← Book details Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 39

Sashe 6

Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru tayi tana tunani kafin tace “ Yana ina?.” Tafiya ya yi tana biye dashi, a bakin kofar gidan suka tsaya ya nuna mata motan tsakiya ya ce. “ Yana ciki.” Kafin tace. “ Nawa zai biya?.”

*Masu karatu idan baku manta ba nan ne farkon littafin ko? To yanzu zamu daura daga inda muke.*

*CIGABA DA LABARI*

Shower 🚿 ya sakarwa kansa ya dafe jikin bango, tunani ya fara yi tun sanda ya fara aikata zina, gani yake kamar bai aikata ba, ji yake kamar tursasa shi ake yi yake yin wasu abubbuwan.

Jikinsa kwata-kwata bai basa cewa wai shi yayi zina da Jannah da Safeera ba, wai tukun nan ma ina suke? Ya tambayi kansa kafin ya furzar da iska yana dungule hannu ya kai naushi da karfi.

Bai san sanda ya saki ihu ya furta. “ Safeera!!!!!.” Wanda kusan sai da ya dauki gidan.

Daura towel yayi da sauri a kugunsa ya fito, inda ya jefar da wayansa ya koma ya dauka, number dazun ya kira, safa da marwa ya fara sai da ya kusa katsaiwa kafin aka dauka.

Da sauri ya ce. “ Dan Allah wacece ke?.”

Ta cikin wayar matar ta ce. “ Kai fa ka kirani.”

“ Eh nasani, amma dan Allah kina wani unguwa ne ko gari?.”

“ Malam lafiya kuwa na maka wani abu ne kakeson ka kamani?.”

Dafe kai yayi ya ce. “ A’a babu abunda kika yi, kawai so nake na sani.”

Shuru akayi kafin ta ce. “ Ina Maiduguri wajen 20 house’s.”

Jijjiga kai ya mata kamar tana kallonsa ya ce. “ To na gode, dama tambaya nake ko Safeera tazo.”

Shuru tayi ta ce. “ Safeera tun jiya da safe bamu sake ganin ta ba har yau.”

Wani numfashi ya sauke kafin ya ce. “ Ke din y’ar uwarta ce?.”

“ A’a haduwa kawai muka yi.”

“ To shikenan nagode.” Ya karashe jiki a sanyaye wanda ya rasa na meyasa.

Number Sageer ya danna, bugu biyu ya dauka yana cewa. “ Sir nazo kuma ka fita.”

Bai kula zancen nasa ba ya ce. “ Sageer bayan gidan da muka je dauko yarinyar nan kasan wani gurin da take zuwa kuma?.”

“ A’a Sir, dan nima ranar ce na fara ganin ta a rayuwata, amma lafiya ai naga kuna tare.” Sageer ya fada yana mamaki.

Numfashi Saif ya sauke ya ce. “ Sageer wai na kore ta ne.”

“ Bangane ba Sir? Kana cewa wai, me hakan ke nufi ba kai ka kore ta ba tafiya tayi?.”

“ Sageer bata min rai tayi shine nace ta tafi.”

“ Sir kuma ta tafi?.”

Kamar zai yi kuka ya ce. “ Eh fa kuma idan na zauna sai ina kallon ta tana naiman taimako na, Sageer akwai abun da ya samu yarinyar nan, Sageer Safeera tana cikin matsala duk da nasan ni ne silan komai amma nasan ita ba karuwa bace, ai kaga da ita karuwa ce to gidan zata koma amma kaga bata koma ba, zan mutu idan banganta ba, akwai hakkinta akai na, Sageer ina Safeera take?….

*DR TEEMERH ✍🏼*

8-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari

Na

Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*

Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

*Page 8*

Kamar zai yi kuka ya ce. “ Eh fa kuma idan na zauna sai ina kallon ta tana naiman taimako na, Sageer akwai abun da ya samu yarinyar nan, Sageer Safeera tana cikin matsala duk da nasan ni ne silan komai amma nasan ita ba karuwa bace, ai kaga da ita karuwa ce to gidan zata koma amma kaga bata koma ba, zan mutu idan banganta ba, akwai hakkinta akai na, Sageer ina Safeera take?.”

Duk ya rikita shi yama rasa taya zai fara, yasan waye Saif kuma yasan halinsa, sai dai kwanan nan ya canza hali gaba daya.

Muryansa ne ya katsai Sageer jin yana cewa. “ Baka ce komai ba ko na fita naimanta ne?.”

Saurin girgiza kai Sageer yayi yana cewa. “ Sir zan nemo ta.”

“ To kayi sauri.”

“ Ok.”

Numfashi ya sauke ya zauna yana tunani.

*SAFEERA POV*

Wani karamin bukka ne na kara an masa ado da kayan da, sai ka sunkuya kafin zaka iya shiga cikin bukkan.

Wani tsoho ne ya shigo da kwarya a hannunsa ciki da ruwa, sai da ya sunkuya kafin ya shiga cikin bukkan.

Inda mutun yake kwance akan gadon kara ya nufa, ajiye kwaryan yayi a gefe kafin ya zauna kusa da gadon kaban.

Addu’a yayi yana tofawa kafin ya janye gashin da ya rufe fuskarta, kyakkyawar fuskarta ya bayyana mai cike da nutsuwa, a hankali ya fara karanto addu’a yana tofa mata da ruwa.

Ya kusa mintuna goma yana yi kafin ya tsaya yana kallo hannunta din da ya fara motsi, cigaba da yi yayi yana watsa mata ruwan a fuska, wani dogon numfashi taja tana saukewa tare da bud’e idanunta.

Murmushi dattijon ya mata yana cewa. “ Alhamdulillah kin farka, kina gani na ?.”

Zuba masa ido kawai tayi tana kallon shi, kafin ta sake lumshewa a hankali ta bud’e.

Muryanta a sanyaye ta ce. “ Waye kai?.”

Tashi yayi da sauri ya nufa waje, ta bisa da ido, ko seconds bai yi ba ya dawo shi da wata mata fara kyakkyawa, nan ma bata ce komai ba sai kallon su da take yi.

Zama suka yi a gefen ta, matar na cewa. “ Ya sunanki yarinya?.”

“ Safeera.” Ta fada a sanyaye.

“ Daga ina kike?.”

Kallon dakin tayi kafin ta ce. “ Ina ne nan?.”

Tsohon ne ya ce. “ Borno ne.”

“ Wani unguwa?.”

“ Bulunkutu.”

“ A ina kuka samo ni?.”

Matar ta ce.” Yanzu dai kiyi wanka tukun, sai kici abinci kafin mu fara.”

Gyada kai tayi, k’ok’arin tashi ta fara Inna tasa mata hannu tana kamata, a hankali ta saukar da kafarta tana kallon yanda yaji ciwo ya gurgurje, hannunta ta gani yanda shima yaji ciwo, numfashi ta sauke a hankali kafin ta kalle su tana cewa. “ Nagode.”

Murmushi Bappa ya mata yana cewa Inna ta kaita tayi wanka, shi kuma ya tashi ya fita.

Bayan sun fito daga band’akin ne Inna ta bata kaya ta ce ta saka, karba tayi ta saka tana godiya, Inna ta tashi ta fita.

Shuru Safeera tayi tana kallon hannunta din da yaji ciwo sosai, hawaye ne ya zubo ba tare da ta sani ba, hannu tasa ta goge, Inna ta shigo da kwarya a hannunta.

A gabanta ta ajiye, murmushi Safeera ta mata tana cewa. “ Inna sannu.”

“ Yawwa dai y’ar nan, sauko na baki abinci kici dan tun da aka dauko ki daga bakin kogi har yau baki ci komai ba.” Inna ta fada tana bude biski da miyan alaiyaho da ta kawo.

Da mamaki Safeera ta ce. “ Inna kwanana nawa a nan?.”

“ Kinyi wata daya da kwanaki fa.”

A dan tsorace ta ce. “ Kuma ban mutu ba ina raye?.”

Murmushin manya Inna ta mata tana cewa. “ Kina wasa da lamarin Ubangiji ko? Ki godewa Allah kawai da yasa kina raye, amma lokacin da muka tsintoki mun dauka ma bakya raye, saboda irin ciwukan da yake jikinki.”

“ Nagode.” Ta fada a sanyaye tana saukowa ta fara cin abinci.

*SAIFULLAH POV*

Tun bayan da ya kori Safeera hankalinsa bai sake dawowa jikinsa ba, ko zama yake ita yake kallo ko tafiya yake ita yake kallo ko bacci yake ita yake kallo, lokaci daya ya rame yayi duhu, duk cases din da yake dasu a court baya zuwa sai dai ya tura Ammar yayi wakilcinsa.

Baya yi wa kowa magana a gidan, kullum yana bangarensa baya fita, abun duk ya damu Ummah da Dad, duk da kuwa ko da yana fitowan ba kulasu yake ba.

Mom ma abin ya fara daure mata kai dan ko ta kirasa a waya baya picking, bata ganinsa ma bare ta tambaye shi, ya daukewa kowa na gidan kai.

Idan kaga yana waya to da Ammar ne ko Sageer, Sageer din ma suna waya ne dan ko yaji labarin Safeera amma shuru.

Idan yaji yunwa sai dai yaje kitchen ya hada tea ☕️ ya sha, abinci ya manta rabonsa da ci, ya baza hotunanta a gari da gidajen radio 📻, kuma ya saka kudi da mota ga duk wanda ya samo ta, amma kullum labarin daya ne babu ita.

Yau ma yana zaune a falonsa, yayi duhu ya rame sai ido, gashin kansa ko gyara babu, yana sanye da three quarter baki da tea sheet fari, hannunsa rike da cup da black tea ☕️ a ciki, yana sha yana kallon hotonta da ya dauka bata sani ba lokacin da suka je dauko ta a 20 houses.

Yana kallo yana tunani, hankalinsa duk baya jikinsa, yayi zurfi a tunani, fuzge wayan akayi a hannunsa.

Shuru yayi bai dago kai ba dan yasan sarai waye ne da wannan aikin, rai a bace Ammar ya ce. “ Saif yaushe zaka daina tunanin banzan nan ne? Dubi yanda ka rame kayi baki ka lalace akan mace, macen ma karuwa…..”

Bai karasa ba ya cukume wuyan rigarsa yana huci yake cewa. “ Ko da wasa kar ka sake cewa Safeera ta karuwa, ko da duniya zata kalle ta da wannan sunan ni bazan taba ganinta dashi ba, saboda idan ma ta baci ni na bata ta, ni zaka kira da gwarto ba ita ba, akanta babu abunda bazanyi ba dan ni na cuce ta.” Ya karashe yana sakar masa kwala.

Baki a sake Ammar yake ganinsa har ya gama, kafin ya jijjiga kai yana cewa. “ Na fahimta, ashe shi soyayya babu ruwansa da kai waye, wai yau *BAR.SSS* kuma aminina yana k’ok’arin dukana akan mace yar kwalta.”

A tsawace ya furta. “ Ammar ya isa!!!!, ka daina kiran Safeera da banzayen suna.”

“ Naji Saif kuma na daina, sai dai ka sani wannan tunanin bashi zai saka ta dawo ba dan bata ma san kanayi ba, sannan ka sani al’umma suna buk’atar ka, kuma mutane dayawa suna jiranka a court dan shari’arsu yana hannunka.” Ya kai karshe yana juyawa zai fita.
Chapter 6 · 0% Book details