← Book details Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Bani Da Zabi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idannuwanta ne suka sauka tsai cikin nasa, gabanta sai da ya yanke ya fadi ta yi gagawar juyar da kanta gefe domin idannuwanwa sun sauka tas a kan fafadan kirjinsa dake huci shi kadai

Hannunta ta jimke dan kaduwar da ta yi, a ranta take ayana wai su basu da kunyar zama da kaya irin haka ne?

Cike da rashin kunya ta ce" da Allah malan ka tashi ka saka sutura a jikinka da su Mom a kofa suna jira kar su gaji da zaman jiranka kai kuwa kana wani zaune da wasu kaya sai kace karuwin namiji🙆🏻‍♀😲😳

Alaidine jin magangannun nata yake tamkar a mafarki, tabas ya yarda yau da irin maganar da ake fada cewa mafadaciya ce bata da kunya dan akoy wani saurayi sale da ya tambaya kawai inane gidan su Wujdane,? Ai da ya takarkare ya fara yi masa zuba, domin ta taba wanka masa mari suka dambatu kuma shi yafi shan wahala, ya kara da fadin Wujdane Mama, banda yawo da masifa ma abinda take yi a rayuwa , harda rantsuwar yanzu haka yayi imanin wanda ya aureta ya kwashi masifa ne da kansa domin watarana idan ya yarda ya bata mata rai sai tayi masa lilis dan kowa a anguwar yana fadin tabas aljannu ne da ita masu saka mata karfin doki a jikinta (toh fa)

Murmushi ya tsinci kansa da saki, ya mike a hankali yana takowa kusanta, du taku daya sai ya ayana irin kokarinta na ta kale shi ta tafka masa rashin kunya,

Sai da ya zo daf da ita daga bayanta, yar ficik da ita idan suka jera, aman dan kokari ta iya buda fitsararen bakinta ta yi masa fitsara haka ko ji take Jamail ne?

Wai karuwin namiji, bayan ita ce mai yawo?

Tsahonsa ya rage, ya dora habarsa a daidai wuyanta inda sajensa yayi masauki a wuyanta da gefen fuskarta, a hankali yake dan goga sajen nasa yana shakar wani fitinanen kanshi dake dukan hancinsa , hannunsa a zagaye da jikinta ya riketa aman ba sosai ba

Tsoro ne ya darsun mata lokaci guda jin wani abu na gugan fatar jikinta wanda bata taba jinsa haka tunda aka haifeta ba, da sauri ta kufce ta juyo da karfinta sai dai tana juyowar ta afka a cikin kirjinsa har sai da daurin dan kwalinta ya kufce ya fadi kasa, mayafinta daman ya jima da faduwa gashinta tufkar nan ta warware aman daurin mai kunce ba

A hankali ta furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, A.uzubilahi minna shaidanin rajim

Murmushi ya saki ya sasauta rikon da yayi mata, ai kuwa ta samu bakin magana ta dago kanta ido taf da kwala ta ce" meye wannan ? Me kake yi wannan?

Idannuwansa ya kankance ya ce" karuwancin ne wai zan gwada maki

Wujdane da ido ya raina fata ta janye jikinta a nasa ta ce" ka ga malan ni bana son salon iskancin nan.............

Kafin Wujdane ta karasa maganarta sai jin wani dumi dumi ta yi a lebenta, wanda ta ji shi har cikin bakinta,
Alaidine ne ya cafke bakinta da niyar ya hukunta yanda take kokarin yi masa rashin kunya gatsai gatsai haka , aman maimakun ya hukuntatan sai ya bige da bata wani zazafan kiss, wanda shi kansa bai taba sannin wai idan aka yi kissing din mace ana jin irin abinda yake ji a yanzu ba, bai taba kawowa ransa cewa just kissing zai hargitsa masa tunani ya rikita shi ba sai a yau, hannunsa na rawa ya saka ya talafe kanta , na damar kuwa ya rike bayanta ya matsota sosai jikinsa dan tana wutsil wutsil din kwatar kanta, a hankali ya........

😳😳😳😳😳😳 ku ga du anyi zuru a ji yayi mai🤣🤣🤣🤣, naki din😎🤣🤣🤣

Shin Alaidine na kokarin fice gona da iri ne bayan ko nomata bai soma ba?
Su Mom fa? Suna ina ne?
Hajiya Wujdane sarakan fitsara ina bakin ya tafi ne????????????
[2/1, 2:30 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*32*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

*ina barar adu.a bayin Allah , na gode*

Kalar baya son rainin nan yayi da fuskarsa ya ce" mu tafi ka aje ni gidan Mom, na gaisheta na ga Boy

Anwar ya mike ya shiga tatara kayan yayan nasa dangin su waya bai ce komai ba, can kasan zuciyarsa kuwa dariya na tukarsa yana ayana abubuwa da dama da ya ga sun canza a wajen yayan nasa a kasan ransa

Shigowarsu gidan Mom gabansa ya yanke ya fadi, domin ya ga wani sabon babur a ajiye a nan daga an shigo toh aman bai saka komai a ransa ba sai sa ya hango Wujdane ta fito da gudu gudu ta nufo tsakar gidan da wata doguwar riga baka mai santsi a jikinta, garin gudun da take ya saka dan kwalinta ya fadi aman bata tsaya damar daukansa ba

Lukman ne kamar yanda suka yi da Aba kan ya zo zai yi masa bayanin da zai saka shi kara gamsuwa ya yi amana da halin da yake ciki a yau ya shirya zuwan wanda ita bata san da zancen ba kwata kwata shi sin kansa bai san cewa wai a nan gidan take ba

Tana zaune ta ga shigowarsa kamar a mafarki hakan ya tunzura zuciyarta ta mike ta nufo shi dan ta yi masa tas irin wulakancin da yayi mata domin ita rabonta da ta saka shi a ido tun aurensu sauran kwana uku gashi yanzu ya zo ya saka haka ta faru ta auri mutumin da bai san darajarta ba

Shi dinma gidan yake karewa kalo, a kasan zuciyarsa yana aiyana lale Aisha ta shigo baban gida, yana kallon tsare tsaren gidan ya hangi budurwa na nufo wajensa da gudu gudu ko dan kwali babu a kanta hakan ya saka shi bada hankalinsa wajen daidai shigowar su Alaidine

Tana isowa ta ja ta tsaya dan nesa kadan sa shi auka shiga aikawa juna da kallo, ita kallon haushi da tambayar abunda ya kawo shi gidan take shi kuwa kallon mamaki , soyaya kai harma da kokonton anya Wujdane dinsa ce?

Hannunsa ya dago ya nunota cike da fara.a ya ce" WuWuWujdanena? Ke ce? Dan Allah ke ce? Daman Elhaj nan ya kawo min ke? Wujdane na daman kina raye? Daman ba.a yi maki aure ba yayanki yace na manta ki anyi maki aure? Daman na fada masa ko wa kike aure sai ya sake ki na auri abinna domin dan ni kadai aka halice ki Wujdane na, ni na san ba zaki taba mantawa da soyayarmu har ki auri wanina ba

Anwar da ya lura da yannayin yayansa yayi kokarin bude motar dan ya karasa ya babala wannan mahaukacin da yake yiwa kallon bashi da hankali sannan ya kora Wujdane da har ta tsaya sauraron wani kato da aurenta ko shigar kirki babu a jikinta, aman mai sai Alaidine ya dakatar da shi
Gaba daya jikinsa rawa yake, du irin sanyin ac din motar Anwar bai hana zufa karyo masa ba, a hankali ya bude motar ya fito ya dan matsa wajensu ya ja hannunsa ya harde a daidai kirjinsa ya tsurawa yannayin tsayuwarsu ido sannan yana iya jiyo abinda suke fada daga inda yake

Wujdane ki amsa ni mana? Ina rokonki ki amsa ni Wujdane, 👏🏽 Lukman ya karasa da kalar tausayi yana kallon Wujdane da take jifansa da harara

Cikin wata murya mai cike da takaici ta ce" Lukman, mai nayi maka a ranar nan? Abinda kawai nake son sani mai yayi zafi da ka so zubawa iyayena kasa a ido? Yanzun bai isheka ba ka biyo ni nan? Mai ka zo yi min a nan?

Nan Lukman ya marairaicw murya ya ce" Wujdane ki gafarce ni, a wannan rana kadarata ce ta afka min, bani da sanin abinda zai faru sai ana sauran kwana biyu, an yi min aure da wata a gidanmu sannan an hana ni aurenki, ba yanda banyi ba dan su saurareni aman suka yi bilis da ni, Elhajin gidannan shi ya taushe ni harma na samu nutsuwa na tafi cike da kunyar malan, ashe ya kilace min ke a nan Wujdanena?

Wani kallon sama da kasa ta bi shi da shi, ta ja uban tsaki ta ce" haka ne, an tarda su an fada masu Wujdane yar iska ce ko? An gargade su kar su yarda ka auri mai sifar aljannu ko? Lukman ni nayi imanin dama da wuya yan gidanku su soni aman banyi tunanin zaka shiga jikina haka sannan ka wulakantani ba, sai dai ka sani a yanzu ba wani abin da zai iya shiga tsakanina da kai domin an yi min aure, an aura min dan gidan Elhajin gidan nan dalilin da ya saka ka ganni a gidan, an aura min mijin da a duniyar nan ina gannin ina cikin mutanen da ya tsana, an aura min mijin da aka yi masa dole baya ra.ayin ganina baya maraba da ni, banyi tunanin mijin da zan zauna da shi zai kyamace ni ba, na dai yi tunanin dangin mijina aman a rayuwana na yau ina cikin gidan mahaifiyar mijin da aka aura min take sona tamkar yarta, aba na kulawa da rayuwana yan uwansa na mutunta ni, Lukman ba komai ka je Allah ya baka zaman lafiya da jakar matar da ka aura

Tana gama fadan haka ta juya da nufin barin wajen, domin har ga Allah ita tana jin Lukman a ranta ko ba komai shine mutumin da ya jure haukanta harma ya saka tayi amana da shi
Chapter 5 · 0% Book details