← Book details Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 39

Sashe 4

Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*

*Page 5*

A firgice ta juyo tana kallon shi dan ita bata yi tunanin zai fito yanzu ba, fuskarsa a tamke yake kallon ta cike da zargi, kafin tayi wani magana ya jefa mata tambaya. “ Wacece ke?.”

Wani yawu ta hadiye mai kauri, kafin ta dan sai ta nutsuwarta tana cewa. “ Ban gane wacece ni ba?.”

“ Kar ki raina min hankali mana, wa ya aikoki gurina?.”

Ja baya ta fara yi ganin yana matso ta, muryanta ya fara rawa gurin fadin. “ Babu wanda ya aiko ni, kuma ai naga ku kuka dauko ni, sannan..”

A tsawace ya ce. “ Munafuka dukan ku bakin ku daya, kowa kudi yake nema, burin ku kawai ku kashe ni, na dauka ke mutumiyar kirki ce na dauko ki ashe kura ce ke lullube da fatar akuya.”

Da mamaki ta nuna kanta tana cewa. “ Ni!!! Me ka min da zan kashe ka, ku fa kuka dauko ni…”

“ Dalla malama ki dena fakewa da ni na dauko ki, dama kin shirya cutar da ni ne Allah ya kama ki, mara mutunci kawai, ina k’ok’arin mai dake mutum ashe ke zuciyarki baki ne.”

Hawayen da suke shirin zubo mata ta dauke, kafin ta mika masa wayansa tana fadin. “ Ka sallame ni zan tafi na hakura da aikin.”

Gira daya ya daga mata ya ce. “ Ga hanya nan daga nan har lahira, na sallame ki, ki fice daga rayuwata ko kadan bana buk’atar ganin ki.”

Jijjiga kai tayi tana kare masa kallo, kafin ta bud’e kofar ta fice daga dakin, da sauri ta sauko daga kan stairs, direct kofa ta nufa ta bud’e ta fita.

Tana fitowa compound din ta nufi hanyar get, bud’e mata karamin kofa mai gadi yayi ta fice.

Tsuki yaja lokacin da yaga fitan ta daga gidan, komawa daki yayi ya shirya cikin kananan kaya JC red da trouser baki, ya dauko wayansa ya fice daga gidan baki daya.

*SAFEERA POV*

Tafiya take yi ba tare da ta san inda zata nufa ba, wani daci take ji har zuciyarta, tun da aka haifeta har ey yanzu bata huta ba, kullum cikin wahala take tana fadi ka tashi, sanadiyar yunwa ta siyar da martabarta na y’a mace, a tunanin ta zata samu kudin da zata cigaba da karatu da kuma samun abinci, sai dai kash babu riba, bai bata kudin ba bai kuma kalle ta da daraja ba, karshe ma korar kare ya mata.

Wani kwalla taji ya tsiyayo mata, hannu tasa tana taba hawayen, murmushin da yafi kuka ciwo tayi tana cewa. “ Yau ni nake zubar da hawaye? Lallai abun ya min zafi, ashe zan sake kuka?.” Ta tambaye kanta tana mamaki.

Cigaba da tafiya tayi akan titin tana murmushi kamar wacce ta zauce, ciwon da take jin kasarta yake mata yanzu duk ya dena, babu abunda yake damunta kamar yunwa da kuma inda zata kwana.

Shuru tayi tana zancen zuci. “ Ko zan koma gidan karuwai din ne? Amma idan na koma babu riba fa, me amfani idan na lalata kai?.” Wani zuciyar ya ce mata. “ Lalata kanki na nawa kuma, kawai kije ki cigaba da yi.”

Saurin girgiza kai tayi a fili ta furta. “ Yau din ma tsautsayi ne, kuma na daina bazan taba sake kusantar zina ba ko da zan mutu da yunwa kuwa.”

Ba tare da ta ankara ba har ta fita daga unguwar GRA dake garin maiduguri, tafiya kawai take ba tare da ta san inda take nufa ba, tun tana ganin mutane da motoci har ya zamana ta daina kallo baki daya, alamun dare yayi, ba kajin komai sai kukan tsuntsaye kawai.

A bakin gada ta zauna tayi shuru, tunawa da tayi bata yi sallan mangarib da isha ba, da sauri ta mike ta nufi inda ta ga ruwa a kogi.

Tana isa ta tsugunna a bakin kogin, muryan gardawa ta fara ji suna tunkaro inda take, da sauri ta waiga dan ganin su, su shida ne kuma kallo daya zaka musu ka gane a buge suke.

Inda take suka nufo, alamun tsoro ne ya bayyana a fuskarta, da sauri ta mike dan guduwa, dayan ne ya sha gabanta yana dariya da fadin. “ Ga nama har gida yau.”

Dariya suka kwashe da shi, ta gefe tayi zata gudu suka zagaye ta, a dan tsorace ta furta. “ Ku matsamin zan wuce.”

Dariya suke daya na kama hijabinta, kan kame jikinta tayi tana cewa. “ Ku barni dalla ni ba irinku bace.”

Dariya daya ya mata ya ce. “ Hahhhh… haba… ashe keeeee… ba iriiiiin mu bace… ya kamata ki zama irinnn mu kam.” Ya fada yana fuzgota da karfi zuwa jikinta.

Ihu ta saka tana cizonshi a hannu, wanka mata mari yayi yana yage mata hijabi da karfi, bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba.

Wurgar da ita yayi a kasa yana shirin hawa kanta, da sauri tayi burgima ta nufi bakin ruwan, jawo kafarta suka yi, ta naushe shi a kafa, da sauri ta mike tana kallon su, duk da dare ne sosai amma hasken wata ya haska fuskar su.

Kafin kowa ya ankara daya daga cikinsu ya saka hannu ya tunkude ta cikin kogin, ihu ta saka tana fadawa ciki, kusan a tare suka ce. “ Kashe yar mutane kayi fa, kasan zurfi da kogin nan yake dashi.”

Tuni suka wartsake daga mayen da suke, wanda ya yaga mata hijabi ne ya ce. “ Azumi ya hau kanka san tabbas ta mutu.”

Shuru gaba dayan su suka yi, kafin wanda ya tunkude ta ya furta. “ Kuzo mu tafi kawai, anyi an wuce wajan.”

“ Baaba wannan fa ba eya bane, mu gwada shiga ko zamu same ta mana.” Cewan wani daga cikin su wanda tun da suke maganar bai ce komai.

“ Ba dani za’ayi aikin nan ba, kunga tafiyata, wanda zai biyo ni muje to.”

Tafiya suka yi, dayan na juyawa yana kallon kogin..

*Hmmm nace kunga na muku typing kadan ko, yoo ai bakwa yin comments da like’s ne, kuma maganar gaskiya na zauna kusan awa uku, biyu ina typing, common comments bazaku iya ba😉 sai da ku. Muje a haka more comments da like more typing.*

*DR TEEMERH✍🏼*

6-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari

Na

Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*

*Page 6*

Tafiya suka yi, dayan na juyawa yana kallon kogin, ji yake kamar ya koma ya duba ko ta na nan, tsayawa da tafiya yayi yana kallon baya.

Juyawa suka yi ganin baya bin su, daya daga cikin su ya ce. “ Kazo mu tafi kafin police su iso.”

“ To.” Ya fada yana bin su suka bar wajen, duk da kuwa hankalinsa bai kwanta ba.

*SAIFULLAHI POV*

Tun bayan fitansa daga gidan bai tsaya ko’ina ba sai gidan su, yana zuwa security suka bud’e masa get ya shiga yayi parking, ko kallon bangaren Mahaifiyarsa bai yi ba ya wuce apartment nasa ya shige.

A falonsa da ya sha haduwa ya zauna ya rasa me yake masa dadi, idanunsa sunyi ja gashin kansa ya hargitse, dafe kai yayi yana tunanin abun da ya mata.

Wayansa ne ta soma ringing, mantarwa yayi sai da yayi ringing sau biyu ana uku ya dauka ya manna a kunne ba tare da ya duba number ba.

Muryan mace yaji tana sallama, sauke wayan yayi ya duba yaga number kafin ya manna ya amsa sallaman.

Ta cikin wayan aka ce. “ Dazu an kirani bana kusa shine na kira.”

Shuru yayi yana tunanin ma wa ya bawa wayansa, muryan matar ce ta katsai shi, da sauri ya tuna cewa Safeera ta dauka, hakan yasa ya ce. “ Sorry mistake din number nayi.”

Matar na cewa. “ Ba komai nagode.”

Da haka ya kashe wayan yana cilli da ita, tashi yayi ya shiga daki.

*WAYE SAIFULLAHI?*

Alhaji Amdaz Saifullahi shine asalin sunan Dad, haifaffan garin Maiduguri ne, Iyayensa ma ƴan garin ne, shi daya suka haifa daga shi kuma Allah bai sake basu haihuwa ba, ba masu karfi bane amma hakan bai hana su sa yaronsu a makarantar boko da kuma addini ba.

Tun daga nursery school har degrees Dad yayi, haka ma saukan Al-Qur’ani, yana gama degree bangaren business ya fita da aikinsa, nan da nan kasuwanci ya budu Allah kuma yasa masa albarka a ciki.

Sosai yake taimakawa iyayensa, haka ma yan unguwa, duk inda ka shiga idan kana aibanta shi sai an maka cha akai, sosai Al’umma ke son shi, gidajen mai yana da su kusan guda biyar, company ma haka ga albarkan iyaye na ta bin shi.

Babban gida ya gina a unguwar Gomari, apartment guda biyar ya gina a ciki, nan ya kawo iyayensa apartment daya, shi ma ya zauna a daya, nan kuma Nanah ta fara damunsa kan cewa ya isa ya ajiye iyali yanzu, nan ya bata zabi kan cewa ta nemo masa wacce zai aura.

Nanah taji dadin hakan inda ta tuntubi Baffa kan cewa yana da wacce yakeso Amdaz ya aura ne? Baffa ya bata wuka da nama ta nemo masa na aure, ita kuma ta nemo masa yarinyar kawarta wato Ummah, auren ko sati biyu bai kai ba aka daura, Ummah ta tare a gidan a apartment daya.

Sosai zaman lafiya ke wakana a cikin gidan, Ummah tana bin umarnin Amdaz sawu da kafa, haka ma tana yiwa iyayensa biyayya dai-dai gwargwazo.

Ana haka ne kuma Zazzabi ya kama Nanah, wanda ko kwana biyu bata yi ba ta ce ga garinku nan, Amdaz yayi kuka sosai wanda har ya zuba masa ciwon kai, haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau da dadi gobe babu.

Ummah tayi shekara biyu a gidan amma ko batan wata bata taba yi ba, tun Amdaz baya damuwa har ya fara yi, sun je asibiti da dama amma abu daya suke fada musu cewa lafiyansu kalau yake.

Ranar Amdaz ya samu Ummah ya ce. “ Amina zan kara aure.”

Bata ce masa komai ba sai fatan zaman lafiyan da ta musu, duk da kuwa zuciyarta na mata zafi amma haka ta daure ta danne zuciyarta.
Chapter 4 · 0% Book details