Sashe 19
Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Baci take na mamaki, tun bayan salar asubah aunty shafa wace ta kwana a gidan ta bata kari da kwayar maganin baci daya ta sha hakan ya bata damar rama bacin da ta jima bata yi ba dalilin tunani
Bacinta take hankali konce saman lalausan gadonta da rufar bargonta mai laushi cike da dadadan mafarkai
Wasa wasa sai da ta kai salar la.asar tana baci
Mom da Aunty Shafa da Inna wace Mom da kanta ta je dan ta yarda ta zo ta kara yiwa yarta adu.a suna dan zantawa, duda bata fiya yin magana a zancen ba aman ta bayar da hankalinta kansu can kasan zuciyarta kuwa tana mamakin bacinnan ma Wujdane sannan ta cika da mamakin yanda ake shirye shiryen tarewar wujdane din a gidan mijinta hakan ya kara kontar mata da hankalinta ta saki jiki tayi amanar yarta ta samu karbuwa
Mom ta kali aunty Shafa ta ce" shafana ki dubo min yarinyana plz, bacinnan bai isa haka ba kuwa?
Aunty shafa ta mike tana murmushi ta ce" aunty ai tayi bacin yana da kyau, bara na koma na gano
Tana tura dakin ta tarar Wujdane saman salaya ta gama salolinta tana karanta alkur.ani cikin zazakar muryarta sannan idannuwanta cike da hawaye
Murmushi tayi a ranta tana ayana baiwar Allah du a tsorace take zata yi nisa da gida
Bayin ta shiga bayan ta dauko yan jarkoki na hade haden da tayi na wannan rana, ta koma bayin ta tara ruwan wanka masu dumi sosai har suna hayaki dan itacen da za.a zuba a cikinsu su dahu, ta rufe wajen gudar ruwan ta dawo
Wani inji inji ne, wanda ake saka mutun sai kansa kadai a waje aka sakata a ciki, hayakin siracinsa na dukan jikinta har kasanta domin zindir take dake cikin wanda ke watso hayakin mai kanshin lemun da aka yanyanka a cikin ruwan hakan ya saka jikin ya dauki kanshin lemun da kuma santsi na mamaki
Idannuwanta take rufewa dan zafin wannan siraci har aka gama ta fito da tawul dinta ta shiga bayin ta shige ruwan zafin bisa umarnin aunty shafa
Har dan ihu take na azabar zafinsaduda ya mugun huce aman fatar jikinta ta dawo tamkar ta jariri hakan ya saka kadan ta ji wuya tana ficewa a hayacinta
Bata gama tantance abinda take ciki ba aunty shafa ta shigo bayin ta hade rai danma karta ce zata fice a ruwan ta shiga kunce rufkar da ta yiwa gashin kanta ta dauko sabulun wanke kan mai hade hade sai kanshi yake ta shiga wanke mata kan nata da shi sosai har tana lumshe ido dan tunda ta fara yi mata gyaran jikin rabonta da kanta ya samu ruwa
Ba su su fito a bayin nan ba sai da suka kusan dauke minti talatin
Wujdane ce a gaba da labcecen tawul dinta, Aunty a bayanta dauke da kaskon turaran wuta da tayi mata turaran tsuguno
Suna fitowa aunty ta jawo wani lakadeden bargo ta sakata tsayawa ta kara wara kafafuwanta ta saka mata turaren jiki mai sanyin kanshi wanda ta rufe mata har kanta da damshin ruwan wankan nan a jikinta turaren nan ya bigeta sosai har sai da ta dawo ta gaji da tsayuwar kafin Aunty ta bude mata rufar
Ya salam kawai nake iya furtawa domin fatar Wujdane yanda ka san fatar jariri sabon haihuwa haka take daukan ido da haskawa, idan ka latsa kuwa sai kayi zaton jini zai biyo yatsar naka
Kanta a sade tana dan yamutsa fuska na an dameta gashinta ya bazo ya kare fuskar nata aman ya dan saka duhu a hasken nan nasa dalilin turarukan da yake sha na gyaran gashi da mayuka kala daban daban
Zama ta yi a bakin bed ta karbi abincin da aka miko mata ta shiga ci cikin nutsuwa nan aunty ta fice dan ta shigo da mai mak up din da aka kirawo da su Mom
Abincinta take ci hankalinta konce duda yanda take ji gabanta na dan faduwa, sai ruwan garaigarai da dafafen sasaken baure da mazarkwaila da sauransu da aka dafa mata tana dan kurba a haka aka turo kofar suka shigo
Dago da kanta ta yi jin muryar Mom sai idannuwanta suka sauka a kan Mom da innarta
Wangale baki ta yi tana murna ta ce" Lah innata,
Sannan ta bi shigar innar nata da kalo, dinkin bugagiyar atamfa ne ta sha wuyanta da sarka da yan kunaye da awarwaro masu shegen kyau, kai harta innar tata sai ta ga ta dawo wata fresh🤣
Zama suka yi ai kuwa ta shige tsakiyarsu ake ta labari, innar kanta ta tsorata da yanda kyan Wujdane ke daukaka da wani kwarjini da take fitarwa, sai tayi hamdallah a can kasan zuciyarta ta godewa Allah da kuma iyalan Aba
Sai bayan sun gama salar magariba mai mak up dinnan ta dan gyarawa Wujdane fuska , ba wani makup ne ta yi mata ta cika mata fuska ba, an dai gyara mata girarta an saka mata dan jan baki kalar kasa mai man lebe sai kwali da aka daidaita aka bi mata a idannuwanta
Gashin kanta aka shiga gyarawa, coiffure ne aka yi da shi inda ta dunkule shi a tsakiyar kan ya bayar da kala ya mugun fito da fuskar yayi mata kyau sosai
Ana tsaka da kimtsata Aisha ta karaso sai matar Anwar itama da yaranta sai wata datijuwa makociyarsu itama tana falo
Lafaya ne irin na larabawa kalar ja mai ratsin fari sai duwatsu masu kyalkyali birjik da suke haskakata aka fitar, irin sababin bugowar nan ne na dubai
Wani yan kunaye ne siraru masu dan tsayi na gwal aka daka mata, su kadai ba.a saka mata sarka ba ba.a saka mata wasu awarwaraye ba
Bra fara kar aunty Shafa ta bata da pant shima fari kar wa.inda suke zubar da kanshi inda Wujdane ta labe ta saka tana ta sine kai dan su duba kin fita suka yi sun saka ta a gaba
Doguwar riga mai siririn hanu mai santsi mai bin jiki fara kar mai shigen rigar baci ne aka bata ta saka wace za.a yana lafayar a sama,
Rigar sai ta bi jikinta ta lafe sosai ta fitar da ainahin kirar jikinta wace ko mace sai tayi mata kalo biyu dan karya ne ki yi mata daya ki kawar da kanki sai kin kuma ko dan ki tantance sannan ki sarawa ubangijin da ya halici halitar nan
AUNTY shafa ta gyara mata ta yi mata daurin dama, aka rufe mata har kanta,
Aisha dake dauka da katuwar wayarta android iPhone7, wani irin shauki da murna sun cika mata zuciyarta su Auntu da Matar anwar suka shiga yi mata wanka da ruwan turare bayan wanda ke jikin tufafinta da fatar jikinta (kun san du yawan turare baya saka amarya mura koda mai huka ce baya tashi wannan nice kat),
Kanta a sade, ta kasa tsayar da hawayen dake ziraro mata daga idannuwanta a lokacin da aka tsugunar da ita a gaban iyayenta, wato mahaifiyarta da mahaifiyar mijinta wa.inda su kansu zuciyarsu ta karaya sun kasa wani kwakwaran motsi
Wujdane ji take yaune za.a rabata da gidan iyaye, wannan rabawar da za.a yi mata ita tafi daga mata hankali domin ta farko bata wani damu ba, aman a wannan ji take tamkar ba zata kuma ganninsu ba sosai take jin tashin hankali na rabuwa da iyayenta
Mom ta yi gyaran murya a hankali ta ce" y.ata, a zaman da nayi da ke baki taba bata min ba, kin kawo min haske a cikin gidana, kin sha shayar da ni mamaki, Wujdane ina jinki a raina tamkar yar da nayi ta nema ban samu ba sai gaki Allah ya bani, ki rike jawaban da auntynku tayi ta yi maki ki rike hakuri sosai Wujdane, Allah yayi maki albarka sannan ki yafe min nima kin ji?
Ai kuwa wujdane har kankame hannayenta take dan kuka, kukanta take sha harda haki, inda suka bi inna da tayi mata jawabi
Inna ta saki murmushin karfin hali ita kam daman basu kawota ba dai take ji tamkar zata kara rabuwa ne da Wujdane,
Ajiyar zuciya ta kuma saki ta ce" Mai zan ce? Ai hajiya kun gama yiwa Wujdane fada kun fada mata komai, ni Wujdane abinda zan kara fada maki shine *ki rike mijinki, ki bi mijinki, ki yi masa biyaya Wujdane , ko mai zaki zama a gidan duniya ke Wujdane koda shugabar kasa zaki zama karki yarda karki amince ki daga muryarki sama da ta mijinki, ke ba kowa bace sai darajar da ya luluba maki, ke ba komai bace idan ba shi, kyau kuwa da kuruciya masu gushewa ne, ki rike masa mutuncinsa ki kare masa hakinsa, daman ban sanki da kawaye ba karki yarda ki fara ki rike kafafuwanki a duk inda yayi maki umarni da zama, ki kasance mai yi masa godiya da girmama shi* Allah ya yi maku albarka
Sosai suke dan share hawaye har Aunty ta samu ta mikar da ita suka kamota suka nufi bangaren Aba wanda yayi mata nasiha daga shi sai ita yayi tayi mata godiyar da ta rasa inda zata tsoma ranta dan kunya ya salameta suka fito
Dankareriyar mota ce fara kar, sabuwar limousine, mai tafi da gidanka mai bakin gilas, nan aka shiga da amarya inda Anwar ne direban sai gayar da yayi na abokansa sojoji da yan anguwar suka layu da motocinsu aka saka ta amaryar a tsakiya ake tafe a hankali
A haka suka shigo gidan su ba tare da sun san har an karaso ba dan tafe take kamar bata tafiya
Abin mamaki shiru kake ji sai ma.aikatan dake dan kai kawo sai tsuntsaye dake karansu
A hankali aka fitar da Wujdane daga motar, gaba dayanta a jikin Aunty take tana sakin ajiyar zuciya tana biya karatun dake dan tashi a wayar aisha wace ta sako bakara dan samun nutsuwar wajen