Sashe 29
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 31*
*BOOK TWO*
Fitan shi ke da wuya suka ji muryansa daga waje yana faɗin. “ Dan Allah kuyi hakuri ku min rai.”
Inna ta dafe kirji tana faɗin. “ Mun shiga uku.”
Da gudu suka yo waje ita da Jannah.
Gardawa sun zagaye Baffa a tsakiya, wani tuluki daga gefe yana sanye da blue din shadda, gajere kallo daya zaka masa ka hango munin shi, ya ce. “ Ko ka biyani kudina ko na sa a kashe ka kuma na auri diyar taka tun da dai matata ce, dan na biya sadaki.”
Jannah ta ware ido, wace diyar tasa kenan?, dan ita a iya saninta Baffa ita kadai ya haifa.
Inna ta ce. “ Malam me ya maka kake cewa zaka kashe shi dan Allah?.”
“ Da ke ai naga aka ci kudin, dan haka ko ku biyani kudina ko na saka a miki dan banzar duka.”
Baffa da yake hada zufa ya ce. “ Alhaji kamin rai, kudinka zan sa a biya maka nan da anjima.”
“ A gidan uban wa zaka samu ka biyani, Gunda ku masa dan banzar duka.”
Duka suka shiga kai masa, Inna na kuka Jannah na kuka, suna bashi hakuri amma yaki hakura, Jannah ta durkusa a gaban shi tana fadin. “ Dan Allah ka bar shi zan baka kudin ka.”
Ya kare mata kallo yana cewa. “ Ke!!! Da gashin kanki zaki biyani?.”
Ta dubi yanda Baffa ke ihu Inna ma ke kuka, ta juyo da sauri tana cigaba da cewa. “ Nawa ne kudin zan baka na rantse.”
Kallon baki da hankali ya mata kafin ya ce. “ Million uku yaci a hannuna dan zai auramin diyarsa, kuma yaki.”
‘ Million Uku!!!.’ Jannah ta fada a ranta kafin a fili ta ce. “ To zan biya amma dan Allah ku barshi dukan ya isa.”
“ Yaushe zan zo na karba to?.”
Shuru tayi kafin ta ce. “ Gobe da safe.”
Jinjina kai yayi, ya daga hannu yana cewa. “ Ku barshi ku zo mu tafi, gobe da safe zamu dawo mu karbi kudinmu, idan kuma bata bada ba ku yanka shi.”
Su ka dakata da dukan suna bin bayan Alhajin.
Inna ta isa da sauri tana rike Baffa ita da Jannah, idanun Baffa sunyi tsulu tsulu tsabar azaba, fuskarsa ya sha duka, ta kafarsa kam har da dan fashewa, Inna ta goge hawayen fuskarta ta ce. “ Yanzu dan Allah me haka kayi.”
Ya kalle ta yana magana a hankali. “ Ku shigar dani ku dafamin jikina.”
Inna ta ce. “ Jannah rike shi mu shigar da shi.” Da kyar suka iya kai shi kan taburma, duk nishi suke.
Jannah ta ce. “ Haba Baffa, tunda kana da kudin ka kawo a bashi kawai.”
Murya irin na wad’anda suka daku ya ce. “ Ko kashe ni zaiyi sai dai su kashe ni.. amma kudina.. ba.. zan.. bada ba.. Allah ma ya rufa asiri bai san motan nawa bane, da fasawa za suyi, masu hassada sun cika gari ta ko’ina.”
Inna tayi murmushin takaici ta ce. “ Kudinsu fa kaci, kuma ni bansan yaushe kaci har million uku ba Wallahi.”
“ Ina zaki sani tunda ban kashe miki ba.” Ya fada yana cije baki ya daga hannu da kyar, Jannah ta ce. “ Sannu Baffa.”
“ Babu wani sannun da zaki min, ke ne kika jawo, da kin auri Alhaji Saifullah ai da yanzu ba zancen ake ba.”
Jannah ta sunkuyar da kai tana fadin. “ Baffa ni fa ba son shi nake ba, kuma bazan iya auren shi ba.”
Pillow da ya daura hannunsa a kai ya buga mata yana fadin. “ Sai goben idan sun dawo su kashe ni, amma kudina kam bazasu yi ciwon kai ba, ke kuma.” Ya nuna Inna, yana cigaba da cewa. “ Ko na mutu a binne ni da kudina.”
Ya kalli Jannah ya ce. “ Idan Alhajin yazo sai karki yarda ki aure shi, kin ga idan na mutu alhakina a kan ki, yar kusun uwa.” Ya karashe yana taba goshinsa da ya kumbura tim.
*SAFEERA POV*
Tana zaune a falo ta dukunkule a kan kujera tayi shuru, Saif ya fito daga dakinsa sanye da kayan barrister zai tafi aiki, ta daga kai ta kalle shi tana saukewa.
Ya iso gurinta yana cewa. “ Sweet pie zo muje ko.”
Girgiza kai tayi tana cewa. “ A’a zanyi bacci ni.”
Ya zuba mata ido yana karantar yanayin ta, kafin ya tashi ya sumbace ta a goshi ya ce. “ A mana addu’a zamu shiga.”
Bata kulasa ba ta kwanta akan kujeran tana lumshe ido, ya dade yana tsaye kafin ya sauke numfashi ya fita, ta baya ya rufe kofar ya tafi da key din.
Bacci tayi sosai har na awa uku, kafin ta farka duk jikinta zufa, tana kallon cikin falon a razane, a hankali ta ce. “ Mama.”
Sai ga hawaye zurr sun zubo kamar an bude famfo, kuka ta fara tana tunawa da yan uwanta. “ Ko ina suke? Ko sun ci abinci ko basu ci ba babu wanda ya sani? Allah sarki Raudah ina ga ni na cuce ki.”
Nan taji kanta ya sara kamar zai fashe, da sauri ta damke kan tana lumshe ido, kusan mintuna biyar tana haka, kafin ta bud’e idon tana tashi ta nufi hanyar fita a falon.
Tana k’ok’arin bud’e k’ofan ta ga an turo kofar, suka tsaya suna kallon juna, sun dade kafin ya ce. “ Ina zaki je?.”
“ Wajen Raudah.”
Yayi shuru yana kallon ta dan shi ya manta ma wacece Raudah din, sai da ya tuna labarin ta kafin ya tuna wacece, amma ai bata san inda take ba.
“ Kin san inda take ne?.”
Ta masa kallon Up and down tana bi ta gefe zata wuce, ya toshe hanyar yana cewa. “ Ina zuwa?.”
Cikin daga murya ta ce. “ Dalla Malam ka matsamin zan wuce, ka wani toshe min hanya.”
“ Yau din kuma?.” Ya fada da mamaki, dan shi yanzu ya rasa yanayin Safeera din, kafin ya ce. “ Ina zakije idan kika fitan?.”
Shuru tayi kamar tana tuna abu, ta dan nutsu a hankali tana tuna rayuwarta na baya, ta dafe kai da sauri ta furta. “ Wayyo kaina.”
Da sauri ya sake jakar hannunsa yana riketa, ya ce. “ Safeera!!!
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA*

*Page 32*
*BOOK TWO*
Shuru tayi kamar tana tuna abu, ta ɗan nutsu a hankali tana tuna rayuwarta na baya, ta dafe kai da sauri ta furta. “ Wayyo kaina.”
Da sauri ya sake jakar hannunsa yana riƙeta, ya ce. “ Safeera!!!.” Ta ɗago ido ta kalle shi tana rufewa.
Jijjiga ta ya soma yi, duk ya fice a hankalin shi, ajiye ta yayi ya nufi fridge da gudu yana ɗauko ruwan sanyi yazo ya fara yayyafa mata.
Amma shuru babu alaman zata tashi, wurgar da ruwan yayi ya ɗauke ta zuwa waje da gudu; Jon yana kallon shi yayi hanzarin buɗe mota, shiga yayi da ita a hannunsa, shima Jon ya shiga yana tada motan, mota biyu na security suka bishi dan Dad yace duk inda zaije suna raka shi har sai asirin wadan da suka kai masa hari ya tonu.
Suna zuwa aka karbe ta emergency ana shirin shigar da ita, shima ya biyo bayan su da zummar zai shiga, Dr ya dakatar da shi.
A harzike ya ce. “ Dalla malam matsamin na wuce.”
Dr ya sunkuyar da kai ya ce. “ Sorry to say Sir amma bazaka shiga ba, idan kuma kai zaka mata aiki go ahead.”
Masifa ya soma yi a gurin, Dr bai kula shi ba ya shiga emergency din, Jon ya iso yana fadin. “ Sir ba zaiyu ka shiga ba.”
Wani kallo ya jefa masa wanda yasa shi ma yaja gefe yana bin shi da ido, idan yace Uban gidan nasa baya bashi mamaki karya yayi, amma wasu abun da yake kamar ba shi ba, idan yana tare da Safeera zaka rantse ransa ce, idan kuma yana tare da Jannah zaka ce rayuwarsa ce.
Jon ya sauke numfashi yana cigaba da kallon shi.
*MOM POV*
Yau ne ranar karshe da suka yi da Ashiru cewan zata bashi kudin, amma duk abunda ta samu bai wuce 5m ba, kuma ta tura masa dazu sai dai tana ta kiran number shi baya shiga.
Gashi yanzu warin da take yi ya wuce na hankali, dan har ya kai da maruru ne ke fitowa daga farjinta yayi diwa, idan ta fasa kuma sai warin tsiya, amma duk da haka bata bi ta kai ba.
Ita matsalan ta daya shine kar Ashiru yayi posting din videos din.
Gashi dan iskan bokan bayi da lafiya, taja tsuki tana hada zufa, ta sake danna number Ashiru a sau ba adadi, amma amsa daya ce shi ne Switch Off.