← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 26

Sashe 2

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Boy yayi dariya abinsa, cokalin karshe ne ta debo a hannunta sai Boy ya karbe ya kai bakinta da niyar ta sha

Wujdane ta dan kawar da kai tana nunin ta koshi,

Firr Boy ya kiya yana neman fara yi masu balebale a dole ta dan buda bakinta ya lasa mata madarar , sauran da ta rage a cikin cokalin ya nufo bakin mahaifinsa da ita

Ido Alaidine ya dan zaro, sauran bakinta ne Boy yake son sai ya sha? Shi mai ma ya tsayar da shi a wajen su ne? Shi ko ruwa ka sha ka rage baya sha dan mugun kyankyani, a rayuwarsa ko sauran bakin boy baya sha bale na wani, baya hada cokali, ko kofofin shan ruwansa ba.a tabawa dan baya hadawa da na kowa, sai gashi abinda ya cusawa Wujdane a baki ya ciro da yawunta a jiki Boy zai saka shi sha???

Da yannayin yiwa yaro dabara ya ce" Boy, u see bana iya sha yanzu, ka ajiye min ko ka bawa auntynka ni sai ka bani tomorrow ohk????

Kwabe fuska yaron yayi, niyarsa ya kwala ihun kukan domin har idannuwansa sun cika da kwala

Da sauri ya kai hannunsa wajen cokalin na hannun Boy dan kokarin sakinsa yakeya zube sai dai a rashin sa.a ya ji ya dora saman hannun Wujdane wace itama ta kawo da niyar tarewar kar ya zube mata a jikin hijab
A tare suka kali junna wanda a yauma abinda suka tsinta cikin kallon junna kennan, faduwar gaba... da sauri ya cire idannuwansa a kallonta ya yi gagawar kai cokalin bakinsa ya shanye yar madarar ya mike ya dauki Boy ya fada falo da sauri har yana dan waiwayen kofar dakin

A hankali take janye kafafuwanta daga mikewan da ta yi,

Matar Anwar ta saki murmushi, a fili ta ce" yanzu na yarda da maganar yayana(Anwar)

Juyowa Wujdane ta yi tana kalonta da neman karin bayani,
Ta maida hankalinta wajen Aisha ta ce" kanwata, ya zamu yi mu raba amaryar oga da miskilanci mu koya mata yawan magana ko zata kara damke mana oga???

Gaba daya kalonta suke kawai, domin dai ba abinda suka fahimta,
Ta ci gaba da fadin" idan ana irin haka na tabata akoy ranar da zai kasa rike nasa sarautar, aman fa sai ta fara zubar da nata, matsalar a nan ita ce shin ana iya raba mutun da yannayin halitarsa?

Aisha ta yi murmushi, ita kanta yannayinsu ya birge ta duda su suna kusa sosai suna jin du abinda ke faruwa sun san ba soyaya bane, aman na nesa ko kashe shi zaka yi ya ga wannan yannayin ba zai taba lamuntar cewar wai ba wata aba wai ita soyaya a tsakaninsu, sai maganar canza yannayin Wujdane
AISHA ta nisa ta ce" toh kin san ana cewa ba abinda baya yiwuwa, aman abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, sai dai a gwada a ganni mai yiwuwa a dace

Matar Anwar ta gyara zamanta ta ce" shin kun san wanene Alaidine kuwa? Yaya Alaidine ni dai a kusa kusan nan ban taba cin karo da mai irin halayensa ba, ai shi mutun ne m........
.
..................nan ta yi ta basu labarin Alaidine, yannayin rayuwarsa da yanda mijinta ke bata labarin irin murdiyarsa, da fannin kyankyaminsa da irin hasashen arzikinsa da yawan sadakarsa da rashin son raininsa da irin yanda yayi ta aure aure aman bata san dalilin rabuwarsa da matan ba, haka ta yi ta basu labari wanda Aisha ta mayar da hankalinta kacokam tana sauraro ita kuwa Wujdane sai ma ta kawar da kai gefe tana kallon tsakar gidan a kasan zuciyarta tana fadin sai me karma ya kula tan

Sosai su Aisha suka dage suna tataunawa kan lamarin wanda Wujdane take jan carbinta , ita ganni take aikin yi ne basu da shi (jama.a mu yiwa kanmu da kyau, Malan liman na baba yake cewa" idan ka mutun malan zaka ga nan da nan an manta da kai, wasu cikin yayanka da kake kokarin tarawa duniyar har adu.a suke Allah ya kar giwa ko sa ci nama, kalilan daga cikinsu zasu yi ta kokarin yi maka adu.a a cikin salarsu da sun mike sun zubar da komai, zaka ga ana tashin hankali kan dukiyar da ka tara, sai ka ga wasu kafin a dauke gawarka ma zasu shiga labarin ankon wurin biki, maza kuwa su fara neman kayan shayi dan abin zama ya same su, dadayku ne ke zulumin idan ka je mai zaka tarar? Basu fi a kirga ba da zasu zubar da hawaye dan tausayinka da tausayin kansu, mahaifanka idan ka girmama su a tsayin rayuwarka zasu yi ta binka da adu.a harma ka ga idan mamanka na wani abin ta dakata tsam ta share hawaye idan ka fado mata a rai, idan ka kasance mai kyauta mai sadaka mai hakuri zaka ga al.umma na yabonka suna binka da adu.a, idan ka gina masalaci ko rijiya ko asibiti na taimako sunnanka na yawo a bakinsu zakai ta samun adu.a, ya Allah ka sa mu dace)

Alaidine na shiga suka yi arba da Alawiya wace tamkar ta fashe, du abinda ya faru tana kallo kyar domin tunda ta zo hankalinta daman na kan Wujdane wace ta mugun tsoratata, bata taba hasasho kamanin wujdane din haka ba, ita bata ma yi tunanin cewar Wujdane din wai wata babar baby ce ba a tunaninta kawai Aban ne da rarume rarumensa ya kwasowa mijinta wata dan kawai a takura mata, a yanzu abinda idannuwanta suka gane mata tsakanin mijinta da Wujdane ya mugun girgiza mata zuciya, ita ba zata manta ranar da ta yi gigin saka cokalinta cikin abincinsa sai barin abincin yayi yana fadan ta saka masa yawu, aman yanzu daga bakin Wujdane din aka fitar da abin aman ya saka a nasa bakin

Yannayinta ya kalla ya kawar da kai ya samu waje ya zauna , Mom ce da Alawiyar da Lami da Khadija sai yaran wajen Anwar a falon

Ba wani hira suke ba ana dai zaunen ne mai jan carbi na yi mai dannan waya na yi yaran kuwa na wasan su

Yana zama aka fara silalewa a hankali sai yayi sauran Mom da Khadija da Alawiya

Boy ya lafe a jikin mahaifinsa yayi lamo abinsa Mom na yi masa magana aman yayi shiru bai motsa ba

Alaidine ya ce" Boy Mom ne fa? Ka je tana kira ko?

Mom ta yi murmushi ta ce" ai yanzu da Wujdane ce da kafin ta nema zai tafi wajenta idan ba ita ba sai Jamail sai ko kai yaro sai kiwiya

*WUJDANE* sunnan da yake ta maimaitawa a kasan zuciyarsa kenan,
Mom ta mike ta nufi kicin tana fadin" bara na samo maka dan abin tabawa

Taba tafiya khadija ta mike itama ta nufi waje daga can baya wajen mahaifiyarta dake hutawa

Alawiya ta ce" aman ni ita wannan din ko daman kuna soyaya da ita ne?

Banza yayi mata dan bata wani nuna da shi take ba, sai da ta kuma kiran sunnansa ta maimaita tambayarta

A hankali ya juya kalonsa waje, wannan lokacin Aisha na kyarawa Wujdane akaifunta na kafa ita kuwa matar anwar tanai mata hira haka kasa kasa ita kuwa tana murmushi,
Murmushinta ya shagala kallo, yana haska mata fuskarta sosai

Tsaki Alawiya ta ja mai zafi tana kallonsa ta ce " wannan wani irin wulakanci ne?

Idannuwansa ya sauke kanta, shi take yiwa tsaki? Rainin nata har ya kai nan? A kasan zuciyarsa ya kudurta abinda zai yi mata dan gobe ko ance ta yi masa tsaki ba zata kwatanta ba, sannan ya yi kokarin farawa tun a lokacin, cike da yannayin cusa haushi ya ce" sai na ga kamar ta cancanci samun soyayar nawa? Suba fa ki ga idan tana murmushi yanda yake kawata fuskarta, komai ta yi yana fido ainahin kyanta da personality dinta, kina gannin yanda take birge mace ma bale ni namiji mai rai da lafiya? Kin san menene? Da ace zan samu soyayar nata ko da kinga yanda ake yi domin da alama ita kudina baya gabanta , da ace yana gabanta da ta yarje ta ci kudin ta ci wulakanci! Please wife ki tayani yakin soyayarta mana? ( aa fa Alaidine, kaja nufin ka fadi haka ne dan ka baiwa Alawiya haushi ko abinda ke kasan zuciyarka kake bayanawa a lokacin da baka shirya ba? 🤣)

Tabas ya kuna Alawiya, ya cusa mata bakin cikin da yafi wanda ta cusa masa, ta yi data sannin yi masa wannan tambaya, ta ji haushin wannan rana gaba daya, tabas ta auri Alaidine ne dan arzikinsa, hakan ya saka ta toshe kunuwanta a irin abubuwan da aka ringa fada mata, ta aure shi take kuwa dangwalar arzikin, aman a yanzu zata iya rantsewa cewar tana jinsa har kasan zuciyarta, tana sonsa Alaidine ba wai kyau da arziki kadai ne ta tara ba aa namijin mazaje ne, gwarzo ne, namiji mai watsa taro ne, a yau ta fito da shi kadai ya isa ta karyar da zuciyar wasu yan matan, shi yasa ko yan gidansu bata son yana anfana ko yana yawan raba, sai dai abin damuwar bata isa ta saka shin ko ta hana shi ba, a tsaye yake yana aikata abinda yaga dama ne, kuma a irin yanda ta san labarinsa na sakin mata sai take gannin wautarsu , yaushe ita zata fada masa kalmar nan da zata rabata da ni.imar nan? Ai sai dai idan ciwon hauka take, yanzu haka ta sani sarai Khadija da taki aure dan kawai ta koma masa ne

Mikewa ta yi ta nufi can ciki, zuciyarta tamkar ta fashe , kuka kawai take bukatar yi ko zata ji sasaucin damuwarta.......
Chapter 2 · 0% Book details