← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alaidine kuwa ido ya tsura mata yana karantar yannayinta, duda ba wani.mugun sabawa yayi da halayanta ba aman zai iya gane idan tana cikin walwala ko she's sad,
Sai ya tsinci kansa da damuwa da yannayin da take ciki domin gaba daya sai ya ga kamar bata cikin nutsuwarta

Mom ta mike ta nufi kicin da niyar bara ko dan jus ne ta hada mata ta sha karta zauna ciki ba komai

Mai ke damunki?
Alaidine ya jefo mata tambaya sannan bai kawar da idannuwansa s kallonta ba

Dago da nata idannuwan ta yi, sai ta ji ba zata iya yin ido cikin ido da shi ba, a hankali ta mayar da kanta ta sada ta shida dan murza karamar yatsarta murya ciki ciki ta ce" ba komai

A ransa yake ayana du miskilancina yarinyar nan ta fi ni da alama, bai gajiya ba ya ce" ko kina son fita ne?

Da sauri wannan karin ta dago da kanta harda yar alamar fara.a a fuskarta sannan ta shagwabe fuskar ta ce" Innata😟

Bai ce da ita komai ba sai da jan hankicinsa da yayi daga gaban aljihunsa ya kara zuba mata manyan idannuwan nan nasa yana dan murmushin da shi kansa bai san ya shagalta a yinsa ba, shagwabarta ta dake shi sosai, a ransa yake ayana du yanda ka yi da ita idan tayi react@ sai yayi mata kyau

Ita kuwa a ranta ta shiga jin haushin bakinta da ya furta masa damuwarta, domin tana gannin dan kawai ya tsankwaleta ne ya kara wulakantar da muradinta yayi hakan

Mom ta dawo da jus na aya mai kauri ta mika mata tana fadin oya shanye min kafin a jima ki ci abinci

Wujdane ta karba ta shiga kurba a hankali kamar mai zafi, shi kuwa ya mayar da ita tv dinsa ko kula da Boy dake faman yi masa labari bai yi bale mom da mamaki ya cikata na yanda soyaya ta mayar da Alaidine dinta

A hankali ya ce" idan kika shanye zan kaiki ki ga Innar yanzu, idan kuwa baki shanye ba ba ke ba zuwa

Ai da sauri Wujdane ta mike harda dan tsalenta ta kafa kai ta shanye gaba daya sannan ta nuna masa kofin tana kalon Mom ta ce" Momna kinga na shanye ko? Zai kaini ne?

Mom cike da farin ciki ta ce maza jeki shirya ya kaiki ai shi yayi alkawarin hakan

Da sauri ta juya abinka da riga mai lafewa a jiki takan nuna yannayin halita ne koda da wasu kayan a ciki, hakan ya saka jikinta rawa a cikin rigar wanda ya saka shi da sauri ya juyo wajen Boy ya shiga kokarin gyara masa rigarsa dan da shi zasu tafi

Sosai wujdane ta yi wanka da turare a jikin lesh dinta da aka yi mata dinkin riga da zani da dan kwali,
Bayan ta saka ta ciro mayafinta mai ruwan blue mai duwatsu farare kal a jiki sai takalmanta da yar jaka marar girma ta fito da dan kwalin dan Mom ta daura mata

Da ido kawai yake binta, komai ta saka tana tafiya da imaninsa ne, du shigar da zata yi tana karbar fatarta ne sai gashinta dake bashi mamaki har yau, shi dai ya taba gannin mahaifinta bata kama da shi aman bai taba gannin mahaifiyarta ba

Mom ta gyara mata gashinta ta daura mata dan kwalin, duda ba irin daurin zamanin nan bane aman sai yayi mata dan das da shi tamkar yar tsana

Mom ta miko mata leda baba, wace ta saka mata turaruka da atampa biyu manya sai mayafi guda tace a gaishe da innar

Cike da murna Wujdane ke godiya, bakinta ya ki rufuwa tana murnar gannin innarta

Motarsa baka mai bakin glass ya dauko gaba dayanta baka iya gannin na ciki sai dai shi ya ganka,
Ciki suka shiga suka dauki hanya wada Wujdane sai waige waige take tana kallon gari kamar wace ta shekara bata fito ba abinka da kafar yawo har suka iso anguwarsu Wujdane sai ta dawo sakin murmushi dan gannin yanda yara a birni ba kauye ba suke bin motar , har manyan kansu sai an raka motar da kallo anguwar kuwa datin nan na nan dankare ba.a canza ba

Kofar gidan ya ja ya tsaya, ya shiga karewa anguwar kalo harma da ginnin gidan su Wujdane, juyowa yayi ya shiga kallonta ta yi ta yi ts bude motar ta ki buduwa sai ta zauna ta shiga kifta ido
A ransa yake ayana Allah mai iko, yanzu cikin gidannan ne gidan da aka haifi wannan anjel din, ita kuwa bata wani damu ba dan sai ta ga an gyara wajen da ya dukan nan kamar zata fadi katangar aman yanzu an gyare ba.a hangen gidansu ta kofa

So take ya bude mata ta fice aman ya ki budewar ta rasa dalili, dago da kanta ta yi da niyar yi masa maganar ya bude mata mana sai ji ta yi ya cafke mata lebe da ta saka jan bakinta yana walwali ya shiga sidewa ko ta kan Boy baya yi wanda ke baya yana buga gm bai ma san abinda ke faruwa ba

Sai da ya side shi tas ya cika mata bakin yana dan hade fuska wanda da kyar ya saisaita numfashinsa, itama har dan kwalinta ya kunce sannan ta zazaro ido kamar an jijiga bera a kwano du ta rikice da sauri ta kai dubanta wajen Boy sai ta ga yana sha.aninsa ta juyo da niyar yin aikin nata wato fitsara

Yatsarsa ya dora kan lebensa ya ce" idan kika furta kalmar da bata yi min ba zan juya da ke ne gida, ai kin san na hana ki shafa abinnan idan zaki fita aman kika shafa dan na sosa maki inda yake maki kaikayi, toh na sosan idan kuwa bai isa ba na kara?

Da sauri take girgiza kai ta gyara daurin dan kwalin tana kara goge leben nata dan kar ya juya da ita haka kawai

Murmushi yayi ya bude mata ta fita da sauri ta bar jakar nata a nan ,

Boy ya budewa ya bi bayanta shi kuwa ya shiga dan shafa geme a hankali ya furta" i love u so much

Da murna ta shiga gidansu, inna na zaune tana yanke akaifa ta dago itama da murnar tana yiwa Wujdane dinta lale marhabin

Waje ta samu ta zauna da boy ta gaishe da innarta wace cike da fara.a take amsa mata da tambayarta gida da iyayen mijinta da mijinta da kishiyarta

Wujdane ta ce" ai da shi ma muke tafe

Inna ta mike tana salalami ta dauko katon hijabinta ta saka wujdane ta yi masa iso, sannan ta shiga neman abinda zata bashi

Gaba take yana biye da ita, abinda ya birge shi a gidan su wujdane shine yanda gidan ke share kyalkyal da shi, tamkar da masu gyaransa ne daban, sai yanda du kananta gidan ba zaka ga can kwano nan ludayi can kaza ba, komai a kilace yake wajen da ya dace

Tabarmar da ya gani shimfide ya nufa a hankali ya cire takalminsa ya zauna da bismillah ya bi Wujdane da ido wada ta cire mayafin nata ta shanya a nan ta fada dakin Malan dan ta san inna nan ta shige

Yelumun kuwa ta tarar da ita ta fitar da sabin kayan shan ruwan malan na azumi da jus kwaya daya bigi na coca bashi da sanyi kuwa ta mimiko mata tana fadin maza wanke ki zuba masa ruwan randar dakina

Murmushi kawai Wujdane ta yi , innarta ba dai son karama baki ba , takan ajiye irin jus idan malan ya kawo bata shan nata sai ta boye dan gudun bakin kunya

Haka ta fito ta yi yanda tace, sai da ta ajiye masa ta tsiyaya masa ruwan sannan innar ta fito ta yi masu salama ta samu waje dan nesa kadan ta dan zauna

Tsugunawa yayi ya shiga gaisar da innar, wada sai a lokacin ya dago yana kallonta, sai da ya saki ajiyar zuciya hango kama a wajen innar da Wujdane har idannuwansu da farinnan
Nan da nan ya ji kaunar tsohuwar ta shiga ransa sosai da gannin girmanta, sosai wata kunyarta ta rufe shi wada bai yi tunanin jinta ba hakama innar ba wani ido ta hada da shi ba dan kunyarsa take ji har suka gama gaisawa ta yi godiya ta mike ta koma dakinta

Sun dan jima ya sha ruwan nan dan kanshin abin tulun ya mugun bashi sha.awa da tsaftar kayan , a ransa yake fadin kenan talauci baya hana tsafta ko wadatar fuska da fara.a

Haka ya kali Wujdane yayi mata alamar da su tafi ko?
Ta kuwa yi kicin kicin da fuska da niyar magiyar ya barta aman sai ya fita hade fuskar sannan kasa kasa ya ce" bakya so gobe na maido ki ne?

Shiru ta yi ta mike tana cewa inna zasu juya

Inna ta fito ta shiga yi masu adu.a da godiya sosai cike da fara.a, ta yi godiyar sakon Mom sannan ta ga dai ya ajiye envelope ta so tambatar meye aman har ya fice sai Wujdane ta dan tsaya suka dan zabta da innarta kan kara hakuri da biyaya a gidan aurenta sannan ta fice bata samu gannin malan ko yayunta ba

Maimakun ya dauki hanyar gidan Mom da su sai ta ga ya canza hanya, aman bata ce da shi komai ba har suka iso anguwar su ELHAJ Muhammad ya ja ya tsaya can gefe wajen sa yakan tsaya idan ya zo shi kadai ya tsurawa kofofin ido yana kalo itama haka dan bata san infa suka zo ba
Chapter 11 · 0% Book details