Sashe 22
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai ba nan gizo ke sak’ar ba, wata rana yazo da daddare zai nemi ni nan na bijire nace sam ban yarda ba, ai kuwa mukayi kaca-kaca dashi daga karshe ya koreni daga gidansa, ni kuma na fita ba tare da na sake waiwayarsa ba, ban tsaya ko ina ba sai nan gidan.
Zuwana nan gidan na fara sabon rayuwa na manta da wani Saifullahi, sannan na manta da ina da wasu iyaye, na zabi na killace kaina daga aikata zina, na zabi wahala sannan na gane illan rashin bin umarnin iyaye da biyewa saurayi.
Ta karashe bada labarin tana kuka mai cin rai, Safeera ma tana tayata kukan.
Cikin kuka Safeera ta ce. “ Jannah kin biyewa saurayin da bashi da tabbas.”
“ Safeera nima nasan nayi dana sani, kuma na gane kuskure na duk da a kurarran lokaci na gane.”
Goge hawayen fuskarta Safeera tayi tana matsowa kusa da ita ta rike hannunta ta ce. “ Ba’a kurarran lokaci bane Jannah, za ki iya gyara goben ki idan kin amince.”
“ Safeera ta ya?.”
“ Ki koma ga iyayenki, ki nemi yafiyarsu, ina mai tabbatar miki cewa Saifullahi zai dawo yana rokonkj gafara.”
“ In Sha Allah.”
Kafin Jannah ta ce. “ Safeera saura naki.”
Dariyar da yafi kuka ciwo Safeera tayi tana bata labarinta tas tun daga farko har karshe.
Jannah tayi kuka na fitan hankali jin labarin Safeera sai taga nata bakomai bane, ashe nata nafila ce.
Kafin ta dubi Safeera da ta zuba mata ido babu hawaye a fuskarta ta ce. “ Safeera ina Haris?.”
“ Hmm!! Jannah da zanga Haris da nafi kowa murna a duniya.”
“ Lallai Allah yana jarabtar bawa dan ya gwada imanin shi, duk da irin halin da kika shiga amma kinki ki aikata abunda ba dai-dai ba.” Jannah ta fada tana jinjina kai.
Sai kusan karfe shida na safe suka kwanta bayan sunyi sallah.
Haka rayuwar Jannah da Safeera ya cigaba da tafiya har kusan na watanni uku, sun koma tamkar yan biyu, duk inda kaga daya zaka ga daya, rayuwarsu abun sha’awa, maza sun musu tallan kudi dayawa dan su bada kansu amma sunki.
Ana haka ne wata rana Jannah ta fita da sassafe zuwa wanke wanke, Safeera kuma tace ta gaji yau.
Tana sanye da hijab ja wanda kanshi ya kode yayi datti sosai, ta fito wajen gidan tana tsaye, wani motoci uku suka tsaya a gabanta.
Wani mutum ya fito ya tsaya a gabanta ya kare mata kallo kafin ya ce. “ Aiki zaki mana.”
“ Nawa zaka biya ni?.”
Murmushi ya mata kafin ya ce. “ Kuɗi ba matsala bane muddin za ki yi aiki me kyau.”
“ Sai naji nawa za’a bani kafin zan yarda, idan naji ingancin kafin zan yi.”
“ Zan baki 5m.”
“ Yayi kaɗan.”
Da mamaki ya kalli yarinyar, yarinya karama da son kudi, amma sai ya ce. “ Iya shi zamu baki idan kin yarda muje idan baki yarda ba kuma shikenan.”
“ Ka ƙara wuta ban yarda ba.” Safeera ta fada tana ta dube duben Jannah dan yau ta dade, kuma ga bonanza yazo na kudi ta tabbata idan ma sukayi aikin aka biya su shikenan su da talauci ya kare, idan aka biyasu 10m zata bawa Jannah 5m itama ta dauki 5m, tana tsaye har mutumin ya dawi yace zasu bata 10m ganin Jannah bata dawo bane yasa ta ce bari taje idan ta gama aikin sai ta dawo.
*Idan baku manta ba nan ne farkon labarin ko?*
*_~MUN DAWO DAGA LABARIN SAFEERA~_*
Safeera ta karashe bawa su Labarinta tana kuka, ba ita kadai ba har Dad sai da ya goge kwalla, Ummah kam kuka take sosai, Umma Fauziyya sai da ta tausayawa Safeera.
Saifullahi kam shuru yayi ya zuba mata ido, ga tunanin Jannah da yake yi, dan tabbas ita ce ba wata ba.
A hankali ya tashi ya fice daga dakin jikinsa a sanyaye.
*Ku suburbuda min comment🥹*
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Comments section
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 23*

A hankali ya tashi ya fice daga d’akin jikinsa a sanyaye, tana mai bin shi da kallon tuhuma.
Dad ya mayar da duban shi zuwa ga Fauziyya yana cewa. “ Kin ce kina nema na.”
Saurin girgiza kai tayi, dan yanzu ko ta tona asirin babu abunda zai faru, dan Dad bazai aureta ba tunda yaji labarin yanda take, kafin ta ce. “ Dama…dama zuwa nayi na muku Allah ya tsare gaba.”
Dad ya amsa da. “ Amen.”
Da sauri Umma Fauziyya ta fita ko bari su hada ido da Safeera batayi ba, a waje ta tarar da Saif yana zaune ya zabga tagumi, da sauri ta fice daga hospital 🏥 din.
*Some hours later*
~bayan wasu awanni~
Dad na zaune a falo shi da Ummah, suna dan taba hira.
Dad ya ce. “ Amina, a labarin da yarinyar nan ta bada baki dauki wani abu ba?.”
Shuru Ummah tayi kafin ta ce. “ Gaskiya ban fahimci komai ba, kuma….” Shuru ta danyi kafin ta daura da cewa. “ Kaman Saifullahin da ta bada labarin shine Ɗanmu ko?.”
Murmushi Dad yayi tare da jinjina kai ya ce. “ Nima haka nake gani, ance ba kyau zargi amma ni fa ina zargin Ɗanmu, kenan yaron nan ya dade yana aikata ba dai-dai ba bamu sani ba?.”
“ Hmm! Amma Saif bazai yi haka ba.”
“ Ku iyaye Mata ba’a isa a faɗi laifin Ɗanku ba, ai shikenan nikam zanyi bincike dai-dai gwargwado na har sai na gano gaskiya.”
“ Allah ya taimaka.”
“ Amen idan da gaske kike.”
Shuru Ummah tayi dan yanzu laifin zai dawo kanta, Dad ya ce. “ Nikam ina ƴan uwanki ne?.”
“ Su waye kenan?.” Ummah ta tambaya da mamaki a fuskarta.
“ Hafsat da Maimuna.”
Tabe baki Ummah tayi tana cewa. “ Ka kirasu mana ai naga matanka ne, kai zaka fini sanin inda suke.” Daga haka ta tashi ta nufi bangaren ta dan dama yau ba girkin ta bane na Mom ce.
*MOM POV*
Tana zaune har aka gama checking din result nata likitan ya dawo, da ido tabi shi har ya zauna yana mik’a mata tagardan gwajin ya ce. “ Hajjaju nayi iya bincike amma ban fahimci komai ba, na miki general check up amma Wallahi babu abunda yake damun ki.”
A hargitse ta ce. “ Taya zaka ce babu abunda yake damuna duk irin tsutsar da nake fitarwa ta gabana, duk nawan da kakeso ka fada zan biya dan asan me yake damuna.”
Murmushi likitan yayi kafin ya ce. “ Hajjaju sai dai ko zakije wani asibitin tunda ni na gagara.”
Wata tsaki ta buga tana daukar jakarta ta fice tana cewa. “ Aikin banza dama baka san komai ba.”
Wani asibitin ta nufa amma amsa daya aka bata cewa lafiyarta kalau, haka ta jera hospital kusan biyar amma duk sakamakon iri daya, daga nan ta nufo gida lokacin karfe bakwai na dare.
Tana saka kafarta a falon Dad dake zaune ya rufe hanci yana mikewa tsaye yana kallonta ya ce. “ Wai ke wani irin wari kike yi ne?.”
Shinshinar kanta tayi taji bakomai kafin ta dago kai ta ce. “ Nifah bana jin warin komai, sai dai ko hancin ka.”
Bai ce komai ba ya fice daga parlon yana komawa part nasa har lokacin ya rufe hancinsa.
Zama Mom tayi tana nazari a fili ta furta. “ Ko dai naje gurin boka ne gobe? Hmmm haka ma za’ayi goben zanje.”
*MUMMY POV*
Ko da suka gama waya da Fauziyya bacci ne ya d’auke ta mai dadi, tana farkawa Radiya ta shigo tana fadin. “ Mummy ashe Saif bai mutu ba, hatsari kawai sukayi, kuma Sageer ne yaji ciwo aka harbe shi.”
A zabure Mummy ta mike tare da cewa. “ Bai mutu ba?.”
Cike da murna Radiya ta ce. “ Eh Wallahi Mummy bai mutu ba, zo kiga hamdalan da nakeyi.”
“ A garin ya? Kenan basu kashe shi ba? Kudina kawai suka karba amma babu abunda suka min.” Ba tare da tasan maganar ya fito sai da taji Radiya na cewa. “ Mummy da sa hannunki a ciki ko?.”
Da sauri ta ce. “ A’a naji dazu kince ya mutu ne shiyasa abun ya bani mamaki.”
Murmushi Radiya tayi ta ce. “ Ok shikenan anjima zanje duba Matar tasa dan tunda tazo banje ba.”
“ Nima banje ba kinga sai muje tare.”
“ Ok Bye mummy.” Daga haka Radiya ta koma bangaren ta.
*SAFEERA POV*
Tun bayan da suka dawo daga asibiti bata sake saka shi a ido ba, a d’aki ya barta bai dawo ba gashi yanzu har kusan karbe tara na dare, a fili ta ce. “ Ko ina ya shiga?.”
Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi d’akinsa, duk da ranta a b’ace amma hakan bai saka taji batason sa ba.
Da sallama a bakinta ta shigo dakin nasa, yana kwance akan gado ya lumshe ido, kallo daya zaka masa ka gane cewa ba bacci yake ba.
Gurin gadon ta isa ta zauna a kan bedside tana cewa. “ Saif tun dazu baka sake duba ni ba.”
Bai kulata ba kuma bai nuna yaji ba, ta cigaba da cewa. “ Ina maka magana amma kayi banza dani.”
“ Ki tashi ki fita ina neman hutu.” Ya fada a sukwane.
Jinjina kai tayi kafin ta ce. “ Amma….” Bata k’arasa ba ya daka mata tsawa a fusace wanda yasa ta mike ba shiri tana nuna kanta da hannu ta ce. “ Ni Saif?.”
*Idona bacci haka na muku typing idan bakuyi comments ba babu abunda zanyi gobe tam🧏♀️*
09027308227
*Sahiba ce✍🏼*