← Book details Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 39

Sashe 5

Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wata ranar Asabar aka daura auren Amdaz da Hafsat wato Mom, inda zaman lafiya ya burkice a gidan, dan kullum Ummah da Amdaz suna cikin masifa akan cewa baya adalci amma haka yayi burus da maganar.

Mom sai da tayi shekara daya a gidan amma bata haihuwa, inda Amdaz ya sake shiga damuwa sosai har ya fara tunanin shine bashi da lafiya, amma sai ya samu Mom ya ce. “ Hafsat zan sake aure.”

Ba tare da ko kunya ba ta fara kwashe masa albarka. “ Amdaz baka isa kayi aure ba, kai baka haihuwa amma kaman bunshuru kullum cikin aure.”

Bai bi ta kanta ba ya fice daga dakin, washe gari kawai sai ji sukayi yayi aure, kusan karamin hauka akayi a gidan, amma Ummah ko fitowa bata yi ba.

Baffa ya musu wa’azi da nasiha amma a banza dan yana gamawa Mom da Mummy suka cigaba da masifa.

Tun ranar kuma Dad bai sake samun kwanciyar hankali ba, ana haka ne kuma ciwon ajali ya kama Baffa, satinsa daya a hospital ya rasu.

Mom da Mummy kullum suna cikin masifa, Ummah idan ta musu magana sai su dawo da fadan kanta, hakan yasa suna farawa zata koma apartment nata ta rufe, ansha fasa TV a gidan ba adadi.

Mummy tayi shekara daya a gidan Allah ya bawa Ummah ciki, wanda sai da Amdaz yayi murna sosai kamar zai kashe kansa dan dadi.

Mom babu shege da ficen da bata yi ba dan cikin ya zube amma yaki fita, Mummy ma haka kullum tana cikin fita amma sunyi sunyi abun yaci tira, hakan yasa suka zubawa sarautar Allah ido.

Cikinta ya cika watq tara ta haiho kyakkyawan yaronta, inda yaci suna Saifullahi wato takwaran Baffa suna kiransa da Saif.

Yaron ya tashi cikin gata da jin dadi, gashi da shiga rai da wuri, kowa ya gani sai yaje wajensa, Mom kullum cikin bakin ciki take idan taga yaron, Mummy kuma ta kawo wani sabon munafurci kan cewa yaron a gurin ta zai na kwana.

Ummah taki amma Dad ya yarda dan kwata baya jin maganar Ummah sai dai na Mummy da Mom, tana ji tana gani suka kwace mata yaro.

Ranar girkin Mom musamman Dad baya fita ko’ina, Mummy ma haka komun aikin da yake dashi bazai fita ba, amma idan na Ummah ne sai dare yake dawowa, tun abun yana damunta har ta barwa Allah komai.

Saifullahi yana da shekara biyar ya gudu daga gurin Mummy ya dawo gurin Mahaifiyarsa, abun ba karamin batawa Mummy rai yayi ba, da ta yiwa Dad magana sai yace ai yaro na kowa ne saboda haka ta barshi yaje ko’ina, inda ita kuma taci alwashi masu yawa akan shi.

Saif an saka shi a Makarantar masu kudi na boko da islamiya, kuma yana da ilimi sosai dan duk abunda aka koya masa tsaf zai haddace, yana da shekara sha biyar ya kammala secondary school nasa, washe gari kuma yayi sauk’a.

Dad da Ummah suka hada masa party da walima, wanda ya tara manyan mutane da yan kasuwa, kuma ya samu kyaututtuka masu tarin yawa da bangarori da dama.

Dad ya turasa Egypt 🇪🇬 dan yayi degree dinsa a bangaren Law, inda ko shekaru biyar ba’a tara ba ya dawo da certificate, nan aka yi murna kamar ba gobe.

Nan da nan gomnati ta dauke shi aiki a matsayin Lawyer, kaf borno sun san Barrister Saifullahi Safwan Saifullahi wanda yake yiwa kansa inkiya da Bar. SSS, ko plate number motan da yake hawwa da BAR. SSS ne a jiki.

Sosai yake son iyayensa, haka ma kishiyoyin Mamansa, kyakkyawa saurayi mai jini a jika, ga kasaita da aji, sardauna kuma hamshakin mai kudi, ga saurin shiga ran yan mata.

Yasha yankewa maza hukunci akan fyade, ciki kuwa har da abokinsa Yazeed, wanda suka yi Secondary tare.

Duk inda kaga Saif zaka ga Ammar, tun da suka hadu a Egypet suka zama abokanai, dan tasu tazo daya kuma abu daya suka karanta.

*DR TEEMERH✍🏼*

7-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari

Na

Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*

Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

*Page 7*

Duk inda kaga Saif zaka ga Ammar, tun da suka hadu a Egypet suka zama abokanai, dan tasu tazo daya kuma abu daya suka karanta, sai dai Saif yana da ciwon zuciya mai zafi, sannan yana da BP amma idan ya tashi suna k’ok’arin control din shi.

Tun Saif nada shekara ashirin da takwas ya daina ganin Ummah a matsayin mahaifiyarsa, dan yama daina kulata gaba daya ko gaisuwa baya had’a su, abun ba karamin burge Mom yake ba dan yanzu a gurin ta yake.

Yana da budurwa mai suna Jannah, sun dade suna soyayya dan tun kafin ya tafi Makaranta, ko da ya dawo bai sauya zani ba, sai dai ya canza hali, dan idan suna hira sai ya taba jikinta, ta nuna bata so amma sai ya ce. “ Baki waye ba, idan kuma ba sona kike ba sai ki fadamin na sani, akwai mata dayawa zan iya son duk wacce naga dama.”

Dake tana son shi sosai, sai ta bashi hakuri ta nuna yayi duk yanda yake so da ita, shi kuma ya samu dama har ya kai da sun kwanta tare, ranar Jannah tayi kuka sosai saboda tasan yanzu kam ba auren ta zai yi ba, kuma ba iyaye ne da ita ba.

Ko da Saif yaga tana kuka sai ya tabe baki ya sha kunu yazo inda take ya ce. “ Kin ga ba kanki farau ba, kuma ba kanki karau ba, idan zakiyi shuru kiyi.”

Cike da zafin rai da kuncin zuciya ta ce. “ Kana yankewa yaran mutane hukunci akan aikata fyade har ka turasu gidan yari, ashe kai ma kana aikatawa, ko kana ganin dan kai Alkali ne yasa baza’a hukunta ka ba? To Wallahi ka sani akwai ranar sakayya, akwai ranar tsayawa, ranar da kai ba komai bane a gurin Ubangiji face bawansa wanda baya tsoron fushinsa…”

Lafiyayyun mari ya sauke mata yana nuna ta da hannu ya ce. “ Ki fice min daga gida.”

Murmushin da yafi kuka ciwo tayi ta sauka daga kan gadon ta fita daga gidan, tana tafiya tana kuka.

Ko da ya koma gida Mom ta tusa shi a gaba tana tambayarsa me ya faru, inda ya fada mata komai da komai.

Cike da murna ta soma cewa. “ Kamin dai-dai Saif, duk yarinyar da ta maka kyau kawai ka aikata abun da yazo kanka.”

Nan ta cigaba da daura masa hudubar da zai kaisa ga halak’a, shi kuma ya dauka.

Ammar ya sha fada masa cewa ya nemo Jannah ya bata hakuri, amma fir ya ki wai ajinsa zai zube, ba yanda ya iya da aminin nasa dan haka bai sake cewa komai ba, duk da kuwa tun wannan abun ya faru bai sake yi ba, ko da kuwa Mom ta tambaye shi sai yace eh yayi, dan abun yanzu ya fara daure masa kai, yana ganin Mahaifiyarsa amma baya so yi mata magana.

Cases din da yayi akan aikata fyade babu adadi, dan yanzu ya zama Lawyer mai zaman kansa ne, duk inda ka shiga a garin borno kana cewa *_BAR SSS_* to fa ansan shi dan yayi suna sosai a taimakon mutane da kwachowa yan mata hakkin su.

Yau Saturday yana gida, kuma bai shiga bangaren Ummah ba haka ma Mom, dan Mummy dama baya shiga, yana bangaren shi zaune yana dannan waya.

Sallama akayi aka shigo, d’aga kai yayi ya ganta Radiya ce kanwar Mom wanda jiya tazo.

Isowa gurinsa tayi ta zauna a kusa dashi tana cewa. “ Ya Saif morning.”

Ba tare da ya ganta ba ya ce. “ Morning dear, how are you?.”

“ Am fine.”

Kowa yayi shuru, kafin ya ce. “ Akwai wani abu ne?.”

Murmushi tayi tana cewa. “ Yaya dama so nake muje outing ne.”

Gyada mata kai yayi ya tashi ya ce. “ Ba yau ba.” Daga haka ya shige daki, ita kuma ta tashi ta fice ranta a bace.

Yana shiga daki ya kama mararsa yana cije lebe, wayansa ya dauka ya kira amintatcen driver dinsa wato Sageer, bugu daya ya dauka.

Gaisawa suka yi duk da yaji muryan ogan nasa kamar ba lafiya, kafin Saif ya ce. “ Wata nakeso ka samo min amma yarinya, zata min aikin shekara daya ne.”

Tsaf ya gane Ogan nasa haka yasa ya ce. “ Sir nace ka shirya muje to.”

Shuru Saif yayi kafin ya ce. “ Ok ina zuwa.” Da haka ya shirya ya fito, yana tafiya yana dan daga kafa a hankali, a bakin falo Sageer yayi parking hakan yasa ya shiga ciki, mota biyu na mara musu baya.

Wajen 20 houses suka yi parking, Saif ya kalli Sageer ya ce. “ Wa ka sani a nan? Bana son wacce take kazanta fa.”

“ Sir nasani, nan y’an mata suna zuwa idan basu da gida ko marayu ko y’an gudun hijira.”

Gyada kai Saif yayi kafin ya ce. “ Hope plate number mota a rufe?.”

Sageer ya ce. “ Eh kana cewa zamu fita na rufe duka ukun.”

“ Gud, sauri ina jiranku.” Ya fada yana dauke kai.

Shiga Sageer yayi yana kallon gidan, y’an mata da karuwai sai matsowa gurinsa suke, hango wata yarinya kyakkyawa yayi tana tsaye daga gefe ta kame jikinta, hannu ya d’aga mata, nuna kanta tayi ya gyada mata kai.

A hankali ta fara takowa zuwa gurinsa, cikin muryanta mai dadi da amo ta ce. “ Ina wuni?.”

“ Lafiya.” Sageer ya fada yana kallon ta tun daga ssma har k’asa, kafin ya kalli fuskarta a ransa ya ce. ‘ TABARAKALLAH.’ A zahiri kuma ya ce. “ Ya sunanki?.”

“ Safeera.” Ta furta a hankali.

Gyada kai yayi ya ce. “ Safeera aiki zakiyi wa Ogana har na shekara daya.”

Da sauri ta daga kai ta kalle shi ta ce. “ Nawa zai biya ni?.”

“ Zamu baki 5m.”
Chapter 5 · 0% Book details