← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 26

Sashe 9

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aman ai kin san Aban ya san muna tare da ke ko? ABDUL KADRE ya fada yana faman tsayar da ita

Ju
Uyowa ta yi ta hade rai ta ce" ka ga malan ka yi hakuri kawai, ai a gabanka aka kwatanta tafiyarmu ba mai yiwuwa bace, koda ban san takamaiman gaskiyar abinda ya faru da yayar Mamana ba hakan bai zama dole na yarda da fadar mutane ba, a kulun kamar yanda mamana ke adu.ar Allah ya bayana mata da yayarta nima haka nake yi ko na samu nima Mama ta biyu mai sunana, dan haka ka yi hakuri

Saima ta daina yunkurin karasawa gidan kakanin nata ta juya kawai ta tsayar da dan adaidaita ta yi masa kwatancen gidansu unguwar Hotoro

A bakin layi ya ajiyeta ta sauka ta bashi kudinsa ta shiga takawa cikin nutsuwa dan karasawa gida

Ja tayi ta tsaya tana kallon kofar gidan amaryar unguwarsu wace ake ta fadin kirkinta, yama ce dai dare bai yi ba sosai aman ba mutane sosai dan wasun basu sauko daga kasuwa ba yawanci kuma yara du ana makarantar islamiya sai daidaiku

A hankali ta shiga konkwasa kofar

Mai gadi ya leko, gannin yar budurwa ya bude yana tambayarta ko wa take nema?
Marwa ta ce" wajen Hajiya aka aiko ni

Mai gadi na jin haka ya bata waje yayi mata nuni da inda zata nufa dan gannin hajiyar

*Aisha* na kokarin jera kayan abinci a saman table , gefenta *JAMAIL* ne yana amsa waya sannan yana binta da kalo du inda ta yi, suka ji ana konkwasa dakin

A tare suka kali juna dan ana iya hangen mai konkwasawar ita dai ce bata iya gannin mutanen cikin

Kai Jamail ya dafe ya ce" ni kam na rasa cikin ji da ke wa yafi wani farin jinnin jajibar mutane, tunda safe aikin da ake kennan a gidan nan , sai shigowa yan anguwa suke, gaskiya zan dauke ki mu yi tafiyarmu mu huta ko na canza anguwa

Murmushi ta saki tana gyara hijabinta ta nufi kofar dan budewa domin haka suke idan namiji ne shi ke tafiya ya bude idan kuwa macece komai kankartarta ita ke budewa , ta ce" kai Hubby ka sanfa yanda amarya keda farin jinni, ai da an kwana biyu zaka ga an rage daga baya ma a daina shigowar sai kuma idan ni ina da zumunci sai na kara tarawa kaina mutanen,

Binta yayi da kalo har ta bude tana amsa gaisuwar Marwa

Jamail dake zaune yayi gagawar dago da kansa dan haka kawai ya tsinci wata faduwar gaba daidai lokacin Aisha ta baiwa Marwa waje tana fadin" *aa ki shigo mana ai ba komai*............

Shin masu karatu suna biye da ni kuwa? Wa ya gane wacece maman Marwa?
[2/1, 2:30 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*33*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Ya ce" mai kike son ji? Kina son sannin idan har na damu da wulakanta aurenki da kike yi ne ko kina son sannin idan saurayinki da kuka gama watsewa ya cika namiji? Kina so a yaba salon tsagerancin iskancinku ne na tsalake titi da yawon banza a dawo cikin gida, gidana na aure da igiyar aurena a kanki ya biyo ki a gaban idannuwan masu aiki da direbobi ya kuma kama jikinki a yannayin talar masa da kika yi? Ko kina so ki tabatar min da tsohon dan iskanki cikeken fitsararen namiji ne? Yakan mantar da ke duniyar sa kike idan ya.....

Ya tsayar da maganar ya bi jikinta da kalo, ya sasauta rikon wuyan nata karshema ya cika mata wuyan wanda yayi jajajir har fuskarta suka hade suka dan haye , aman bai matsa daga kurace mata wajen da yayi ba, idannuwanta a lumshe tana yannayin tashin hankali aman wani irin kyau da haske da take yi masa a idannuwansa sannan numfashinta idan ta fitar shi yake shaka itama tana shakan nasa mai cike da kanshin cingam da ya dan tauna a office
Yatsarsa mai bima baba ya dora a gefen kuncinta na dama, a hankali ya shafo har wajen habarta, lebenta ya tsurawa ido bugun zuciyarsa na tsannanta haushinta da soyayarta suna daukaka a zuciyarsa, a fili sannan kasa kasa ya furta" *Koda zamana da ke bai yi nisa ba, na yi maki alkawarin zuciyarki bata da masaukin kowa sai nawa, sannan daga wannan rana koda zaki mutu da bukatar wani namijin koda ni ne, domin baki kai girman ko darajar da zan yi taraya da kazamin jikinkin nan ba, kuma kinyi bankwana da wani sai dai idan bana numfashi a doron kasa jikinki wani dan iskan ya gama taba shi, ke duniyata ce wace nake da iko da ita sannan zan horata na kin yin shuka sma cikinta, ni masaukinki ne wanda du bukatarki ta duniya zaki iya zube min aman banda ta dalilin da ya saka ba zan rabe ki ba, da a ce zan iya kalon jikinki da zamu gwada ni da mazan da kuka gama watsewarku wa ya fi iya buga kwallon, ki tafi ki yi kukan rabuwa da duniyar...........wife!*!

Yana gama fada ya saketa ya juya cike da mugun sauri tamkar ya tashi sama ya fice ya tarar da Anwar dake tsaye gefensa Lukman ne yayi tsuru du ya gama sarewa

Yana karasowa ido ya zubawa Lukman, tunani ne birjik a cikin ransa fadi yake yanzu wannan ya gama sannin matata, yanzu wannan ya je wajen da ban je ba? Yanzu wannan ya kara gudun zuciyar matata?

Anwar ya dan matso ya ce" yaya, ka yi hakuri ka sanyaya zuciyarka a yanda yake fada baima tabata tana da aure ba sai yanzu kuma wajen Aba ya zo wanda suka yi maganar zai zo su yi wata magana mai mahinmanci , yana neman afuwa ba zai kuma gigin aikata hakan ba

Alaidine ya dago ya watsawa Anwar kalon bayan ya gama cutata? Kai ya kada ya ce" ban gamsu ba, ka je da shi zan shigo a kowani lokaci

Yana gama fada ya juya dan ya koma gidan

Cikin gidan Jamail da Aisha

Zaune suke cike da soyayar juna da dumbin kulawa da juna duda a daren farko bai taba ta ba aman a darenta na biyu a gidansa a ranar Allah yayi abinsa, wanda hakan ya kara wani dankon kauna da shakuwa tsakaninsu duda irin wahalar da ta sha a hannunsa, domin ta jigata iya jigata sannan ta ji tsoronsa fiye da tunaninta, tana gannin girmansa fiye da dala da gauron dutse🤣,

A unguwar hotoro gidansu yake, tankamemen gidan da Alaidine ya gina masu, gida mai amsa sunnan gida domin ya hadu ya gama hadewa

A makotansu gidan wata datijuwa ce, wace zata kai shekaru arba.in da dan dori a duniya, yarenta biyu kawai a duniya da *MARWA* da Aliyu

Sosai Marwar ta zama budurwa matashiya, ta dauko kyan gidan mahaifiyarta , yarinyar dai masha Allah ga kirki , sam bata da girman kai ga son amare a wajen Marwa
Hakan ya saka tunda aka kawo Aisha anguwar take zumudi tana faman neman mamanta ta barta ta je ta gaida sabuwar amarya aman fir ta hana tana fadan ita ta rasa gane kan shirme irin na Marwar haka kawai daga an kawo amarya sai ta nace ita sai ta je? Duda al.adar hausawa yin hakan ba wani abin bane domin idan an kawo amarya akan shiga wasu dan zumuncin ne qasun kuwa dan tsegumi ne, aman maman Marwa ta nace kan ba inda zata je
(Wacece maman marwa?)

Alaidine, tunda ya shigo falo ya zaune Mom na zaune da Boy a gefenta yana ta fama da ice cream yana kallon tom and jerry a tv

Mom cike take da shi, domin du rabin abinda ya faru tana sane a kan idannuwanta da ta ji wasu magangannun ne ta bar wajen, gashi yanzu ya kai minti ashirin zaune bai ce da ita komai ba bai shiga sabgar kowa ba

Wasa wasa yama ta yi, magariba ta shigo, yannayin zamansa tun na farko shi ne, hannayensa bibiyu a dafe da kansa, Mom ta fito a kicin idannuwanta suka sauka a samansa nan take gabanta ya fadi, kar dai yaron nan bashi da lafiya ne?

A hankali ta karaso wajensa ta dora hannunta ta ce" Alaidine, lafiyarka kuwa?

Jikinsa zafi sosai haka dukan yannayin jikinsa ya saki a hankali ya dago idannuwansa da suka yi jajir ya sauke a fuskar mamansa,

Abinka da Da da uwa, zuciyarta ta ji ta kara karyewa, tana hango fasarar da dan nata ya kasa amincewa, haka wani murna ya darsun mata a ranta na idanfa ya yarda da haka may be hanyar saukowarsa kasa kennan

Sosai yake jin nauyin zuciyarsa, a hankali ya dora kansa a hannun mahaifiyarsa murya kasa kasa ya ce" Momna

Mom ta ce" mai ke damunka son?

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" ba komai Mom,

Murmushi ta yi , shi kam zurfin cikinsa ba zai barshi ba, Mom ta ce" da kamar zazabi a jikinka, ka tashi ka tafi gidanka matarka ta kula da kai son,

Ajiyar zuciya ya saki ya ce" Mom, zan tura direba idan bata da damuwa ya daukota, ina son na dan huta a nan ina son zama kusa da ke Mom

Murmushi ta saki ta ce" son, yarinyar nan ina son taci gaba da karatunta kar a tauye ta, kafin Abanku ya yanke ranar tarewar tata itama ko?

Shiru yayi wannan karon bai ce komai ba, bashi da niyar tankawa dan bazai yiwu Wujdane ta koma makaranta a haka ba, ba zai yiwu ya bari ta koma makaranta ba sai dai ya dauki malamai su rinka koya mata daga inda ta tsaya,

Jin yayi shiru ta ce" ka mike ka haura sama ka yi alwallah ka yi sallah kafin lokacin cin abinci yayi, sai docter ya zo ya baka magani
Chapter 9 · 0% Book details