← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba su su bar gidan ba sai bayan salar isha.i, a yau dinma wata maganar kirki bata hada shi da Wujdane ba, ko gaisuwa bata hada su domin ita tana gannin ita ce mace, komai talaucinta komai irin auren da aka yi masu shi ya dace ya fara yi mata magana kafin take saukowa, shi kuwa yana gannin fitsarar tata tayi yawan da tana kallo kowa na gaishe shi ko ana tsoron yin wani abin idan yana nan aman ita bata wani damu ba ya zuba mata ido yaga iya inda girman kan nata ya kai ne?

Bayan anyi adu.ar bakwai a kulun Mom zata yi iya rarashi dan Aba ya amince su tafi gida koda ita ce zata shiga shi ya tsaya a kofa sai ya nuna sam bai san zancen ba wannan abin na damunta sosai cikin ranta sannan tana yawan yiwa kanta tambayar shin mai yake kai Alaidine ne? Ko ya daina fushin da su?????

Alaidine kuwa wajen satinsa biyu rabonsa da gidan, yana dai yawan haduwa da abansa yana kuma kiran Mom dinsa, ba dan komai ya kuma dauke kafarsa a gidansu ba sai dan ya sakawa kansa tsari, yana tsoron abinda zuciyarsa ke bijiro masa sosai yana mugun tsoron irin abinda ke kokarin tarwatsa tunaninsa yana jin haushin kansa da na Jamail domin da bai dauko maganar yarinyar nan ba da bata shigo gidansu ba da baima santa a rayuwa ba

Shirye shiryen tarewar Aisha Mom take sosai wanda du wani abu mai mahinmanci idan aka yiwa Aisha sai an yiwa Wujdane, ita abubuwan shan birgeta ma suke dan irin zakinsu sai kawai ta daina wani kula abinci koda yaushe tana didikar tsumi

Mom da kanta ke shafe su da madara peak sai ta bushe a jikinsu a wanke da ruwa mai dumi dumi sannan da dare a kuma hada na kwai a shafa masu da lemun tsami, haka fatarsu ke haske da santsi saima ta wujdane dama da santsinta sai abin ya karu sosai

Fannin turaren wuta da na kulakca ba.a kama hannun yaro, Mom mutun ce mai son kulawa da jikinta hakan ya sa ta iya hade haden turaruka masu mahinmanci ga jikin mata, sosai ta koya masu zama cikin kanshi wanda ya zame masu jiki

Jamail idan ya zo gidan nan yakan cika da mamakin yannayin aisha, gashi ta koyi wata kisa ta karfi da yaji ko magana za.a yi masa kalarta daban da yanda za.a yiwa wani, hakan na ruda shi yana bannin mom an gama gyara ta bashi matarsa mana?
Hajiya Wujdane dama ba gwanar yawan magana ba, sai hakan ya hadu ya hade mata biyu ya kasance kamar da gangan take yin wasu abubuwan, wato sai kace wada aka sakata a makarantar koyon yanga da jan aji sannan abin yana hawanta sosai

Gashinta tun ranta na kiyawa idan Mom tayi kiransu kan gyaran gashi har ya zame mata jiki, ita da kanta take zuwa ta zauna mom ta gyara mata tas sai bulbulan kanshi yake ta zo abinta, sannan Mom ta kwadaita mata yi masa ado kala daban daban ta fannin nuna mata a tv tashar larabawa da indiyawa masu kalar gashinta ta hana ta saka yambo

Ido ne Mom ta kawo ta sakawa alaidine, jiran ranar da zata ga ya shigo gidan take sannan sam bata taba kawo masa maganar matarsa ba, tana jiran shi ya yi mata magana ne

Yau ta kama alhamis, sauran kwana biyu kawai Aisha ta tare a gidanta, tunda safe direba ya kawo su gida

Inna ta sha mamakin yayan nata, gaba daya sun canza mata, sai yannayin nutsuwar Wujdane harma ta fara tunanin ko ta daina fada?????

Sun kusan wuni da mahaifiyarsu da mahaifinsu da yan uwansu, sosai inna ta kara yi masu nasiha na zaman duniya,
Da zasu tafi kamar su yi kuka haka suka juya suka tafi ransu a bace ba dan sun so ba (Uwa mai dadi)

Zaune take a guarding tunda suka dawo tayi tsai tana kallon tsuntsaye na shawagi a filin

Ba wata salama ba sanar da isowa khadija ta zauna face dinta , ta ce" kina nan kina faman amsar shirye shiryen amare bayan baki ma san wa kika aura ba? Baki ma san wanene asalin Alaidine ba????

Dago da kanta ta yi, a duniya tana maraba da ranar da zata nunawa wannan mata ta fita iya rashin mutunci aman tana adanna ranar nan, mikewa ta yi da nufin barin mata wajen sai dai mai, abinda kunnenta ya jiyo mata ya tayar mata da hankali, ya firgitata, bata san lokacin da ta juyo da mugun firgici ba da muradin jin maimaicin kalmar da Khadija ta fada wada ta kunshi harufa biyar kawai aman ta tara dukan tashin hankalin duniyar, kalmar da idan har haka ne tana da ja da wannan aure, kalmar da idan dai haka ne tabas zata daina gannin girman matar gidan dama dukan wanda ya rabu gidan...................
[2/1, 2:29 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*29*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Yannayin yanda Wujdane ta shiga lokaci guda sai ya baka mamaki, cike da tsoro ta ce' aman Khadija kin san girman furucinki kuwa? Kin san irin tarin tashin hankalin furucinki kuwa?

Khadija ta kada kai ta ce" komai girmansa idan gaskiya ya kunsa ai ba damuwa ana iya furta shi koda a gaban sarki ne

A hankali Wujdane ta kai kasa zaune, tunani ne barkatai a kwakwaluwarta,

Gannin irin yanda take tasiri a Wujdane ya sakata gyara zama ta shiga fayacewa Wujdane cewa" *MIJINKI DA KIKE MURNAR AN AURA MAKI HAR KIKE WANI RAWAR KAI SHEGE NE, SIRRI NE DA AKE BOYEWA YAYAN MUTANE HAR SAI SUN JI SUN BAYANA BACIN RANSU SAI YA SAKE SU YA MAYAR DA SU KANANUWAN ZAWARAWA*

Kina nufin shine dalilin sakin mata da yake??? Sannan daman ba su Mom ne iyayensa ba? Cewar Wujdane

Sune kam, su suka haife shi, Mom dai da Aba, bakya mamakin ana zaman makokin mutumin da mu bamu ma san shi ba? Toh a gidannan Mom da Aba kawai suka sanshi, dan uwan Aban ne, tun lokacin da suka tafka abin kunyarsu family dinsu suka cire su a sahun yan gidan, ya kasance sun kore su kwata kwata, yanzu zaman da suke yawancin jama.a kallonsu kawai suke domin ba wani yarda aka yi da a yanzun ma zaman aure ne ya hada su ba, mai yiwuwa sauran yayan ma hakan ne wato *SHEGU* ne

Tamkar ta watsa mata barkono haka take ji, gaba daya duniyar tayi mata zafi, zuciya da ba kashi ba har zuciyarta ta karaya, a hankali ta mike tana langi ta nufi falo, direct wajen Aisha ta nufa wato dakinta

Tana zuwa ta zube jikin Aishar dake konce tana waya da Jamail

Firgigit ta mike tana kalonta, tsoron yannayin da take ciki ya firgita Aisha, cike da tashin hankali ta kashe wayar ta kamo hannunta tana aikin tambayarta lafiya?

Wujdane dai bata yi wani kuka ba, sannan bata bude kwayar idannuwanta ba saima yamutsa hannunta da take a cikin gashinta, a hankali ta ce" ni abinda nake son sani a nan shine, Malan ya sani? Idan kuwa Malan ya sani toh tabas zaman halal suke, toh aman kadara ce? Ina mai rokon Allah hakan ya kasance kadara a kansa, ace daga kansa basu kara wani ba, ina cike da zulumin abinda na tsinta a yau

Aisha kanta ya shiga duhu, zama ta yi sosai tana fuskantar Wujdane, tausayin yayar tata ya cika mata zuciya, ace a rayuwa mutun damuwa na damunsa aman baya iya kuka? Cike da muryar lalashi ta ce" ki fadan damuwarki Aunty plz

Sai da Wujdane ta sauke ajiyar zuciya ta labartawa Aisha abinda ya faru,

Ita kanta ta kadu da jin wannan baban furucin, tabas wata maganar zata kasance gaskiya koda watar bata kasance gaskiyar ba,
Waje ta samu ta zauna gefen Wujdane, hannunta ta kamo ta rike tana kallonta, ta jima a haka kafin ta ce" aunty, ni kuwa sai nake gannin kamar kin yi saurin karaya a irin hare haren da za.a iya kawo maki

Wujdane ta ce" mai kike nufi?

Aisha ta nisa ta ce" Aunty shin kin manta wacece Khadija a wajen aban Boy? Khadija ita ce matarsa da suka zauna zaman aure, wace suka samu karuwa da shi, rabuwa ta gita ta dawo zama a cikin gidan iyayensa, wa.inda suka yi mata rana suka ki bari ta wulakanta kamar yanda mahaifinta ya koreta, suka karbeta suke ciyar da ita suna shayar da ita suna tufatar da ita, take zaune taki kula kowane namiji tana jiran wannan bawa da ta sheganta a yanzu harma ta sheganta iyayensa ya dawo ya aureta, shin aunty wannan bai saka kin dasa ayar tambaya ba?

Kallonta take cike da mamakin Aishar, sarai sai yanzu ta shiga yiwa kanta tamabayoyin irin haka, duda hakanan ta kaleta ta ce" kina nufin karya tayi kenan da ta sheganta shi?

Aunty idan shegen nema shi sai me? Aunty a yau yannayin rayuwar gidannan zaki duba ki yarda cewa akoy tarbiya, akoy girmama juna da gannin mutuncin juna, aunty yau koda mijinki, wanda mahaifinmu ya zaba maki ya kasance shege ya zaki yi bayan ki karbe shi ki rungume shi , aunty koda shine mai tara shegun kina gannin kinada yanda zaki yi bayan adu.a da neman Allah subahanahu wata allah ya shirya? Ni na tabata koda sunnan da ta kieayeshi da shi hakane aunty kadara ce zata fadawa su Aban wanda mu din nan kai har mahaifiyarmu bata fi karfin Allah ya jarabceta da hakan ba, na san abin da tsoratarwa irin yanda ta baki labarin, aman aunty kin san wani abu? Yau koda harda yaya Jamail a haka ko, wly a lokacin zan rungumi abinna, dan nayi imanin nima ban fi karfin Allah ya jarabceni da hakan ba, sosai na yi mamakin yanda kika fada a tarkon wannan da kika zauna da ita kika ganne nufinta ta fitar da ke ne ita ta shiga aunty
Chapter 3 · 0% Book details