← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 26

Sashe 14

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsam Mom tayi, 8dannuwanta suka hasko mata rantsuwar mahaifinta kan idan ta saki ta dawo mada da cikin shegen nan na jikinta , ta je ta zubar a hanyar iskancin da ta saba sai ta dawo muhalinsa idan kuwa ba haka ba sai ya tsine mata idan ta dawo masa gida da cikin,
Ajiyar zuciya ta saki ta bi su Wujdane da kalo, tana tsoron yin maganar a gaban Wujdane taji sirin Alaidine, tana tsoron wata fitinar a irin yanda Alaidine ya shaku da wujdane tana hudun idan ta ji wannan lamari ta guje masa domin abin yan matan nan na zamani basa tunani sai dai su haye kan tsani

Jamail kam ya fahimci Mom dinsa hakama Alaidine wanda ya sada kansa yana sauraron abinda ke faruwa

Mikewa Jamail yayi ya kali wajen Aisha Da Wujdane ya ce" madame mu tafi dakin Mom mana mu barsu su zanta da matar yaya

Alaidine ya dago da kansa ya sauke kan Jamail, sai ya saki dan murmushi ya maida kalonsa kan Wujdane sai kuma ya kali khadija da ta fito itama take kalon abinda ke faruwa, haka ya juya wajen Marwa, a kasan ransa ya baiwa kansa amsar ta san dalilin da ya saka mamarta da yayarta suka yi nisa da juna dan haka ya ce cikin murya mai nuna kasala da an tabo maka miki ya ce" ka barta Jamail, *Matar Alaidine* ta aminta da yanda yake, a haka take zaune da ni saima idan na nuna damuwa ne a kan lamarin take hukuntani da fushinta, aman ka ganta nan bani da abinda zan boye mata daga Mom dina da Aba sai ita du fadin duniya domin sai da ta ji wanene ni kafin ta koyi sona

Kalonsa kawai Mom take cike da mamaki da kuma tausayin Wujdane, a hankali ta maido da dubanta wajen Wujdane ta sakar mata da tsadaden murmushi mai tsayawa a zuciya sannan ta dawo da dubanta wajen kanwarta dake kalon Alaidine tana tambayar kanta shine? Shine yaron wajen yayarta ya zama cikeken mutun haka mai cike da kamala da kwarjini? Shine wannan kakarfan namijin haka? Da abansu ya matsa har aka zubar da cikin nan da ya tafi shikenan?

Mom ta ce " shafana, inajin ba zaki manta yanda muka yi da Dad ba, a gabanki yayi rantsuwar kar na dawo masa sai na barar da kyautar nan da ya zamto garkuwa gareni da ni da dukan jama.ar da ta zagaye shi, na san ko a cikin anguwa zaki ji sunansa *Elhaj Alaidine*, shine wannan yarona da shi da Anwar shi soja ne sai Autansu Jamail shima kinga matarsa, sis ina cikin kewarku fiye da tunaninki aman ya zaki yi da rantsuwar dad ?

Jikinta ne yayi sanyi, ta mikawa alaidine hannu kan ya zo gareta,
A hankali ya taka ya karaso wajenta ya zauna, ta shafa gefen fiskarsa da sajensa ta saki murmushi ta ce" SON,

Shima kalon nata kawai yake ya dan juyo wajen su Wujdane sai ya ga wayam basa nan ya dawo gareta ta ce" insha Allahu ni zanyi yanda zan yi dan na ga kun dawo gida gaba dayanku, da gatanku a kulun Mamy maganarta ke tayi ta tambaya ko yanzu mai kike yi? Ko kuna tare da Yaya? Ko kin haihu? Rayuwarki ta ci gaba? Abinda dai taki amincewa shine kin mutu takan cewa ita tana ji a jikinta kina raye, su yaya du ba a gari suke ba domin du sai tsoron Dad ya saka kowane yayi nesa da shi sai nice nake gari nima sai na jima ban saka shi a idona ba, Mamy tana zaune da shi a haka, ta kawar da kanta tayi hakuri aman a kulun burinta ta ji labarinki bata san cewa yarta ta zama big hajiya ba ga jikokinta har sun yi aure komai da komai

Bakin Mom yaki rufuwa hakama na yar uwarta sai labarin yaushe gamo suke sannan tana rike da hannun Alaidine wanda ya gaji da zama yana ta hangen sama

Zaune suke, Aisha na biyewa Marwa labari Wujdane kuwa na gefe tayi gum da bakinta , iya du surutunsu ya cika mata ciki tana son ta dan zanta da yar uwarta aman abin ya hagara domim marwa ba dai labari ba

Tsuru take bin Wujdane da kalo, ta lura Wujdane bata da magana aman ita ta birgeta sosai da ita fa amaryar anguwarsu suna da kyau sosai wato Aisha, saima da taji cewar itama amarya ce ta zuba tagumi can ta ce" Oh nima watarana amarya ce ko aunty?

A tare suka juyo wajenta Aisha ta bushe da dariya, kai Marwa bs dai dirama ba ta ce" sosai mai sunnan Mom, ki ci gaba da kare mutuncin kanki kin ji? Kema watarana amarya ce

Wujdane ta danyi murmushi domin sai yarinyar ta bata dariya, wai iya nan so take ayi mata aure kenan, toh maima ta sani a auren?

Haka dau sukayo ta yin labari har Marwa ta bingire nan baci yayi gaba da ita

Da sauri aisha ta dawo ta tsare Wujdane da kalo irin na kurullahn nan

Wujdane ta ce" meye? Kallon fa?

Aisha ta saki murmushi ta ce" ai sai a bani dadadan labari an shirya da big yaya, kai aman kun birge ni aunty yaushe aka tsunduma a soyatar haka?

Wujdane tayi tsam tana kallon kasa fuskar Alaidine kawai ke yawo a idannuwanta da kuma zuciyarta, tabas ta sani yanzu ta fada soyaya mai tsauri wace ta saka zuciyarta a garari domin tana mugun kishin Alaidine fiye da tunanin mai karatu dan kuwa kwana biyun nan da suka yi a karkashin innuwa guda suna cin abinci tare, suna kulawa da yaronsu suna kulawa da du motsin dan uwa sai take tunanin idan zai koma gidansa ya zata yi da ranta? Sai take jin haushin Alawiya , yanzu du kulawar nan da kallon da yake jifanta da shi mai tsuma zuciyarta haka zai je yanaiwa wata can? Sai kawai taji hamkalinta ya tashi iya tashi harma ta tsiri share shi sai yayi lalaba,
Aman abinda ke bata mamaki shine idan yana zaune ko suna hira da ta fada jikinsa zai yi gagawar zameta ne ya bar wajen, ta rasa mai ke damunsa haka? Aman fa kulawar duniya yana bata yana kare hakinta yana nuna kishinta karara domin ko masu aikin gidan maza yayi masu shamaki da shawagi a tsakar gidan falo kuwa yama haramta masu shigarsa
Murmushi ta saki da ta tuna idan zata yi baci yakan zauna ne ta zuba mata ido bayan yayi mata adu.a hannunsa cikin nata idan sun hada ido sai ya furta mata " *i love u*, har tayi baci sai ya gyara mata rufarta ya dawo wajen boy su konta

Aisha ta kama baki ta ce" lale, wannan ita ake kira soyaya mai tsada, ka ga salon soyayar miskilai kenan
Bata kai ga rufe bakinta ba ya turo kofar ya shigo, dan dakatawa yayi yana kalon wujdane dake zaune ta jinginar da bayanta jikin abin bed din kafafuwanta a mike, doguwar rigarta ta ja sama sai ta fitar da fararwn kafafuwanta waje tana zabga murmushi tana sauraron Aisha dake ta yi mata tambayoyi tamkar wata yar jarida

Angel, ya furta murya ciki ciki

Wujdane ta dago da sauri tana kalonsa da ido yayi mata nunin ta gyara rigarta

Tana ja kuwa sai ga Jamail ya shigo shima yana fadin" hajiya ki tashi mu juya yama na yi sosai

Aisha ta mike tana gyara rufar mayafinta, ita kam gulma na cinta sosai aman ya zata yi? Haka ta bi bayansa bayan sun tayar da Marwa suka sauka tare da niyar su tafi su juya da Marwar aman banda mamanta dan ta je ta baiwa yayanta abinci sannan su juyo da shi su dauki mamansu

A hankali take takawa kyam idannuwansa a kanta har ya kure mata waje

A hankali ya duka, ya mika hannunsa ya kami hannunta na dama ya dora lips dinsa ya sumbuta wanda hakan ya saka mata faduwar gaba da wani irin abu da taji har tsakiyar kanta

Dago da kansa yayo yana kalon fuskarta, shi kam a kulun kara masa haske take a idannuwansa, ya shiga dan murza hannunta murya ciki ciki ya ce" Auntynki bata da lafiya har an kamata a asibiti, tana da bukatar kulawata a gefenta shi ya saka zan juya gida dan na kula da ita

Wani irin faduwa gabanta yayi, yanzun tana murnar yana kusa fa ita shine kuma zai yi maganar tafiya, duda rashin lafiya ne aman ai itama tana da bukatarsa a kusa da ita ko?

Fuskarta ya shafo a hankali ya ce" Angel baki ce komai ba? Ko zaki zo mu yi tafiyar mu?

Ajiyar zuciya ta saki, koda wasa ba zata nuna zalamar muradin kasancewa kusa da shi ba du irin shakuwarsu kuwa, hakan ya saka ta shiga dan janye hannunta a hankali ta ce" ka je ka kula da lafiyarta hakimta ne, Allah ya bata lafiya

Adu.ar kirki tayi masa aman sai yake gannin ba a farin ciki tayi hakan ba, mikewa yayi ya zauna sosai ya rungumota jikinsa duda yanda yake jin bugun zuciyarsa na karuwa aman ya riketa sosai a jikinsa, a hankali ya shiga kokarin lalubo lebenta wanda ya saka suka shiga shakar numfashin juna,
Jikinsa na bari ya shiga kokarin zaro harshensa dan kaiwa nata cafka yana ta yawo da kwayar idannuwansa a cikin nata idannuwan ta farkar da shi ta hanyar furta" Corazon, karfa dare yayi maka ka ga da nisa anguwowin, gashi har magariba ta shigo fan haka sai mun yi waya ko?

Tana gama fada ta kubcewa rikonsa domin sam jikinsa ba wani karfi , shi bai samu abinfa yaje neman ba sannan du jikinsa ya zama tamkar an zare masa laka sai uban kanshin jikinta da ya kwasa wanda ya kara saka shi zama wani shiru shiru

A hankali ya mike yana kalon bayin da take tsaye, ransa ne yaji yanai masa zafi kenan in dan ita ne yayi ta tafiya ko? Bata wani damu da hakan ba take nufi in dan na ita ne yafi ruwa gudu? Juyawa yayi ya nufi fita wanda yana bude kofar ya maido mata ita gam ya rufe mata
Chapter 14 · 0% Book details