Sashe 9
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon Inna tayi lokaci guda hawaye ya zubo mata, da sauri ta rungume ta tana kuka, sakin baki Bappa yayi, a hassale ya ce. “ Wannan munafurcin fa har ina? Yaushe kuka saba ban sani ba, idan ma wani siddabaru kike kulla mata to ashirr dinki, dan kudi kam kamar na samu.”
Sakin juna suka yi Safeera tayi gaba su Sageer na mara mata baya, da sauri Jon ya bud’e mata back site, gudu Bappa yasa yazo ya shige motar yana fadin. “ Haka kawai na taimaka muku ku gudu kuma, ai baku isa ba chabbb sai kun biya ni kudina ni da hakkina.”
Babu wanda ya kulasa har ya gama surutun shi, hawaye Safeera take yi tana kallon Inna wacce itama hawayen take.
Shiga motar tayi Jon ya rufe, su ma suka shiga aka fice daga unguwan da gudu kamar zasu fure.
*SAIFULLAHI POV*
Tun bayan da Ammar ya masa fada akan tunani tunanin da yake yi kullum, bai kuma sake zama yayi dogon tunani ba sai dai abun da ba’a rasa ba.
Haka kuma tun da Ummah ta kawo masa abinci yaci yaji kawai yana son sake cin wani girkin ta.
Yau Monday yasan yana da shari’a karfe goma akan wani fyaden da akayi wa yarinya yar shekara goma, hakan yasa ya shirya cikin kayan lawyer, wanda ya masa kyau sosai kamar ka sace shi, gemunsa wanda rabon shi da yayi kyau haka tun bayan tafiyar Safeera, shafawa yayi yana murmushi wanda ya rasa gane na menene.
Jakansa ya rike a hannu da hulansa da rigar daurawa akai irin nasu barrister, murmushi yayi yana rike wayoyinsa ya fita daga bangaren.
Kallon apartment din yayi kafin yaji yana nufan na Ummah.
A bakin kofar ya tsaya yana kallon kofar kamar zai shiga kamar bazai shiga ba, hannu yasa ya tura yana saka k’afarsa na dama tare da yin sallama ciki-ciki.
Kamshin turaren wuta ne ya masa sannu da zuwa, lumshe ido yayi dan rabon da yaji wannan kamshin tun yana shekara ashirin da uku.
Takowa yayi zuwa tsakiyan falon yana kallon hanyar kitchen dan jin motsi.
Ummah ce ta fito da food flask a hannunta zata kai dining table, hada ido suka yi, da sauri ta ajiye flask din a dining ta dawo inda yake tsaye ta zuba masa ido.
Sanyayyen murmushin nan nasa da ta dade bata gani ba yayi, bata k’ara burkicewa ba sai da taji ya ce. “ Ina kwana?.”
Da sauri ta kalli fuskarsa ta ce. “ Lafiya Saif.”
Kallom inda ta ajiye flask din yayi yana fadin. “ Akwai abincin ne?.”
Da sauri ta ce. “ Eh kazo na zuba maka.”
Dan bata fuska yayi yana cewa. “ No bazan ci a nan ba ki zoba min zan tafi dashi.”
Jinjina kai tayi jiki na bari ta nufi kitchen, basket 🧺 ta dauko medium ta dauko madai-daicin food flask da tea flask ta fito lokacin ya zauna a kan kujera.
Tana kallonsa tana murmushi tare da addu’a a ranta Allah yasa danta ya dawo gare ta, potato da kwai ta soya ta zuba masa, ruwan shayi ta zuba a tea flask din, milo da madara na sachet ta yanka tana saka masa guda bibbiyu, kana ta zuge zib din basket din tana daukowa.
Tashi yayi ya saka hannu zai karba, girgiza masa kai tayi ta ce. “ Zan kai maka har mota, yau kadai kazo gurina cin abinci bayan shekaru da dama.”
Bai ce komai ba ya nufi hanyar fita, mara masa baya tayi da basket din har zuwa compound din gidan, hango shi tayi tsaye masifa.
Karasowa tayi zuwa inda take tana jin yana cewa. “ Idan shi Sageer zai fita shi daya to me yasa zai dibi sauran security’s din? Ni waye zai kai ni yanzu?.” Ya fada a fusace yana danna waya da alama kira yake yi.
Hannu Ummah tasa ta karbi wayan nasa, da sauri ya d’ago kai dan ganin wani isheshen ne, lokacin da yaga ita ce sai ya kawar da kai yana cewa. “ Zan yi kira ne.”
“ Zaka yi late, ka bari baka san wani uzuri ne ya fitar dashi ba, akwai sauran security’s din Dad dinka sai su kai ka.” Ummah ta fada a cikin kwantar da murya.
Shuru yayi kafin ya jinjina kai, inda security’s din Dad suke ya kalla yana daga musu hannu, nan da nan suka iso gurin shi.
Ummah ce fada musu cewa zasu kai Saif, nan suka kawo mota guda uku, bude masa suka yi yana shiga, Ummah ta ajiye masa basket tana fadin. “ Ga wayanka.” Karba yayi, ta kuma cewa. “ Allah ya tsare ya baka lada sannan Allah ya baka sa’a a duk shari’an da zaka gudanar, Allah ya kau da hau.”
Lumshe ido yayi yana dago kai ya kalle ta ya furta. “ Ameen.” Da haka suka fice daga gidan, kafin Ummah ta nufi dakin ta.
Koman da ya faru akan idanun Mom ne, har sai da ya fita daga gidan kafin ta sauke labulen tana furta. “ Akwai bala’i, kut wai matar nan da wani boka ta dogara ne, hmm 🤔 dole na koma gurin Malamin nan a sake min aiki a kan shi.” Da haka ta koma dakinta.
*STATE HIGH COURT OF JUSTICES ( SHCJ )*
Yana zuwa ya wuce office nasa yaci abinci, yana ci yana yabawa a kan yayi dadi.
Tun bayan da ya gudanar da shari’a na karfe 10, bashi ya samu kan shi ba sai guraren karfe sha biyu da wasu mintuna.
Suna zaune shi da Ammar a office suna hira, wayansa ne yaji ya fara ringing, dubawa yayi ganin Sageer ne yasa ya dauka rai a bace ya fara cewa. “ Wai Sageer ina ka shiga ne tun da safe? Bayan kuma kasan babu wanda zai kaini gurin aiki.”
Ta cikin wayan Sageer ya ce. “ Sorry Sir.”
Numfashi ya sauke ya ce. “ Me ya faru?.”
Sageer ya ce. “ Sir kana gurin aikin ne ko zaka koma gida ko gidanka.”
“ Lafiya kake tambaya na?.” Cewar Saif da mamaki.
Sageer ya kuma cewa. “ Sir na samo maka Safee…”
Bai karasa ba Saif ya mike a haukace yana cewa. “ Safeera ta ka samo min? A ina kuke yanzu? Tana lafiya ko babu abun da ya same ta ko? Taci abinci? Ka fadamin inda suke gani nan zuwa yanzu yanzu..
*A cigaba da sambadomin comments da like’s ni kuma zan cigaba da suburbudo muku typing 😂🤸♀️*
*_TAKU HAR KULLUM DR TEEMERH✍🏼_*
12-
💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_
*Na*
*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 12*
Bai ƙarasa ba Saif ya miƙe a haukace yana cewa. “ Safeerata ka samo min? A ina kuke yanzu? Tana lafiya babu abun da ya same ta ko? Taci abinci? Ka faɗamin inda kuke gani nan zuwa yanzu yanzu.”
Ta cikin wayan Sageer ya ce. “ Sir muna gidanka na GRA.”
“ Ok.” Kawai ya ce yana ɗaukar key ɗin mota zai fita, tare hanya Ammar ya yi yana masa kallon mahaukaci, a fusace ya ce. “ Malam ka bani guri na wuce dalla.”
“ Baka cikin hankalinka Saif, saboda haka bazan bari kayi driving ba sai dai muje tare.”
Cilla masa key na motan ya yi, ya karɓa suka fito haraban kotun wanda yake nan cike da mutane, ta baya suka bi dan gudun idon mutane, inda motar Ammar yake fake suka nufa, ya bud’e da sauri Saif ya shiga gurin mai zaman banza, Ammar kuma ya shiga gurin driver.
Da ƙarfi ya fuzgi motar suna barin gurin, gudu Ammar yake tsalawa a tsakiyar titin kamar ba gobe, direct titin da zai sada ka da GRA suka nufa, har suka iso bakin get na gidan babu wanda yayi wa wani magana.
Horn Ammar ya danna, mai gadi ya wangale get da wuri suka shiga.
Ko parking dai-dai Ammar bai yi ba Saif ya fice da sauri har yana k’ok’arin fadi.
Dake Sageer yasa pin din ƙofan falon hakan yasa ya bud’e musu shi da Safeera da Bappa suka shiga, sauran kuma suka tsaya a bakin ƙofar.
Kallon su Saif ya yi, kafin ya saka hannu a jikin kofar, sai da yayi scanning kafin ya rubuta Welcome kana ya bud’e.
A haukace ya shigo falon yana tsayawa cak lokacin da idanunsa ya sauk’a cikin nata, k’asa ɗaukewa yayi haka itama, a slow motion ya iso inda take, kafin ta ankara ya rungume ta da ƙarfi yana sauke ajiyar zuciya, wani sanyi mai ratsa jiki ya mamaye shi.
Sun fi minti biyar a haka, Bappa ya sake baki yana kallon su haka ma Sageer, Ammar guri ya samu ya zauna ya daura k’afa daya kan daya shi ma ya zuba musu ido.
A hankali ta fara gane me yake faruwa, tunawa da ajikin wanda take tayi hakan yasa ta fara mutsu mutsun kwace kanta, sake manne ta yayi tsam a kirjinsa yana cigaba da sauke ajiyar zuciya.
“ Ka sake ni nikam ka matse ni sosai.”
Girgiza kai yayi yana dan sausauta rikon dan shima yasan ya matse ta sosai.
“ Ni ka kyale ni dalla.” Ta fada a fusace tana ture shi daga jikinta wanda ko motsi bai yi ba balle tayi tunanin zai turu.
Jin d’igon ruwa a wuyanta yasa tayi mamaki, Ammar ne ya taso yazo ya banbare shi daga jikinta da kyar, hannu tasa ta juyanta tana lafuto d’igon ruwan, kallo take kafin da sauri ta kalli fuskarsa wanda hawaye suka wanke.
Ammar da mamaki ya ce. “Saif kuka!!!.”
Sageer yayi sauri ya fita daga falon dan kukan uban gidan nasa tamkar karaya ne a gare shi, Bappa kuma ya samu guri ya zauna a kan carpet yana tuna a ina yasan me wannan fuskar.
Zubar da gwiwowinsa yayi a gabanta yana hade hannaye biyu yayin da idanunsa ke zubar da kwalla, Ammar da mamaki ya kamasa ya saki baki yana kallon ikon Allah.
Magana ya fara yi cikin muryan kuka. “ Na roke ki, dan Allah dan girman Allah kiyi hakuri.”