← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 26

Sashe 18

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wujdane ta yatsina bakinta wai itace ma mai laifi, dan kawai ta ce ta yafe, ta sasauta muryarta ta ce" eyah ba haka nake nufi ba, na ga ai ta fadi gaskiya ne sanin gaskiyar ta fada ya saka na goya mata baya harma na furta na yafe, ai dan karna takuraka ne na jima da sannin ba abinda zaka neman ko ba wannan wace ta shigo a baya da wace aka tarar ai ba daya bane, rikon mace biyu ma ai sai a hankali,
Ni nace na yafe ba da nufin cin fuska ko wani abin ba, na bar mata kwanakin da nawa da natan ta hade

Tunda ta furta kalmar Alawiya gaskiya ta fada na maganat ita ba budurwa bace ya daina fahimtar yarenta, hankalinsa ya gama tashi, shi kam ya jima da sakawa ransa hakan aman a yanzu da ta furta masan sai yaji du duniya bashi da wani farin ciki,
Du hasken fuskar Wujdane sai ta dawo masa bakikirin a idannuwansa ya ji lumfashinsa na garwaya da tsananin bacin rai da muradin sannin wanda ta baiwa kanta har take ikirarin hakan ma kunyar Allah ba tsoronsa

Taku biyu yayi ya damki wuyanta da hijabin, hakan ya saka tawul din faduwa daga ita sai hijabinta a jikinta ya jata har jikin bangon dakin , muryarsa ta canja dan masifa ya ce" WuWujdane, uban wa kika yarda ya keta maki hadi har kike maimaita min? Ki fada min wani dan akuyan ne ya zo maki har kike maimaita cewar kin yafe? Wujdane danme kika yi min haka? Danme kika zabi na ringa kwana ido biyu ina zubar da hawaye da girmana? Wujdane fahimtar da kika yi inai maki matsanancin so bai isheki aya ba da zaki kiyaye furtan wani ya taba zuwa wajen da aka halito min? Bakya tausayina ne ke? Wujdane na zo da niyar just nayi kissing dinki kika zile min dan me? Wanda kika yi hakan da shi shine kika fi so ko ya fini zama namiji ne ? Ko Wujdane sai an biya ki ake taba jikinki ne ban sani ba?

Da hannu daya ya riketa aman ta kasa kwatar kanta, banda kakari da take yi tana jujuya idannuwanta sai wani hawaye da ya ziraro mata na wahala
A kasan makoshinta take furta "aa aa aa (Wujdane an ji shaka)

Jikinsa ne ya ji ya yi masa wani nauyi, hakan ya sa ya cikata ya tafi luuu ya kife nan kusan bed dinta ya dora hannunsa biyu a kansa ya rike sosai idannuwansa a rintse

Wujdane da ta dawo hayacinta ta nufo shi da sauri ta dago kansa ta dora a jikinta tana rizgar kukan da ta rasa dalilin yinsa,.
........a hankali take furta" ka tuna da hadisi wanda yake yi mana nunin zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne,
Karka manta koyarwar adininka wato zurfafa tunani da kuma daukaka fushi ko kiyaya,
Alaidine, bani da bakin da zan iya furta maka wata kalmar da zaka yarda da ni, aman ina so ko gobe zaka yi furucinka cikin bacin rai ka tuna cewar nima mutun ce, musulma ce, ina da gatana, sannan du talaucinmu kudi ko wani abin ba zai saka na je na baiwa wani kaina ba na cire maka kadara, Alaidine karka yanken hukunci ba tare da ka san wacece ni ba, har yanzu sunana da gudanmu da yanda wasu mutanen ke fasara ni ka sani, ka yi hakuri karka sakawa kanka ciwon kai sannan ka tayar da ciwon da ya jima bai tashi ba, ka yi hakuri koda baka son na zauna a gefenka ne a gidanka ne sai na kara gaba da ya kasance ni mace ta biyu na nayi imanin *nafi ko wace mace sonka* a duniya zanyi sanadin shigarka a kunci ko da yaushe, ka yi hakuri ka sanyaya zuciyarka Alaidine, a yau yau a yanzu zan bar maka gidanka sannan zan je na sanarwa Aba nice nan na nemi hakan ba laifinka bane Alaidine domin ka sani shi mutun idan ana sonsa farin cikinsa ake nema masa, du sauran su biyo baya ne

Du abinda take fada Alaidine na sauraronta, har lokacin da ta shiga yinkurin tashi tana mai tabatar masa zata yi nisa da shi

Da sauri ya mayar da ita zaunen, ya kankame cinyoyinta ya cusa kansa a hijabinta, ya kamo hannunta na hagu ya dora saitin zuciyarsa,
Murya a shake ya ce" kina jin yanda take buga min, na jima ban ji emotion din da yake mitsa min ita ba, kina jin kuwa yanda take duka, kin gama zagayeta
Ki zauna da ni, ki yi hakuri ki kula da ni My Wujdane
Sai.kawai hawaye ya shiga bin kuncinsa wani na bin wani

A haka ta janye kafafuwanta ta silale kusansa ya kankameta a jikinsa suna sakin ajiyar zuciya ( Alaidine bai dai daina yarda cewar Wujdane a rufe take )

Wannan kennan

Yau kwannan Wujdane hudu a gidan Alaidine,
Shakuwarsu ta yanzu ta zarce ta baya nesa ba kusa ba
Du irin sa idon Alawiya ta dan daga dan ita ke gannin abinda ranta zai bace domin ko a falo baba Alaidine kan jawo Wujdane a doguwar kujera idan yana konce ta hau kusansa sosai ta dora kanta a kirjinsa yana shakar kanshin turarenta yana dan shafa hanayenta da suke tamkar fatar mage wani irin santsi da taushi,
Hakan na saka su su duka a wani mugun yannayi wanda nan da nan idannuwansa zasu canza launi du yannayin jikinsa ya tona shi ta hanyar nuna bukatunsa, itama takan fara mika wace ta kasa gane ko ta mecece, jikinta ya mutun mata, ta fara hama bayan ba baci taje ji ba ba kuma yinwa ba, aman ko kiss a baki bai taba zuwa nema ba dan yana cike da fargaba, yana gannin su duka sun fara alamar bukatuwa yakan yi dabarar ko daga waya ko ya fice da nufin yana zuwa har sai ya dan fara nutsuwa kafin ya waiwayeta,

Yau ta kama lahadi, Wujdane ta gama kimtsa kayanta da ta wanke abinta da hanunta bata saka a mashine ba, ta daura tawul ta yi wankanta ta fito ta yi salar azahar ,

Ta mike ta cire hijabin ta konta da yar doguwar rigarta ta baci ruwan pink tana tunanin ko Alaidine ya dawo daga fitar da yayi wajen gaisuwar rasuwa da aka yi a anguwar

Baci ne ya dan fara daukanta wanda tayi juyi sai jinta ta yi a jikin mutun, ta bude idannuwanta da sauri sai ta ga Alaidine ne ya konta a gefenta

Shigar jikinta ta dan bi da kalo, ta yi kananta sosai domin gaba daya cinyoyinta a waje suke aman sai ta ja bargo cikin dabara a tunaninta bai ankara da ita ba ta dan rufe har daidai kugunta

A hankali ta furta har ka dawo???
Alaidine ya gyada mata kai kafin ya ce" har na yi wanka, i miss u

Ta yi murmushi, wai gata ga shi yana fadin yayi missing dinta,
Jin ya jawota kirjinsa ne ya saka ta fahimci rungumar ce ake bukata dan haka sai ta saki jikinta a kirjinsa dan ta san ba abinda zai yi mata

Alaidine dake da dan gajeran wando yayi saurin rintse idannuwansa jin yanda ake dan harba masa anai masa :::::dil.....dil....dil😳,

Ya dan shafa bayan Wujdane sai ya ji har daidai inda pant dinta ya tsaya domin rigar nan ce mai shefen santsi wace ido na iya gannin abinda ta boye hakama hannu na iya ji idan ya laluba

Da sauri ya maido hannun nasa wajen gashin kanta yana dan shafawa yana sinsinawa, yana matukar mamakin yanda a koda yaushe ya rabo jikin Wujdane sai ya ji tamkar ya suma da bukatuwa ko dan tana sabuwa a wajensa ne ko mai
Igiyar yake ji ta taurara, bakinta na ambaliyar amai mai haske wanda yake kara tabatar da lafiyarta da bukatar aikata aiki

Lumfashinsa ya fara fitar sauri, Wujdane dake konce daidai zuciyarsa ta dago da sauri tana kalonsa ta ce" Yaya baka da lafiya ne? Sometimes sai na ji bugun zuciyarka ya tsananta bayan da farko ba haka kake ba

Idannuwansa ya rintse da wata kunya da ta kama shi, somin dai du yarinyar da ta san namiji karshen sani zata fahimci halin da yake ciki aman sai Wujdane ta ringa raina masa wayo ta hanyar yi masa tambayoyi kamar wace ba abinda ta sani

Mayar da ita yayi kirjinsa ya rungume , dan ya kasa furta mata ba komai din ma

A hankali jikinsa ya fara daukan zafi, wanda ita dake konce a samansa ta fara jin hakan,

Hannunta ta saka a cikinsa a hankali ta daga rigar wajen cibiyarsa ta dora hannunta da niyar yin sama da hannun nata dan ta ji ko zazabi ne ke shirin rufe shi wanda hakan ya saka shi dan zabura bai san lokacin da a fili ya furta " *Wayo Alahna* ba

Da sauri ta mike zaune ta dan ja bargon tana kalonsa da tsoron kar aje bashi da lafiyar ne? Ta furta" baka da lafiya ne yaya Alaidine?

Bata kai da karasa tambayarta ba, ta ji gadan gadan tamkar kura ya wawuri bakinta yayi masa riko tamkar marayan zaki ya shiga tsotsa tamkar za.a kwace masa

Yanda jikinsa ke rawa, hanayensa na kokarin cire mata rigarta lumfashinsa na sauka a hancinta

Da sauri ta saka hannayenta biyu cikin mugun tsoro ta ririke rigarta da yake kokarin cirewa, gashi bakinta a cikin nasa ta kasa fitar ds kalamanta, hankalinta ya kai kololuwar tashi tsoro ya bayana a act dinta, bugun zuciyarta ya tsananta da tsananin tsoronsa haka idannuwanta ke yawo suna kokarin sai sun shiga nasa ko zai farka ya gane da yake kokarin aikata hakan .

...........ni kuwa nace wa ya gaya maka Alaidine , kai har ka isa ka kunacewa mace guri haka du muninta koda ba komanka bace ai mace da namiji tamkar auduga da ashana ne, aman kayi gagawar sakawa, tambayar a nan itace WUJDANE zata iya kwatar kanta ne ko kuwa a kada mata ta mutu ta lalace?🤣 sannan mu yi gangamin zuwa gashi🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀
[2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*39*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*
Chapter 18 · 0% Book details