawa wlh, dole suka karba badan sun soba, har gate takaisu sann tadawo anan taci karo da mansura tarava ta gefen ta tawuce mansura tadaka

mata tsawa ke ina xua, joda tabuga mata tsaki sann tayi wuce wata sama, mansura tabita dasauri wai ina zakije nace basu hafsa sun wuce ba ke kuma pa meya dawo dake joda tace eh sun wuce zasu gida nikuma nadawo saga rakiyarsu na shigo gidan mijina kuma habibiy na, hannu tadaga zata mareta sega Ahmed yace ke ke lfy?

Mansura tace wann marar kunyar yarinyar mana wai gidan mijinta, Ahmed yace eh karya tayi ne nan ba gidan mijinta neba, mansura tace wai bala'i billahil'azim baxan zauna da ita ba, Ahmed yatada kafada fine kofar gidan abude take dama ni kawo ki ne ? Joda tace kuma kadaya mata tabini sau dakafa Dan nice uwar gida nice babba bazan cen shekaru

Ahmed yaje famata key din mota dake nake magana, joda ta bare baki wlh ban yafe ba, Ahmed yabita dasauri ta rufe ganbun dakin dakarfi, mansura tajuya afusace tahada kayan ta tafito taja mota tabar gidan, Ahmed na kallon ta yamata banxa gidan su taje tazayyane wa uwarta komai, innasarsu tace to miye aciki tinda bakulata yakeba

na tabbatar ubansa ne yace dole yamaida ta gidanshi kedai kawai kikoma ki cigaba da ya go mana shi, dahaka aka batar mata da kishin ta. zuwa 11:30 tadawo gidan, shiryawa tayi cikin kayan bacci taje dakin Ahmed ko kallonta baiyiba taduka tabasa hakuri , Ahmed yace shikenan yawuce daga nan suka lula wata duniyar

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B Aleeyu 💕 page 9⃣7⃣
Tin randa joda tazo mansura take samun biyan bukatar ta agurin Ahmed har se ta ki wani lokacin, dalili kuwa joda ce keruda shi amma tsabar jinkai da karta renasa yasaka yake neman mansura dukda tana gamsar dashi 70% amma ko kadan ba itaba sha'awar taba , mansura kuwa ansamu yanda ake so har anfara wani epixy epixy ,

joda kuwa al amarinta take baruwanta da kowa agidan barinma yanda taga Ahmed ya share ta. itakuma tafita har kanshi ko mrng tadena yimasa, se hadu tarava masa hanya amma bawanda zero yiwa wani mgn Kullum safiya seta zana da biro kwana Kin da tayi agidan , yau Watanta biyu cif,

joda takara cika yanda take cin kayan dadi gakuma hutu aykin komai batayi se gyaran dakinta, yau tashirya cikin wata atampa brown tayi kyau, tanada dankwalin ta simple taje dakin Ahmed tareda mansura tasamesu suna iskanci inji joda aranta tace tanbadaddu kawai se ayita ta shafe2 iskanci 😂 , baya tabasu sann tace ina son zuwa gida inga gwaggo na, Ahmed yamata banza, mansura tace honey ana mgn fah kayi shiru, Ahmed yace ni Dan iska ne dazan amsa mata mgn tabani baya

Joda tace nima kuma ba yar iska ceba dazan kalleku kuna tanbadodi , Ahmed yaxubura mansura tarikesa yi hakuri cweet heart, Ahmed yace sekin dawo out kuma daga dakina joda tace koma baka ceba , ba tsayawa zanyi ba kallon iskanci, allah yashirya wanda yabata tana kai nan tawuce, Ahmed yayi tsaki sena karya wann yarinyar watarana

Zuwa aza har tagama shirinta tsab ta rufe dakinta tadauko kasa, mansura tace har kin fito, kigaidasu Allah kiyaye joda ta yatsina fuska ameen idan dagaske kike, Ahmed yace kewai bakida hankali koh se kiyi ta yiwa manya fitsara, joda tamasa kallon banxa tawuce abunta, mansura amma dae honey baida ce kabar ta taje gida ita kadai ba zuwan fari kuma ni banga tayi wani tsara ba ba hannu rabbana zataje, Ahmed yace hakane ina zuwa, ciki yakoma yasauya kayan shi sann yabita dae2 gate yayi wa maigadi hannu alamar kar yabude gate.

Ahmed yasameta yace mata kee fito muje amotana , joda tace why bayan gatawa, Ahmed yace to haka nakeso, joda tace nikuma bahaka nakeso ba , Ahmed yace zan ballaki fah ki fito kafun na saba miki Joda tace ni banida hannuwan tuka mota ne se anjani, Ahmed yace shikenan karki fito wlh ba inda zakije, joda tace so what? Fitowa tayi a motar tarufe ganbun da karfi tabuga masa dogon tsaki sann tawuce ciki, Ahmed yabita da kallo

Hafsa tafito zata inda gwaggo ana tahadu da Mahmud, yana waya da amina dae2 kunnenta taji yace I love you amina more than you could think " wani kololo taji yana taso mata a zuciya zafi zuciyar keyi aykuwa tadafe ta anan tafadi timm, Mahmud yajuyo yayi kadi da wayar yace hafsa koda yadago ta jini abakinta dakyar ta iya furta ya Mahmud kawai seta yi baya , wayarshi yaciro yakira Ahmed, Ahmed baijira yagama bayani ba ya tsinke wayar, motarshi yafiga yazo gidan Allah ne kaday yakaishi lfy
Chapter 17 · 0% Book details