Sashe 10
Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai kawai ya iya gyada mata dan gannin yanda ta damu, sannan da tace sama dakin wa? Su dai ba shiga bayinta suke ba, a saman kuwa daki biyar ne daya na Aba, daya na Mom, sauran nasu shi da kanninsa, bayan sun bar gidan kuwa sai Wujdane ta maye nasa, Aisha na Jamail, dayan kuwa Mom ta mayar da shi kicin dinta na biyu idan bata ra.ayin sauka kasa takan dora girki a saman,
A yanzu dai ba zai shiga dakin da matar kanninsa ta shiga ba, a takaice dai Mom na nufin dakin da Wujdane take ciki? Toh idan zai kwana a gidan fa? A kasa dai dakin Khadija yake wanda koda wasa ba zai so ya tare a dakunnan falon kasan ba dan kar su hadu ko su hada makotaka da ita, aman ina zai je ya kwana? Ko dai gidansa yake tafiya abinsa?
Yana nan zaune aka fara kiraye kirayen salar isha.i, ya mike da hankari ya fice ya nufi wajen bayin mai gadi ya shi ya fito yayi alwallah ya nufi masalaci
Bayan ya gama dukan salolinsa da adu.o.insa ya fito yana tafe da carbinsa yana ja har ya karaso gida
Yana shigowa ya tarar suna table suna cin abinci, aman bai hangi Wujdane ba, bai kawo komai a ransa ba ya zauna yana dana wayarsa
Alawiya ce ta yi masa missed calls da yawa da test message tana fada masa ba zata iya zuwa ba dan bata jin dadi sannan ba zata bar gidan ba kowa ba
Bakinsa ya yatsina ya ajiye wayar yana kalon Lami na jera masa abinci a gabansa tana faman fadin Uban gidanna ya jikin? Momy na fadin baka da lafiya
Bai amsata ba sai bin kulolin abincin yake da ido, a ransa yana tambayar kansa wa ya dafa abincin?
Bai taba ba, baiyi niyar ci ba don mugun kyankyamin dake damunsa
Jifa jifa yakan daga idannuwansa ya kalo wajen dakinta sannan ya maido dubansa wajen Tv har su Mom suka gama suka dawo Falo
Mom ta ce" Lami ki kuma duba min idan har ta farkan kin ji? Auntynsu a gaba a yi murzar ta dare ko?
Aunty Agaishat ta ce " Momyn yara yau yar taki da alama rigima take so mu yi shi yasa ta konta da wurin nan tana fadin cikinta ciwo, aman yanzu zan hau na murjeta idan yaso ta yi ta fushin
Mom ta yi murmushi ta ce" aa kinga a bi min yarinya a hankali yau yan mulkin ne ai kinga abincin ma ance ba
a ci dan haka kar ku rikita min ita
Du abinda suke tataunawa a kan kunayensa, har agaishat ta mike ta haye sama
Tambayar kansa yake kenene murza kuwa?
Yana nan zaune Mom na dan zantawa da mutanenta har aunty ta fito daga wajen Wujdane ita kanta sai kanshi take zubawa na kayan turaren da ta yi mata ta zauna itama aka shiga labarin da ita
A hankali ya mike, ya jaye jikinsa ya haye sama
Dakin Wujdane ya tura a hankali ya shiga daidai ta fito a wanka daga bayi daga ita sai tawul dan madaidaici wanda ya rufe mata mazaunanta kawai, wankan ruwan turare ne ta yi bisa umarnin Aunty Agaishat
Kanta sai tsago yake na ruwa sannan ya dan kare mata ijiya bata ga Alaidine da yayi mutuwar tsaye yana kallonta ko dakin ya kasa rufewa bale yayi kokarin yin abinda ya kawo shi dakin
Wayarsa ce ta......
[2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*35*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Shigowa Marwa ta yi tana dan rarabewa abinka da rashin sabo da mutane, sannan muryar namiji da ta ji ya tabatar mata da namiji a gidan
Aisha ta bata damar zama ita kuwa ta nufi frij dan dauko mata jus
Rabewa ta yi ta sada kanta, murya can ciki ta ce" ina yini
Jamail kalo daya yayi mata ya amsa yana mai mikewa dan shigewa dakinsu, sai yake gannin kamar ya san yarinyar nan toh aman a ina ya santa?
Tana miko mata jus din Marwa ta mike da sauri ta ce" aa aunty amarya zan koma gida sai Mamana ta barni zan dawo
Kafin Aisha ta bata amsa har ta fice da sauri sauri dan yanda take jin faduwar gaba da tsoro
Tana fitowa suka yi ido hudu da yayanta Aliyu, ya zabga mata harara ya juya da sauri ya rigayeta fadawa gidansu
Mama mama, ai kuwa Marwa daga gidan amaryan can take, kin ganta nan
Ta dago daga dana wayarta da take ta sauke kwayar idannuwanta a kan Marwa, yanda Marwar ke bari ta gane eh gaskiya ya fada , da hannu ta yafito ta dan Abanta yana gidan idan ya ji zai hana ta dukanta
Marwa a hankali ta karaso tana son gane idan abanta na gidan ta wangale baki ko zai ceceta aman ina kafin ta fahimci hakan umanta ta damke hannunta ta ja kuncinta irin yanda ake yiwa yara ta kala mata yatsu a bakinta ta zazaro mata idannuwa ta ce" Marwa kennan bakya jin magana ko? Na hane ki da shiga gidan amryar nan shine kika shiga?
Mama dan Allah ki yi hakuri, ba ita kadai na tarar ba mama
Marwa ta fada jikinta na bari har kwalah ta fara ziraro mata
Ta girgiza kai ta ce" da wa kika tarar da ita?
Bata yi tunanin za.a tambayeta da wa ta tarar da ita ba, hakan ya kara tsoratar da ita ta ce" mamamamama da da mijinta yana gidan
Hajiya ta kama kanta ta ce " Ya Allah, yanzu Marwa da mijinta a gidan har kika shiga? Ai yau sai na yi maki duka tunda bakya ji, dan kinga ina tsoron zuciyarki ko? Sai na lalasaki a gidan nan sannan mu tafi na basu hakuri tunda baki da hankali ke
Mahaifinta ne ya fito daga falo da jarida a hannunsa ya ce" aa aa, banda lalasawa maman Marwa a yi mata hakuri, ina nema mata yafiya
Ta dago ta kale shi, yayi alwallah da alama masalaci zai je ta saki hannun marwa ta mike ta nufe shi dan taya shi saka takalminsa bata ce komai ba aman Marwa ta bata haushi , danme zata shiga gidan amare a wannan lokacin, ita da ta tafi gidan kakaninta mai ma ya dawo da ita? Aman aban Marwa baya so a taba masa lafiyar jikinta hakan yake sakawa wani lokacin take tabararta sai idan daga ita sai ita a gidan ne sai ta nutsu ta san idan ta yi zata daku ne (Marwansi🤣)
Baci barawo ne yayi nasaran dauke Alaidine a cikin irin halin da ya saka kansa, asubar fari kiraye kiraye ya farkar da shi inda yayi adu.ar tashi daga baci yayi salati ya sanar da ubangiji
Kokarin mikewa yake idannuwansa suka sauka a kan mahaifiyarsa dake zaune tana jan carbi sai a lokacin ya tuna a dakinta ya kwana,
Fitowa yayi ya dauki jakarsa da anwar ya kawo masa ya shige dakin wajen jamail,
Tastas ya tarar da dakin babu wani abu da ta bari ko wata kazanta haka ma bayin kyalkyal da shi, dan haka ya saki jikinsa ya yi wanka ya dauro alwallah ya dawo wajen salaya
Ya jima kafin ayi kiran sallah ya mike ya fice inda ya hangi hasken fitila dakin Wujdane hakan ya tabatar masa ta farka itama
Karfe bakwai da doriya ya dawo gidansu, direct dakin ya koma dan ya sake hantsewa kafin ya fito falo
Mom ce zaune a dakin, hakan ya nuna masa shi take jira dan haka ya zauna a hankali ya shiga gaisheta
Mom ta amsa masa hankalinta a kansa har ya samu waje ya zauna ya dan tankwashe kafafuwansa
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" Allah bai haliceka a yanda ya haliceka dan ka yi masa laifi ba, bai halice ka dan ka gama rayuwarka a kuntace ba, ka sakawa zuciyarka sasauci, ka sanyaya zuciyarka ka nema mata abinda take so, ka sani hakan ma da kake aikatawa laifi ne dan kamar kana fushi da yanda allah ya halice ka ne
Cike da tsarguwa Alaidine ya ce" Mom wani abin aka yi ne?
Ta yi murmushi ta ce" kar fa ka manta ni na haife ka Alaidine, shawara nake baka ka rungumi ni.imar dake tare da kai ka zama cikeken namiji tun kafin wuri ya kure maka
Tana gama fada ta mike ta fice a dakin ta nufi wajen Aba
Ajiya zuciya Alaidine ya sauke ya mike ya yaye labulen windows yana shakar sanyin safiya
Wajen karfe tara na safe Wujdane ce ke saukowa daga sama, ta sha doguwar rigarta kalar ash irin na kanti din nan, kafarta saye da takalmi fari kar mara tudu, sai kanta da ta yane da mayafi, yau tunda ta farka da kewar gida kawai ta farka hakan ya saka a shiru shirun nata na da ta kara wani
A hankali ta karaso inda ta sauke idannuwanta a kan su Mom da Alaidine dake zaune ya sake wanka ya canza kayansa sai kanshi yake da haske dake kara bayana a fuskarsa
Har kasa ta kai tana gaishe da Mom wace take amsawa cike da kula,
Bayan ta gama gaishe ta ta juyo da fuskarta wajen Alaidine ta sada kanta kasa ta ce" ina kwana *yaya*,
Alaidine da ya ga abij wani banbarakwai domin ko matarsa bata yi masa irin gaisuwar nan da mutunci ko shi ko iyayensa sai ya ji kansa ya kara wani girma, hakan ya saka shi dan sakin murmushi ya ce" Morning Hajiya Wujdane
Dago kanta ta yi jin yannayin amsa gaisuwar tasa kamar mai cike da farin ciki, ta dan murmusa ta mike ta koma can gefe aman bata hau kujera ba dan Mom na zaune a saman kujerar
Mom ta ce" Lamy ki kawowa yarinyata abincinta ta karya yau tayi latin tashi,
Wujdane ta ce" aa Mom, yau bana jin yunwa ne kwata kwata
Mom ta shida dan mitan wujdane bata son cin abinci tunbama Aisha da bata gidan ba sai ya kasance ta rage cin abincin sosai