← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 26

Sashe 12

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun jima suna kalon nan, can ya sauke ajiyar zuciya bayan yanke hukuncin fada mata ko shi wanene da yayi ya juyo sosai da kalonsa wajenta dan ya gaji, ya gaji iya gajiya , bai san yanda xai iya dauka ba idan ya ci gaba da wannan wasan buyan, ya gane cewar shi ba komai bane a wajen abinda yake ji game da Wujdane, ya dauki aniyar idan har ta nuna bata ra.ayin hakan ba zai yi mata dole ba tun kafin abin yayi nisan da ba xai iya dauka ba,
Hannunta na dama ya kamo cikin nasa, ya mayar da hankalinsa kanta sosai ya ce " *WUJDANE, KIN SAN INAJE NAN?*

kalonsa take sannan ta kali kifofi biyun da ya nuna mata, ta dawo da kalonta da alamar bata san ko inane ba,

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce" *wa.innan gidaje da kije ganni, gidajen mutanen da suka kori iyayena ne dan an samu cikina ta hanyar da bai dace ba, wato gidajen nan gidaje kakanina ne wa.inda basa maraba da zuwana duniya dan ina matsayin.......*

Sai yayi shiru ya kasa karasawa fan yanda wani tsoro ya diro masa da bugun zuciya da dana sannin fada mata maganar a wannan lokacin duda bai gane inda hawayenta suka nufa ba, hawayen an cuceta ne? Hawayen takaici ne ko na menene????????

🤒😕☹
[2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*36*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

A hankali ya sada kansa kasa, bai cika hannun nata ba hakan ya bata damar jin yanda jikinsa ke rawa karkarkar

Hannunta na hagu ta saka ta share dan siririn hawayen da ya zubo mata sannan ta yi kokarin saisaita nutsuwarta ta kara waigawa ta kali gidajen nan biyu

Hannunta ta kawo a hankali daidai fuskarsa ta saka ta dago da habarsa abinda bata taba yi ba inda jajayen idannuwansa suka shiga cikin nata wa.inda har suka tsoratar da ita aman ta dake da yar jarumtar da ta yi mata saura ta ce" *ABAN BOY ka mayar da mu gida kar Mom tayi ta duba hanya fa*

Wani iri ya ji sunnan da ta kira shi da shi, sannan yanda ta basar da maganar da ya dauko abin sai ya bashi mamaki, a ransa ya tambayi kansa mai hakan ke nufi? Bama ta son sannin karashen maganar da ya saka aka kori iyayena dan ba zata iya zama da ni ba ko mai hakan ke nufi?

Murmushi Wujdane ta saki wannan karon tayi watsi da tsorotsoronta ta ce cikin wata murya mai kontar da hankali" *Mijina ni fa yunwa nake ji, ka kaimu mu ci abinci tun kafin na rikice maka da kuka a nan* ta karashe tana mai yin kalar shagwaba sosai wanda ya saka tsikar jikinsa mikewa har ya kwalalo ido yana kallonta da mugun mamakin sunnan da ya ci a yau wato Mijinta,

Boy ne ya miko masa wayarsa dake ringin yana hade rai an katse masa gm dinsa hakan ya ankarar da shi , bai iya daga wayar ba , bai iya tabuka wani abin ba bayan kuna motar da yayi cikin mutuwar jiki ya harbata kan titi ya shiga tuki

Shiru ne ya biyo baya domin ko radio bai kuna ba, boy kuwa bai karbi wayar ba saima konci da yayi baci ya fara daukansa,

Tsakanin Alaidine da Wujdane kowane na kokowa da tunaninsa, shi kam ya rasa a wani hali yake ciki hakan ya saka yana tuki ne yana dan kalo wajenta kadan,
Ita kuwa tana tambayar kanta ne , ta kai darajar da zai fada mata wannan sirri nasa mafi girma wanda yake cin zuciyarsa kamar mai? To maima ya kawo shi har ya fada mata ne? Yana sonta ne ko mai?

Ajiyar zuciya ta saki a cikin ranta ta ayana koma meye dalilinka na yin hakan , zuciyata ta jima da aminta da kai a yanda kake , ka rigaya ka gama da zuciyata

Yana tsayar da motar ta bude ta fito , ta bude masa baya dan ya dauko Boy sannan ta kwaso wayoyinsa a hannunta

Boy ya dauko tana gaba yana biye da ita tamkar iska zata dauke shi

Haka yake ji,
Suna shiga falon ta cire mayafin ta nufi wajen Mom

Zama yayi bayan ya shinfide Boy a nan saman kujera, yayi tsuru yana tunani yana dan kada kafafuwansa

Khadija ce ta karaso dauke da ruwa masu sanyi da kofi ta miko masa tana murmushi ta ce" yaya ga ruwa

Dago da kansa yayi sai suka hada ido da Wujdane wada tayi tsai tana kalonsu, ranta na tafarfasa gannin ya mika hannun ya karba sannan bai daina kalonta ba harda yiwa Khadijar murmushi yace" thx dear

Wata kwallah ce ta tarun mata a idannuwanta, a hankali ta mike ta haye sama ranta in yayi dubu ya baci haka kawai take jin haushinsa da na khadijar nan

Zurbat ya mike da niyar binta sai idannuwansu suka sarke da na Mom wace ta lura sarai da abinda ke faruwa, ta watsa mada wani kalo na bashi da kirki ta juya ta fice daman makota zata shiga

Zagaye Khadija yayi ya nufi saman wace ta bishi da kallo ta kada kai a ranta tana ayana " aban boy yana fadin babu macen da zata juya shi, yau ga wace take juya shin yake juyuwa ba tare da ya sani bama

Ya kai sau uku yana dora hannunsa da niyar bubugawa aman sai ya daina,
Har ya juya zai sauka ya dawo a hankali ya murda kofar ya shiga dakin

A konce ya tarar da ita, tana kallon silling, gefen idannuwanta kuwa zar abin hawaye ne ya biyo ya zubun mata,

Har kafarsa hardewa take wajen karasawa gefenta, yana kalon fuskarta a hankali ya zauna yana mai tambayar kansa hawayen kishinsa ne?

Yatsarsa ya dora ya dangwali hawayen hakan ya saka ta mike da sauri tana kalonsa

Yatsar nasa ya nuno mata ya ce" hawayen kishin Alaidine ne ko mai nake ganni a fuskar Wujdane?

Kalon hawayen fiye da hakan ne ta yi masa ta kawar da kanta bata yi niyar tanka shi ba

Zama yayi dangalgal saman kujerar ya ce" ki bani amsa bafa na son ina tambaya ana yi min banza fa

Bakinta ta murguda cike da haushi ta ce" hawaye? Na yiwa wa hawaye? So fa kace? Kuma ka rasa mai zaka ce sai wannan? Aa ni ba hawayen da nake abu ya fada min a ido domin kaima ka fada soyaya karya ne, nima ban yarda da ita ba

Yatsarsa ya dago ya daga murya ya ce" Wujdane, So soyaya ba karya bane, sai dai idan baka hadu da wada ya dace da zuciyarka ba

Aman kina nufin bakya sona kennan har yanzun?
Ya karashe yana kafeta da idannuwansa

Ta mere bakinta ta mike tana kakabe zanin jikinta tamkar wada ta fadi kasa

Janyota yayi da karfi ya rukunkumeta a jikinsa, bugun zuciyarsa na dukan nata bugun zuciyar , lumfashinsa na sauka a kan kafadarta murya a shake ya ce" *Ba Zaki so bawan Allah ba? Ba zaki sasautawa zuciyar da kika gama yiwa illah ba? Ko kema kina cikin masu kyamata ne? Kema kina kyankyamin Shege n......?*

Da sauri ta raba jikinta da nasa ta tsura masa ido yanda du ya zama wani iri, gaba dayanta ta fada jikinsa ta rukunkume shi ta saki kuka mai sauti, wanda rabonta da irinsa ita har ta manta, wai dama haka soyaya ke mayar da zuciya mai rauni? Haka zata tsinci kanta a ciki ita Wujdane din inna da Malan?
Cikin sarkewar Murya ta ce" danme du yanda na so na kauce ka furta kalmar nan sai da ka furtata? Idan rabuwa ne kake so da ni ai ba sai ka biyo ta wannan hanyar ba ko? Kai ka zubar da karatunka ne ko ka zubar da adininka ne? Dan Allah yayi ta haka ka fito an gaya maka ban sani bane? Ko an gaya maka idan ka mutu dan ta haka aka sameka shikenan layinka faban da sauran al.umar annabi? Ni ba rokonka zanyi da ka sasautawa zuciyarka ba tilastaka zanyi, ni ba kuka zan zauna muna yi a kulun fa kai ba kan hanyar da Allah yayi zaka zo duniya ba aa rayuwa zanyi da kai koda kaine na dari ba wai kadara na farko ba, kai baka san kadara bane? Ko an gaya maka akoy iyayen da zasu fito du lalacewarsu su nemi haka wa yayansu ne? Baka gannin kana saka su Mom a halin kunci bayan wanda suke ciki na rashin rungumar kadarar iyayensu ne? Baka san irin abinda suke ciki idan sun ga bacin rai a fuskarka ne? Du ni.imar nan da Allah yayi maka ba zaka gode masa ba ka watsar da wani tunani naka na daban ba? A kanka aka fara ne ? Kana so kace kai kana da zabin yanda ka so Allah yayi da kai da rayuwarka ne yaya? Ina mai rokonka a nan gidan duniya karka yarda ka kuma furtan wannan kalma da bana bukatar jinta daga bakinka
Abin na wujdane tamkar mai sambatu domin idannuwanta ruf a rufe tana yakushinsa tana fada ne da gaskiyarta kan abinda ke bata mata rai

Alaidine tsai yayi yana jin yanda wata kaunarta ke kara shiga zuciyarsa, har ransa yake jinta sannan magangannunta sun yi masa ba zata, daman akoy mata masu irin haka? Dama akoy mata masu hankali haka? Fada ne take yi masa kan abinda yake yiwa kansa kan bata so, ji yake tabas zai ririta Wujdane dinsa, zai malaka mata ko mai take bukata a duniya zai nuna mata soyaya a baki a aikace a gaban kowa, zai sota tamkar nama daya a miya, aman abu daya ne har yanzu baya gannin zai iya yi shine ya zama ita ta zama shi, su Zama abu guda , baya tunNin zai iya haka saboda tsananin kishinta da yake , idan ya tuna wani ya shiga gonarsa kafin shi yakan ji takaici har tsakar ransa hakan nema zai hana shi zama abu guda da ita aman fa soyaya sai inda karfinsa ya kare
Chapter 12 · 0% Book details