Sashe 16
Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwana wajen hudu yana faman jinyar zuciyarsa,
Alawiya dai bata rage shi da komai ba domin girki, konciyar aure a kulun tana karo lesson din yanda zata tarbeshi duda kafin ya samu nutsuwa da kuka da komai aman hakan take jurewa dan ba idanma da laifin mahaifinsa a yi masa aure toh itama mai yiwuwa dan tana mugun tsoronsa a bed ne ya saka yake yi mata irin jiji da kai din nan hakan ya saka idan dai ya bukata toh zata bada kai bori ya hau du irin wahalar da zata sha kuwa,
tana dan gyara falo da dakinta aman dakinsa bata wani shigama dan a tunaninta ba sai ta gyara ba,
Babar matsalarta, babar damuwar dake damunsa da ita, baban bacin ransa da ita shine irin yanda ko a fuskarta ta kasa boye yanda take adawa da iyayensa da yan uwansa, domin shi ba makaho bane du irin yanda suke dasawa idan maganar zai yi taimako ne, ko sadakar da yake yawan yi, da irin yanda yake yawon taimakon bayin Allah sai ya kasance sai idan Allah ya kwata maka ka tardo shi a farke, ko ka same shi a masalaci sai dai karfin rabo domin idan har ita ka tarar zata shuka maka rashin mutuncin da zaka ji makoshinka ya bushe ne, ita dai idan ba yan gidansu ba toh ba zaya kara kowa ba ciki harda iyayensa tana mugun adawar ya yiwa wani anfani koda na kasar gidansa ne
Yana ankare da irin rayuwarta, shi mutun ne mai son sadaka da taimako sai ya bi koyarwar musulunci yake yin abinsa wato ya bayar da hannun dama ba tare da hannun hagun ya sani ba, abinda idannuwanta suka gani kawai take adawa da shi
Abinda yafi damunsa, yaudai sauran kwana goma Wujdane ta tare rabonsa da ya saka ta a idannuwansa tun ranar da ya fito cikin fushin taki amincewa ya ji dan dumin jikinta duda ya tabata daga hakan ba wani waje zai zarce ba,
Sai yake gannin wani kyamarsa nema take ko har yanzu ita bata jin irin abinda yake ji game da ita, sai yake gannin a irin shakuwar da suka yi, a irin yanda suke nunawa juna kulawa ya dace a ce ta jima da yarda da wannan dan abin wanda yayi imanin shine kawai za yana hada shi da ita, aman cikin ikon Allah sai ta kauce masa ta ki karbarsa wai shi zata yiwa wayo ta tunkuda shi wajen wata ita kennan ba abinda ya dame ta
Ba zai iya taba manta irin yanda tsohon saurayinta ya damko tsintsiyar hannunta, idan bai saba yin hakan ba ba zai taba gigin gwadawa ba duda irin rantse rantsen da yayi ta masa, a yanzu haka ya rage zama da Jamail dan sai zuciyarsa ke fada masa irin haukan soyayar da Jamail ya nunawa wujdane har ta furta masa yayi mata kankanta mai yiwuwa girman nasa ta gani ta yi furucin nan (😳🙄)
Tunanin mai kake dear tun dazu ina baka jus din aman baka ma san ina nan ba?
Muryar Alawiya ta katse masa tunaninsa yayi firgigit ya karbi jus a hannunta ya bi shigarta da kallo ta saka yar bintilar rigarta wace ta dan dara pant dinta ta zauna tana kalonsa tana yaba du kwanan duniya irin yanda fuskarsa ke kara haske (salar asubah a kan lokaci)
Dan murmushi ya dakar mata, ya bude jus din ya kai bakinsa bai ce da ita komai ba ya dan fara sha yana ayana dama Wujdane dinsa ce a haka ya zauna yayi ta kalonta har garin Allah ya waye,
Anya kuwa zai iya kara jan fushin nan?????????
Ranar monday, ya kama sauran kwana uku kawai Wujdane ta tare
Alaidine na zaune a park dinsa yana kallon motocin da suka fito sababi na sabon watan nan yana zaben wa.inda ya dace yayi oda a fara gwadawa da su su gani ko zasu shiga, yana ta karanta yanda makerinsu ya rurubuto masa yanda kowace take
A hankali ya cire hular kansa, ya dan kara gudun ac domin aikin ba karami bane ya cire agogonsa dan ji yake yayi masa nauyi ya kara dan tatare rigarsa ya ci gaba da aikinsa da dan jus da faro a gefe sanyi karai yana dan kurba yana ci gaba da aykinsa
Yar karamar wayarsa kirar samsung fara kar ta kuma daukan tsuwa, wannan wayar masu numberta yan gidansu ne kawai sannan yafi dangata mai kiran da anwar ne dan sunyi maganar zasu kirayi juna aman yayi kira daya biyu bai daga ba ba sai ya hakura ba, cike da jin haushi ya janyo wayar bai duba sunnan ba ya dana ya kara a kunansa da hannunsa na hagu na damar kuwa a kan computer bai yi magana ba
Kana jina kuwa hello????????
Muryar Aba ta farkar da shi da sauri ya dago yana mai yin salama a wayar
Yana bada hankalinsa sosai
Aba ya ce" kana ta aikin naka ko tamkar agogo Elhaj Alaidine sarkin aiki
Alaidine yayi murmushi yana sauraron Dadynsa yana dan shafa kansa kadan kadan alamun yaji kunyar nan
Aba ya ci gaba" gidan nan fa an gama, komai har mun je da Momynku da auntynku sun ga yannayin tsarin gidan dan kayan da zasu kawo, sun nace su sai sun je dubai sayen kayan amaryar aman ni nace aa, domin a yanzu a kano an jima da ci gaba, abinda zasu tarar a dubai din akoyshi a nanma, lokoci ba zai isa su tarki tafiya dubai kafin yarewar ba shine Momynku tace ko a matsa ranar tarewar
Alaidine bai san lokacin da ya ce na.am?? Tun karfinsa ba domin kunnuwansa suka cuce shi bai shirya jin cewa za.a ce a matsa tarewar Wujdane ba bayan baban tashin hankalinsa kenan tayi ta tare ta zo kusa da shi ko zai huta da rashin bacin dare da yawan tunani ba
Aba yayi dan tsam , jin Alaidine yayi shiru ya ce" magana ce?
Alaidine da sauri ya ce" aa Dad ba magana bace
Aba ya ce" toh shine ni kuwa na ga aa, ba zai yiwu ana saka rana ana matsawa ba, a yanzun su tafi su sayo abinda yayi masu idan ya so daga baya sai su kuma zuwa su canzo harda ita dinma ina fatan ba takura
Alaidine ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya ya ce" ba takura ko taya Dad, du yanda aka yanke
Aba yayi murmushi daman ya san ba zai wani tanka ba ya ce" yawa sai ita dayar matar taka, idan ka koma itama ka bata wani abin mai tsoka wanda zai isheta ta canza kayanta harma tayi wani abin ka ji ko? Hakan zai kara wanzar da zaman lafiya a gidanka
Alaidine ya amsa da insha Allah dad
Haka Aba yayi masa salama ya shaidawa Mom yanda ya yanken haka za.a yi kawai
Alaidine ya jima kafin ya dawo a nutsuwarsa, mamaki ne ya kashe shi irin yanda magana ta fito masa bai shirya ba kawai dan an ambaci Wujdane,
Yayi murmushi yana shafa kansa da sajensa da ya tuna nan da kwana uku za.a kawo masa ita su yi zamansu a innuwa daya hankalinsa ya konta ya dawo waje guda
Computersa ya kala ya yiwa baturen nan message cewa su hadu gobe su karasa maganar dan a yanzun komai ya kunce masa wata fitinar son ganninta ne kawai ya mamaye masa zuciya, ga waya aman girman kansa ya hana yayi kiranta idan har ba ita ce ta neme shi ta bashi hakuri kan irin yanda ta nuna halin ko
In kula da shi
Murna Alawiya take tana juyi na chek din da ya miko mata bata ma tsaya ta ji na menene ba
Kudi ne har million biyar da sunnanta da nufin yayi mata kyauta, sai da ta gama juyinta yana kallonta shima da murmushin a fuskarsa dan kuwa du yanda kuke da ita idan kayi mata kyautar kudi zata nuna farin cikinta ne a fili,
Dakatawa tayi ta dare cinyarsa, cike da murna ta ce" husband ni dai ba birthday dina bane, sannan ba lokacin tafiya maka bane bale nayi tunanin guzurin jama.ar da zasu tafi ne aka bani na raba da nawa, aman kyautar nan duka na menene?
Alaidine yayai murmushi ya kara gyara zamansa ta saki jiki sosai a jikinsa tana ta lalubarsa sosai har ya dauko caji, ya ce" an gama ginnin gidan nan ne, wanda zaku tare tare da Wujdane, wannan ina so ki yi abinda kike da bukata idan zaki canza gadajenki ne duda akoy sababi aman sha.aninku na mata, idanma wani abin ne aman banda sutura da mota domin nayi maku odarsu,
Tunda ya fara magana ta dakatar da dokin da take, ranta ya gama bacewa ta mike daga jikin nasa cike da fada ta ce" yanzu daman dan wannan ne har kake wani sakin murmushi? Kenan da gaske ne sai ta zo mun jera kishin da ita? Ita nan har macece banda farin mai zata nuna min? Du irin yanda nake kulawa da kai ina baka hakinka ashe bai isheka ba? Toh da ka bani million biyar ita din matar so fa? Nawa ka bata? Na tabata Abanka zai kara mata ne ko? Ko mai kake
Idannuwansa kawai ya rintse yana mamakin mata, wai bata aike shi ba, bata biyarsa bashi, ba adini ba, dan kawai yayi niyar faranta mata sai ta buda baki ta yayaba masa magangannu haka,
Mikewa yayi da zafin nama ya damko hannunta da ta juya zata bar masa wajen aman bata yar da takardar ba, ya juyota da karfinsa da niyarsa na bata mata rai wayarsa ta ma.aikata ta dauki ruri,
Idannuwansa ya wurga ya ga sunnan john ne wanda suke maganar mota da shi
Bai daga ba , ya juyo wajenta yana kalonta zuciyarsa na bugawa
Hannun nata ya saki ya dauki wayar da sauri ya haura sama dan tuna maganar abansa na idan ransa ya baci yayi shiru ya daina daukan mataki a cikin bacin rai
Alawiya nan ta zube tana kuka itama cike da kishin Wujdane, haka kawai bata son su kasance a waje daya da ita da Wujdane da Alaidine, tana tsoron su kasance a inuwa daya su raba kwana da Wujdane