Sashe 30
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka ta fara dan tasan Ashiru sai ya aikata abunda yayi nisa kuwa, zata sake kira kenan wani waya ya shigo mata, ta kalli number tana mamakin waye ne, kafin ta d’auka.
Ta cikin wayan aka falfale da dariya ana cewa. “ Kin duba media kuwa? Ko baki san abunda yake faruwa bane?”
Kuka ta fashe da shi tana sakin wayan ta daura hannu a kai tana ihu. “ Na shiga uku, na mutu na lalace Ashiru ya cuceni a duniya, Wayyo Allah na.”
Ta dauki wayan da sauri tana hawwa IG, page na farko videos din ne ragaja, *Matar Alhaji Amdaz tana aikata alfasha da wani a hotel*, haka ma Facebook da Tiktok duk maganar ake yi, kuka ta cigaba da yi tana saurin tashi ta karkame kofar ta dan kar a shigo.
*DAD POV*
Dawowan shi gidan kenan aka kira shi a waya Abokinsa na ce masa ya hau Facebook ya duba labarai, ko ya kunna Tv ya duba me yake faruwa.
Yana sauke wayan wani kira ya shigo, ya dauka yana mamakin yanda yau abokanan shi suke kiran shi, yana dauka aka ce. “ Alhaji haka ta faru? Ya hakuri dama rayuwar duniyar sai hakuri” akakashe wayan.
Dad yabi wayan da kallo, kafin yayi hanzarin shiga bangaren Ummah dan shine kusa yana fadin. “ Amina kunna min Tv yanzu-yanzu”
Ummah ta fito daga daki ta kunna masa tana faman tambayar shi me ya faru, amma bai bata amsa ba.
Videos din ne a gaban Tv na Mom da Ashiru suna kwance a kan gado yana faman kwakulanta.
Ummah ta tafka salati tana kama baki, Dad yayi baya-baya zai fadi Allah yasa ya dafa kujera yana tsayawa.
Da sauri Ummah ta kashe TV din tana zama, a hankali ta daga ido ta kalli Dad tana fahimtar yanayin shi.
Cikin wani irin yanayi Dad ya mik’awa Ummah wayansa yana cewa. “ Ki kashe.”
Ta karba tana kashe wayan ta ajiye a gefe.
Tashi yayi da zummar tafiya dakinsa, ba tare da Ummah ta ankara ba taji shi timm ya fadi, da gudu ta nufa gurin shi tana kiran sunan shi tana neman agaji.
Asabe ta fito da sauri jin kukan Ummah, bata tsaya wata wata ba ta nufi waje dan kiran security su kai shi asibiti.
*MUMMY POV*
Ita dama wayanta yana hannunta, hakan yasa ta kalla abunda ke wakana a duniya, ta saki baki tana kallo tana mamaki.
“ Lallai ana bura uba a duniya!!!” Ta kyalkyale da dariya tana cewa. “ Ita nata asirin ya tonu ni yanzu nawa ne ke kan hanya, dan tabbas sai wancan dan iskan ya fallasa kan cewa ni na aike su”
Radiya ta fito da wayan a hannunta da sauri tana cewa. “ Mummy kinji me yake faruwa kuwa?”
“ To ni ina ruwana, ita ce bata iya wasa ba”
“ Amma Mummy abun ba kyau din gani”
Har Mummy zata yi magana suka ji fitan motoci, da sauri Radiya ta lek’a window, Mummy na tambayar ta. “ Waye ne?”
“ Mummy ban ga kowa ba amma kamar dai Dad ne dan security’s din shi ne”
Suka danyi shuru kafin wayan Mummy ya soma ringing, ta kalli Number tana dauka: ta cikin wayan aka ce. “ Hajiya idan za ki iya gudu ki gudu, dan yaron nan ya kira sunan mu, ni yanzu ma nake shirin bari k’asar, kuma nasan suna hanyar gidanki yanzu.” Ya kashe wayan.
Mummy ta mik’e tsaye tana fadin. “ Na tafasa na kone, wai me nayi ne haka na shiga uku na lalace, masifa kan masifa, daga wannan sai wancan….” Ba ta kai ga karasawa ba suka ji jiniyar motar yan sanda.
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 33*
*BOOK TWO*
Mummy ta mik’e tsaye tana faɗin. “ Na tafasa na ƙone, wai me nayi ne haka na shiga uku na lalace, masifa kan masifa, daga wannan sai wancan….” Ba ta kai ga karasawa ba suka ji jiniyar motar yan sanda.
Kusan a tare suka kalli junan su, Radiya na fad’in. “ Mummy police fa”
“ Radiya naji” Tayi saurin shigewa ɗakinta ta rufe k’ofa, Radiya ma ta mara mata baya.
Wani daga cikin security’s din ne yazo yana tambayan police din ta turanci. “ Sir akwai matsala ne?”
Police din ya mayar masa ta harcen turanci. “ Munzo kama Hajiya ce”
Da mamaki security ya kuma cewa. “ Sir matan uku ne bansan wanne kake nema ba, sannan kuma mai gidan bayi da lafiya an tafi dashi hospital, and karamin alhaji ma baya nan, kaga ba damar kama daya daga cikin mutanen gidan”
Jinjina kai police din yayi kafin ya ce. “ Aikin mu ne, zamu jira su har su dawo kafin mu tafi da mai laifin, amma ina da tabbacin shi SSS ya sani” ya ciro wayansa yana dannawa Saif kira, har yayi ringing biyu bai dauka ba.
Security ya ce. “ Sai dai ku jira shi, amma gaskiya bazamu iya bari a fita da mutum a gidan nan ba da sanin daya daga cikin Alhajin ba”
“ Is owk zamu jira” ya koma motansu ya zauna, sauran suma suka zauna dan jiran Saif ko Dad.
Security ya koma cikin y’an uwansa suna magana.
Duk yanda akaso a dawo da numfashin Dad ya zama dai-dai abun ya fuskara, har ya kai da suna shirin kai shi ICU kafin aka ci nasara ya dawo amma yana daukewa ya dawo.
Ummah duk tabi ta rikice ta rasa me yake mata dadi, gashi a hospital din ma maganar akeyi ana nuna videos din, duk kunya ya dame ta taji kamar ta rufe fuskarta.
Ta kira number Saif yafi a kirga amma baya d’aukawa, gashi bata da number Jon, dama na Sageer ne kuma shi ma yana kwance ba lafiya.
Dago kai tayi taga Security da yake tsaye kusa da ita, kafin ta ce.” Kana da number Jon ne?”
Cikin girmamawa ya ce. “ Sir Maa” yana ciro wayansa ya kira Jon, bugu daya ya d’auka; sai ya mik’awa Ummah yana komawa gefe ya tsaya.
Ummah ta ce. “ Ina Saif ne ina ta kiransa baya d’aukan waya?”
Jin muryan Ummah ne yasa Jon cikin girmamawa ya ce. “ Maa yana hospital ne Hajiya ce ba lafiya”
Da sauri Ummah ta ce. “ Subhanallah wani hospital?”
Jon ya fada mata sunan hospital din yana kallon Saif wanda ya zuba masa ido, Ummah ta ce. “ Ta wani bangare kuke muma muna ciki”
Kafin yayi magana Saif ya karbi wayan, dan duk wayan da suke yi yana ji, sai ya ce. “ Ummah waye ba lafiya?”
Jin muryan Saif ne yasa ta ce. “ Dad dinka ne”
“ Dad!!!” Ya maimaita sunan kusan sau uku kafin ya ce. “ Me ya fari da shi?”
Ummah ta ce. “ Baka san me yake faruwa bane?”
“ Ummah me yake faruwa? I don’t know fa”
“ Kuna ta ina?”
“ Emergency”
“ Tam.” Ta kashe wayan.
Saif yabi Jon da kallo yana cewa. “ Me yake faruwa ne?”
Jon ya sunkuyar da kai ya ce. “ Sir videos akayi posting a social media na Hajiya Mom”
“ Videos!! Na me haka? Sana’a take yi ne ko me?”
Jon ya sake sunkuyar da kai, dan gaskiya abun da nauyi bazai iya fada masa ba, Saif ya kuma cewa. “ Nuna min videos din”
“ Sir datana ya k’are dazun”
Ya bishi da kallo dan ya gane baya son ya nuna masa ne, ya jinjina kai yana kallon daya daga cikin security ya ce a d’auko masa wayansa a mota.
Bayan security ya bashi ne ya kalli missed calls kusan ashirin, dana Jannah dana Ummah dana Ammar, sai kuma wasu daga cikin friends nasa.
Da mamaki yake kallo dan wasun sun shekara basu yi waya ba, number Jannah ya fara kira, bugu daya ta dauka.
“ Hello”
Tayi shuru tana jin shi, ya sake maimaitawa, kafin ta ce. “ Ina wuni?”
“ Lafiya, ya Baffa da Inna?”
“ Kowa lafiya” shuru ya sake rufe zancen nasu kafin ya katsai da cewa. “ Kinyi shuru? Naga missed calls naki ne, hope lafiya?”
Numfashi ta sauke tana fad’in. “ Dama…”
“ Uhm, go ahead me ya faru?”
“ Dama… dama.. uhmm abu nakeso”
Ya saki murmushi yana samun guri ya zauna wajen waiting bench, kafin ya ce. “ Wani abu kenan?”
Sai da taja numfashi kafin ta ce. “ 3m”
Yayi shuru yana nazarin me zatayi da shi haka, kafin ya ce. “ Turo Acc naki”
“ Nagode sosai.” Ta fada tana kashe wayan, nan da nan ta rubuta ta tura masa, yana shigowa ya gani, Opay dinsa ya shiga ya mata transfer.
Number Ammar ya dannawa kira, yana dauka ya fara cewa. “ Saif ya ake ciki? Ya har yanzu baku ce a goge ba abun sai yawo yake yi fa”
Da mamaki Saif ya ce. “ What’s wrong?”
“ Kamar ya? “
“ Ban san me yake faruwa ba, tun da na koma gida na kawo Safeera hospital ba lafiya”
Ammar ya ce. “ Kana nufin baka san komai ba?”
“ Idan na sani zan tambaye ka ne? Ka fadamin me yake faruwa dalla Malam”
“ Videos din Mom ke yawo a social media, babu inda baije ba, Instagram, Facebook, twitter, tiktok har WhatsApp duk sun je”
“ Videos din na menene? Sana’a take yi yayi trending ko kuwa tasa an daure mutum ne?”
“ No videos din banza ne, like Sex ana mata videos ita da wani guy”