← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 26

Sashe 24

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama fadar hana ta yi tafiyarta abinta ta bar Aisha da kikifta ido kafin take samun waje ta zauna ta yi kiran number Jamail da wayarta dan ya dawo ya dauketa domin Kuwa Wujdane har ta fada adaidaita kuma ba ko sisi a wajenta ( mai hali baya daina halinsa🤦‍♀)

Farkawa yayi, a hankali yake gannin dishi diahi kafin idannuwansa su washe kan Alawiya dake baci rabin jikinta saman bed din nasa rabi kasa ta yi mugun konci har jikinta yayi tsami

A hankali yake tuna abubuwan da suka faru, kansa ya girgiza ya ce" Alaidine me kayi haka? Ya salam ba gangan na suma ba tabas suma na yi , ya Allah ka sasauta min irin wannan zuciyar

Sai a lokacin Wujdane ta fado masa a rai
Ya kai dubansa wajen Alawiya, aman ai yau ba kwannan alawiya bane, idan bashi da lafia mai kwanansa zata kwana da shi mana ,
Kansa ya dafe ya ce" ya Allah ko yaya Wujdanena zata ji? Matar amana , mai fada min gaskiya, Wujdane sonki kawai nake

A hankali ya mike ya tsalake Alawiya ya gyara mata konciyarta ya shige bayi ya dauro alwallah

Nafila kawai yake jerawa yana godiya ga Allah sannan ya roki Allah da ya bashi ikon yafe masu sannan ya kara nemarwa iyayensa gafara wajen Allah

Wujdane Walahi walahi walahi idan baki fada min uban me kika zo nema a gidan nan kafin malan ya dawo sai na yi maki nunusar hankali

A hankali ta kalli yayan nata, ta ga dai yanzu fa ta zama yar gayu, idan kuwa ta yarda sai ya jinyatata a banza,
Mikewa ta yi ta shiga kakabe hijab dinta ta kalli mamanta dake tsaye ta kama haba tana tarababi da Wujdane batai hankali ba? Ta zo masu kawai tace a nan zata kwana bayan an raba rigimarta da dan adaidaita tace masa ya kawota sadaka har yana kokarin kwave riga wai su daku ita kuwa ta tsaya tana jiran ya kwaben yayanta ya karaso ya biya ya toso keyarta yana tambayar lafiya me ta zo yi? Shine tace ta zo kwana gidan ubanta ne haka gatsal ba kwana ba komai

Wujdane ta yiwa mama murmushi ta ce" kifa daina damuwa mamanmu mana, kin ga bashi da lafiya ne yana asibiti kuma ba kowa a gidan, kin dai ji labarin gidan ni tsoro nake kuma gidansuma ba kowa shine na yo nan

Mama ta kama baki ta ce" kuma? Karya kika fara? Da dai ko kashe ki za.a yi bakya karya Wujdane

Kanta ta dafe bayan ta tabatar da ta saka jikinta dakinsu ta rike kofar da kyau ta turo ta rufe ta leko ta window ta ce" yi hakuri umanmu *Yaji na yi*

To fa zan karasa ko sisina ta daina fushi da ni🤣🤣😍😍😍😍
[2/1, 2:33 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*45*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

A tare suka ce" yaji? Wani irin yaji?

Wujdane ta dan dafe kanta , ta girgiza kai kawai ta cire hijab dinta ta zauna bakin tabarmarsu tana kallon dakin

Ke Wujdane ko ki bude dakin nan mu yi maganar arziki da ke, ko na bale kofar nan na hada maki jini da majina kin ji na rantse

Bakinta ta tabe ta shiga jujuya kafarta

Mama ta zauna yarab, ta dafe kanta, kafin a yiwa Wujdane aure tana da fada da rigima a waje aman idan ta shigo gida bata son bacin ran iyayenta, ita kuwa wannan wujdane din kai tsaye take maimakun ta yi laushi sai take ga kamar ta kara tsaitsaye mata, ajiyar zuciya ta sauke kafin take karasawa bakin kofar ta ja ta dan tsaya
Muryarta a konce ta ce" yar abanta, menene haka kike fada? Kina son hankalina ya tashi ne ko me?

Wujdane ta dan cuno bakinta tamkar maman na ganninta ta ce" umma, kina gani na hane shi abu, bayan ya gamai min maganar ba zai yi ba ya je yayi, haka ake rayuwa?

Mama ta girgiza kai ta ce" aman Wujdane ke ya dace ki bi shi fa

Wujdane ta dafe kai , can ta ji muryar mahaifinta ya shigo, nan umma ta labarta masa komai,

Zama ya yi ya tsurawa Dakin ido, can ya nisa kasa kasa ya ce" umma, kin ga yanzu dare ya yi sosai, ko menene zamu ji da safe in sha Allah

Umma kam ta dai yi shiru ne dan bata saba yi masa musu ba ta mike ta shige dakinsa dan yau dole ta kwan a nan dan Wujdane ta garkame daki

Kamar yanda Aba ya saba yayi nafilfilunsa ya tsaya tsayuwar dare, rokonsa Allah ya nutsar masa da yayansa bale wujdane, ya yiwa Wujdane adu.a sosai ya roki Allah da ya shiryar masa da ita

Da asuba tun daga soro Aba yake jin ana dimar abu muryar yayan su Wujdane na tashi kadan kadan yana fadin" in dai ba zaki yi magana ba sai na bala ki yau ni da ke a ga mai taurin kai

Kai kai kai wannan yaron menene haka? Matar aure ce fa? Kulll in ganni ka kuma dukanta
Aba ya fada yana azamar tare dukan

Wujdane ta dago ranta a bace fuskarta a jagule , har ta juya zata koma daki ta dawo ta ce" yaya ko dai kaima kana cikin masu tsangwamana ne dan kalar fatana da kuma idona? Na rasa gane kanka kai kawai a rayuwa baka da abin huce haushi sai jikina? Har kana dira a kaina kana tatakani kuma ka fita waje a ce maka wa? Tun ina karama kake horani yanzun ma ban fi duka wajenka ba? Kai dai Allah ya shiryeka
Rana gama fada ta yatsina fuskarta ta shige dan yin Sallah

Aba ya girgiza kai ya dubi yanda su umma suka saki baki suna kallon dakin su Wujdane

Murmushi yayi ya juya kofarsa ya zauna yana jan carbinsa hankali konce

Sai da ta gama azhkar ta shafa fatiha ta fito cikin nustuwa ta duka har kasa ta ce" abana barka da safiya

Aba cikin jin dadin gannin yanzu Wujdane har tana magana haka nauyin bakinta ya dan rage ya ce" barma mamana, kin tashi lafiya?

Wujdane ta yi murmushi tana kallonsa kadan

Aba ya sauke ajiyar zuciya ya shiga yiwa Wujdane nasiha cikin nutsuwa , can ya ce" aman abin mamaki Har kin yi fushi Wujdane na?

Wujdane ta turo bakinta ta ce" Abanna, ba wai ban dauki nasiharka bane,

Ta dan sauke ajiyar zuciya ta ce" dan ya ga na damu da shi ne? Bayan ya ce ba zai kuma yin abinda raina zai bace ba shikenan sai kuma ya yi?

Me ya yi? Aba ya tambaya yana son kara gaskata abinda zuciyarsa ke fada masa idan ta fara nutsuwa ko da saura wato tana son mijinta ko har yanzu rigimar an hadata da wanda baya sontan ne?

Wujdane ra dago tana kallon Abanta, haka kawai sai take jin ba zata iya fada masa gatsau dalilin da ya sa take jin haushin mijinta ba, to kawai sai ta ce dan yana jin haushin shi ........ne? Aaa koda mahaifinta ya san wanene mijin da ya aura mata ba zata iya maimaita masa ba, kanta ta sada , na farko a rayuwarta da ta ji kunyarsa, kunyar Aba take sosai harma ta ji haushin kanta ya aka yi ta kwaso ta zo?

Aba yayi murmushi yayi godiya ga Allah a ransa, ya ce" tashi ki je ki karya zamu yi maganar.....
Yayi haka ne dan baya so ya kwasheta ya koma da ita haka? Tabas ya sani yaji bashi da alkhairi ba dabi.a bane aman kuma baya so yayi abinda za.a ga ko dan yana talaka yake rawar kai haka, da farko ya yi masu auren nan ne ba tare da yardar dayansu ko na mahaifiyarsu ba, ya tisa keyar su an kai su wajen da basu shirya ba ba shiri irin na amare, ya sani halayen yarsa na taurin kai aman sai Allah ya dora mata kunyarsa, tana jin nauyinsa a rayuwa fiye da komai , batai masa musu.........shi ya sa shima yake mata uzuri da fatan alkhairi, ba zai dauketa a yanzu karo na biyu ba tare da ya binkici abinda ke faruwa ya mayar da ita gidan mijinta ba, idan har yayi bincike ya ga shirme ne irin nata baya ce masa komai ya dauketa da kansa a adaidaita sahu ya bi bayanta ya mayar da ita gidanta

Lokacin da su Aisha suka zo da jamail, a wannan lokacin kowa ya samu zuwa asibiti, Alaidine yana bin mutane da kallo da an bude kofar an shigo sai ya kali wajen da sauri ko zai ganta aman ina sai ya ga ba ita bace, a ransa yake ayanna ke kuwa mai zuciyar Alaidine ina kika makale haka ne? Wujdane ki fa shigo kar ki saka na yi abin kunya na tambayeki a gaban jama.ar nan

Shiru shiru har lokacin salar la.asar yayi, wanda Alaidine ya daure ciki ya shiga wani hali na rashin gannin matarsa, tana ina? Me take ? Ya aka yi bata zo ba? Bayan ya fada mata mata irin son da yake mata, du alkawarurukan da yayi mata na sakata jin dadi a tare da shi,? Ko bata da lafiya ne?

Shi bai san kuma zaman me suke a asibitin ba bayan ya warke ya farfado daga suma kuma rikon me ake masa haka har da familynsa ta tare a asibitin sai wani nan nan suke da shi su mom kuwa an samu yan uwa kadan ta motsa sai an tareta sai dadinta kawai take ji ta kasa lura Wujdane bata wajen

Boy a kama ka ka yi alwallah ka samu ka yi sallah ko? Aba ya tambaya yana tsare Alaidine da kallo

Alaidine ya gyda kansa,

Suna mikewa ya ce" Aba ni zaman me muke kuma bayan da sauki jikina? Ina likitan ne ya zo ya salameni haka mana

Aba ya ce" aa, ka ga ka yi hakuri har likita ya salameka da kansa

Alaidine ya mugun tsare fuskar Aba da kallo, irin kallon nan na ka ji kaina
Chapter 24 · 0% Book details