Sashe 4
Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba daya jikin Wujdane yayi sanyi, wani sabon tunani nema ya darsu a zuciyarta, a can kasan ranta take ayana tabas ita yanzu nema ta ji ya fara birge ta, domin idan har haka ne rayuwarsu kusan iri daya ce, shi ana takura masa ana zaginsa dan kadara ta kasance a kansa, ita kuwa jama.a sun mayar da ita aljannah dan halitarta,
A hankali take hasasoshi a idannuwanta, ita kadai murmuahi ya kubce mata da ta tuna musanyar hararan da suke shi da ita
Nan ta zauna tana tsara abubuwan da ita kadai ta barwa ranta
Mom ce ta turo ta shigo dakin nasu da salama
A tare suka amsa mata suna kalonta
Mom ta ce" dakin naki na je bakya nan sai nace kawai kina nan, tashi ki shirya mi tafi wajen mijinki ashe a konce yake ba lafiya, tana gama fada ta juya ta fice a dakin
Tsai Wujdane ta yi bayan ta fito a wanka tana kalon kayan da Aisha ta fitar mata, Lesh ne kalar tsanwa ruwan shukoki da ratsin farifari a jikinsa, sai mayafi fari kar mai duwatsu sai takalmi mai dan tudu da sarka da dan kunaye masu kyan gaske
Da ido take binta, ta shiga gyara mata gashinta ta daure shi a tsakiya ta hade shi waje guda
Fuskar Wujdane ta gyara mata dan daidai ba wani makup bane, girarta ta bi da ja gira maroon sai gashin idannuwanta da ta caje mata da maskara sai dan jan baki ta dan goga mata kadan,
Wujdane bata yi yunkurin hanata ba, domin itama ta yi kudurta fara gabatar da nata kuduri,
Riga da sket ne, suka bi jikinta luf sket din ya kamata sosai ya fitar da kirar jikinta haka rigar irin mai babar wuyan nan ce sai kuma hannayen na salak ne
Bayan ta gama shiryawa Aisha ta kashe mata daurin dan kwali wanda ta dan ja shi baya kadan daga gaba ya fitar da kontacen gashin kanta sannan dunkulelen ya fito a tsakiya
Nan ne Wujdane tace aa, gaskiya a rufe mata ko.ina aman Aisha ta dage da magiyar dan Allah karta taba
Tafe take takalmin kafarta na bada dan kara kwas kwas kwas suka sauko da Aisha
Mom ce zaune da Khadija sai labari Khadijar ke bata
Gaban Khadija sai da ya yanke ya fadi tayi gagawar kawar da kanta a kallon Wujdane tana jin kanta ta muzanta, Mom kanta sai da ta yi mata adu.a a kasan zuciyarta
Mikewa Mom ta yi, suka yi daga da Aisha wace ta saka hijabinta dan ta raka su itama, Wujdane na karshe
Har zata fita ta dakata ta dawo wajen Khadija ta ce" ji mana
Khadija ta dago tana kallonta, Wujdane ta ci gaba" dole na gode maki, domin kin taimake ni sosai, na so tafka asara na kin karbar mijina a tafin hannuna , aman a yau maganar da kika fada min ta ainahin shi din wanene sai na ji du duniyar nan bani da wanda zuciyata ta aminta da shi da na so shi irin *Alaidine* wato ni wujdane koda Alaidine aljani ne ina sonsa 🤪
Nafa yi yaji gaskiya, na yi yaji kila wa kala zan kamala 😏🙄🙄🙄🙄🙄, ance ❤😍 kadai nake da muradi? Ga na yau byby
[2/1, 2:29 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*30*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
I.m sorry plz wly biki muke
Jansu direba ke yi sun yi shiru , Aisha ce a gaba Mom da Wujdane a baya,
Tunani ne fal cikin zuciyar Wujdane na yanda zatana rama abubuwan da suke yi mata daga matar Alaidine har tsohuwar matarsa da shi din kansa,
Wani murmushi ne ya subuce mata da ta tuna yanda fuskar khadija ta nuna firgici da kalamanta, ita kanta sai da ta ji maganar da ta fada wani banbarakwai da ita wai tana son Alaidine,
Zata buga kwalon da suke bugawa ne, zata yi kokarin yin gem din, domin ta lura zama ne ake marar tsari, daga baya idan hankalin su innarta ya konta ta nemi sakinta a sawaka mata da irin rayuwar nan dan kuwa ita tun tana karama bata muradin cudanya da masu hannu da shuni dan ta rigaya ta hade su cewar basa kyautatawa talakawa basa mutunta talakawa
A haka suka karaso gidan Alaidine,
Ba aisha ba ita kanta sai da ta firgita, gaba daya ginnin irin ginnin nan ne na tsakiya shi ba a kasa ba shi ba a can sama ba, ana kiran gidan ne da gidan glasss, domin du rabin gidan glass ne, ta ko.ina kana iya kallon kanka dan kuwa ma.aikatan gidan suna yin aikinsu
Mom ce a gaba sai su Wujdane na biye da ita,
Jamail ne ya fito da gajeran wandonsa zai je gudu wajen motsa jiki na cikin gidan
Da murmushinsa ya nufo su yana mai murnar ganninsu harda Aisharsa,
Da Aisha da Wujdane gaba dayansu juya bayansu suka yi cike da tsoron ganninsa a haka domin kuwa su dai tunda suke basu taba gannin namiji baba haka da irin shigar nan, (zaku fada ne)
Murmushi Mom ta yi, ta ce" ka ga malan tafi ka saka sutura mana ka sakan yayana jin kunyarka a haka
Shima murmushin ya saki ya miko hannunsa wajen Aisha ya ce" madame zo mu tafi bangarena kafin su fito ko?
Ai da sauri Aisha ta labe a bayan Mom harda rike hijabinta gam kamar wani dodo zai kamata
Dariya yake sosai, ya koma bangarensa, a ransa shi dai yannayin tarbiyarsu na bashi sha.awa,
Da kalo Alawiya ta bi shi, yana daria ta shiga tambayar kanta shi kuwa wannan dariyar menene yake haka?
Kafin ta samu amsar tambayarta sai ga su mom din sun shigo gaba dayansu bayan sun yi salama
Da ido kawai take binsu, irin kallon nan na an takura maka, wanda ya kashe su Wujdane da mamaki, wai mahaifiyar mijinka ne zata yi salama ka yi mata shiru, ta shigo ciki ka bita da kallon raini haka?
Aa ya zaku shigo min gida har ku zarto min falo haka ba wani salama ba komai idan fa kuka tarar da abinda yafi kallon idannuwanku bayan kun san cikin gidana ne hakan na iya faruwa? Kamar an matseta ta shiga sakin zancen nan tana kallon Su Wujdane wato da su take banda Mom a tunaninta,
Mom ta kada kai, bata ce da ita komai ba domin sam ta lura yarinyar bata da girmama mutane, sannan ai ta san sarai wscece Wujdane, idanma ta nuna an takura mata da zuwa gida ai yanzu gidan ba na ita kadai bane
Wujdane wani malalacin murmushi ne ta sakar mata, bata da niyar tanka mata domin a gaban Mom suke, bata da niyar bata amsa a yanzu har sai ta karanci kalar nata rashin da.ar,
Bayan Mom suka bi wace ta umarce su da hakan suka kama haurawa samA
Da wata muguwar harara ta raka su, itama ta aniyar binsu saman wato bangaren Alaidine
A nanma sun wanke isannuwansu da kallo , a falonsa yake, yana kwonce nan kasa saman capet din dakin mai ruwan ash color da bakibaki a jikin mai gashin mage
Jikin dogon wando ne baki, irin na costume sai yar riga fara mai siririn hannu wace ta bayanar mai da damtsen hannunsa da rabi rabin fafadan kirjinsa <karku manta readers irin yanda Alaidine yake motsa jikinsa a rayuwa domin ya mayar da hakan tamkar abin dauke masa kewa da sakawa ya manta damuwarsa>, idan ka ganshi ba irin shigar nan sai ka sha mamakin irin yanda jikinsa yake
Gefensa Boy ne da dan wandonsa ba riga yana ta bacinsa hankali konce
Salamar Mom ce ta saka shi kokarin zaunawa yana amsa mata sannan ya mayar da hankalinsa kan kofar dan gannin Mom dinsa
Maimakun Mom ta fara shigowa sai ta umarci Wujdane da ta fara shiga (tun farko Alawiya, rashin girmama girman mijinta da na sarakuwarta ya saka har Mom idan ta zo takan takawa da kanta ta haura wajen danta, a yau kuwa ta ja tunga ta tsaya ta tura Wujdane ne dan abubuwa biyu, na farko dai ta nunawa Alawiya dake tare da su irin kusanci mata da miji wanda a lokacin da yaronka yayi aure ya dace du wani abin da ya,shafe shi kafin kowa ya shiga ke matarsa kece farko, domin a yanzu a yannayin nan mai yiwuwa suturar jikinsa bai dace su shiga su tarar da shi a hakan ba, sai abu na gaba tana son shakuwa ta shiga tsakanin Wujdane da Alaidine ne)
Fuska ta daure ta tsaya kan kofar danma kar Alawiyar ta shiga, domin a da can bata nuna damuwarta da hakan sai yanzu dan neman izgili
A hankali ta tura kofar ta shiga da salama a bakinta,
Dan dakatawa ta yi tana neman wanda ya amsa masu salamar sai dai bata ganshi ba domin sam bata kawo a ranta cewar zai konta a capet ba
Juyawa ta yi ta duka ta bayar da kanta wajen kofa dan cire takalmin kafarta mai yar igiya siririya,
Sai da ta gama cirewar ta mike a hankali ta juyo ta fara dan takawa tana mai kuma yin salama ta nufi capet dan ta zauna a tunaninta ko wani wajen ya shige ne?
Kallonta kawai yake, a kasan zuciyarsa yana aiyana ta faru ta kare, wato ya guje mata dan kar ya ganta , yana jinyar fitsarariyar zuciyarsa yayi ya warke ya koma sabgogin gabansa sai gata ta zo wajensa, sannan ita fitinana harda juyawa ta nuno masa duwaiya dan ya ga tana da su(a tunaninka🤔😱?), shi a yau din nan, yarinyar nan ta gama firgita shi sannan ta bashi tsoro a lokacin da yake jin zuciyarsa na samun nutsuwa da alama daman itace damuwarsa wace take dauke masa baci yayi ta tunani a kan rayuwarta, wanda dalilin hakan ya je gidansu ya fi a kirga dan kawai ya san wacece ita? Me ta tagaza mai karfi haka da yake wargaza shi a hankali hankali?