Sashe 12
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A furgice ta d’ago kai tana kallon shi, ta kalli Saif wanda shima ita yake kallo da zallan kauna dan shi hankalinsa kwance, sai ma sanyin da yaji a ransa a abun yazo masa da sauki, dan shi a ganinsa ai an masa adalci ne.
Zama Bappa da Dad suka yi a kan carpet, Dad ya kalli Ammar da Saif ya ce. “ Ku zauna.”
Da sauri Saif ya zauna yana murmushi, kallo daya Dad ya masa yana dauke kai, Ammar ma ya zauna.
Ummah da al-ajabi ya gama cike ta ne ta ce. “ Alhaji ba tare da bincike ba za’a daura aure?.”
“ Amina kiyi shuru a nan, ko bakiji shi yace ya gama bincike bane?.” Dad ya furta a dan fad’ace.
Shuru Ummah tayi bata sake cewa komai ba.
Nan Dad ya bud’e taro da addu’a, kafin suka yi niyar daura aure, Dad ya dubi Saif yana cewa. “ Kawo sadaki?.”
Hannu ya saka a aljuhu yaji bakomai, tashi yazo zaiyi Dad ya dakatar dashi yana cewa. “ A nan zaka kawo kar ka tashi.”
Shuru yayi yana tunanin mai zai bada kafin ya kalli Ammar, Ammar ya girgiza masa kai alaman bashi da kudi a jiki, zoben hannunsa ya kalla na Diamond 💍 wanda ya siya 5m a Saudi, cirewa yayi da sauri yana mikawa Dad ya ce. “ Shine sadakin.”
Gyada kai Dad yayi kafin ya ce. “ Waye Alwalinta?.”
Ammar ya ce. “ Ni.”
“ Alwalin shi din fa?.”
Bappa yayi saurin cewa. “ Ni zan zama.”
Nan aka daura auren Saifullahi da Safeera akan sadaki zoben diamond, sannan aka shafa fatiha aka raba goro da minti.
Saif kamar ya zuba ruwa a k’asa yasha yake ji, yayin da Safeera ta zama mutum mutumi, dan har yanzu bata yarda da cewa ta zama matar aure ba, matar auren ma na Saif wanda sai da ya kwanta da ita yaji yanda take kafin ya aure ta, hakan yasa ko motsi ta gagara daga zaunen da take akan tiles.
Ummah ta kalli Saif wanda idanunsa na kan Safeera yana murmushi, kafin taga Safeeran, ajiyar zuciya ta sauke ta nufi d’akinta.
Tashi Dad yayi ya nufi shi ma part nasa, Bappa ya dubi Saif ya ce. “ Dan Allah Ango ku bani kudina da motana.”
Nuna Ammar yayi idanunsa nakan Safeera yana mikewa ya ce. “ Shi zai baka.” Ya tashi yaje gurin ta, shima ya zauna yanda ta zauna yana zuba mata ido.
Bappa ya kalli Ammar, Ammar yana sakar mishi murmushi.
Saurin dauke kai yayi a ransa yana fadin. ‘ Na shiga uku, ashe shi zai bada kudin, na boni yanzu duk rashin kunyar dana masa ashe shine mai arzikin ba wancan dak’ik’in ba.’ Ya fada yana dafe goshi, kafin ya kalli Ammar yana cewa.
“ Yarona ka tausayawa bawan Allah ka taimaka ka agaza kaji kaina ka bani kudin.” Yana hade hannayensa ya fad’a.
Dariya Ammar ya masa yana cewa. “ Mai na sama yaci da zai bawa na k’asa?.”
Kamar Bappa zaiyi kuka ya ce. “ Wallahi arashi ne irin na harce, kayi hakuri.”
D’aga kafad’a yayi yana tashi ya nufi kofa, ya juyo ya kalli Saif wanda ya koma kamar gunki shi da Safeera, girgiza kai kawai yayi yana cewa. “ Nikam na tafi zanje nayi aiki kafin na dawo.”
Hannu kawai Saif ya d’aga masa, da sauri Bappa ya bi bayan Ammar har yana shirin fad’i, har gurin mota suka je Bappa yana bashi hakuri akan ya bashi kudin yana da abunda zai yi.
Sai da ya wahalal da Bappa kafin ya bude gurin mai zaman banza yana ciro envelope ✉️ wanda ciki yake cike da kudi guda biyu ya mika masa, sai zai karba sai ya janye, haka ya masa har sau uku kafin ya bashi, kamar Bappa zai haukace haka yayi lokacin da ya karba, yana bud’e yaga key din mota.
Ihu Bappa yasa wanda yasa hankulan security’s ya dawo kansa, kare da suke kulle suma suka haushi kamar zasu fito.
“ Nagode Allah ya k’ara kawo irin wannan abun, Allah yasa ta sake b’ata na nemo ta, ai wannan batar nata ni yayi wa rana Aradu, huuuu huuuu huuuu, yau sai nayi wata amarya billahil’lazi, na more nima chass.” Kafin ya kalli Ammar yana cewa.
“ Tsaya tukun, ina motar mukulli kawai ka bani ashe.”
Shiga motarsa Ammar yayi yana nuna Sageer ya ce. “ Kaje ka bashi key din zai dauko maka motar.” Da haka ya zuge glass yana fita daga gidan.
Zuwa gurin Sageer yayi yana cewa. “ Saura kai.” Kafin ya bashi key din yana cewa. “ Motar zaka bani.” Karban key din Sageer yayi yana kallo kafin ya ce. “ BMW.” Wani get Sageer ya nufa Bappa na biye dashi.
Jerin motoci ne har guda goma a gurin, inda BMW yake Sageer ya nufa yayin da Bappa ya tsaya a dai-dai gurin GLK yaki matsawa.
Juyawa Sageer yayi ya kalle shi yana cewa. “ Baba ga naka nan ka k’araso.”
Girgiza kai Bappa yayi yana nuna na gabansa ya ce. “ Wannan nakeso ba wancan ba…
*Kun fara rage comments ko🥸*
*DR TEEMERH✍🏼*
15-
💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_
*Na*
*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 15*
Juyawa Sageer ya yi ya kalle shi yana cewa. “ Baba ga naka nan ka k’araso.”
Girgiza kai Bappa ya yi yana nuna na gabansa ya ce. “ Wannan nakeso ba wancan ba.” Murmushi Sageer ya yi dan shi a tunaninsa tsufa ke damun Bappa, hakan yasa ya ce. “ Baba wannan yafi kyau akan wancan din ai.”
“ Kai yaro gar nake ganin ka, ina ganin zabgegen mota kace wai wancan dan karamin yafi kyau.” Cewan Bappa yana shafa GLK din.
Dan mamaki Sageer ya ke kallon shi, dan shi tun da yake bai taba ganin mai son duniya irin Bappa ba, ko a labari ko film, sai gashi yau a zahiri kuma a gabansa.
Rufe bakinsa yayi fuska ba annuri ya tsare ya dakawa Bappa tsawa yana fadin. “ Kai!!!! Ka bar nan idan na fito maka da naka sai ka karba, tsabar son duniya a baka mota na over a million amma kana son na gaba da shi.”
Shuru Bappa yayi yana kallon shi har ya gama kafin ya ce. “ Kaje gurin ubangidan naka ka tambaye shi waye ni a gurinsa? Ni din nan da kake gani Sirikinsa ne atoh diyata ya aura.”
Sageer ya dube shi me kyau yana fadin. “ Yaushe ka zama sirikinsa? Malam zaka fita daga nan ko sai na fitar da kai da karfiin tsiya?.”
Kama kugu Bappa ya yi tare da cewa. “ Yooo fitar da ni ta tsiyar.” Bai gama rufe baki ba Sageer ya bude karnukan da suke cikin cell a kulle su biyar.
Haushi suka fara suna yiwo kan Bappa, a haukace Bappa yasa ya gudu yana fita daga gurin, ihu yake yana gudu tsakaninsa da Allah yana magiyar a taimake shi.
Ya tusa ta a gaba ko gifta ido bayayi, sanyayyen murmushi yake sakar mata.
Yana dar-dar haka ya daura hannunsa akan nata, wanda hakan yasa ta juyo da fuskarta zuwa gare shi ta zuba masa sexy eyes dinta.
Kame-kame ya fara dan ya rasa me zai ce mata, janye hannunta tayi daga nasa tana tashi tsaye, da sauri shima ya tashi yana mata murmushi ya ce. “ Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida.”
Harara ta banka masa tana jan tsiririyar tsuki, annurin fuskarsa ce ta sauya ya ce. “ Akwai wani abu ne?.”
A zafafe kamar zata hayo kansa ta soma cewa. “ Sakina zaka yi malam, dan bazan zauna da mazinaci ba dan bansan bayan ni mata nawa kayi mu’amala da su ba.”
Kallon ta yake cike da mamaki ya dafa kafadarta yana cewa. “ Kar ki kawo zargi cikin auren mu, dan zai iya rusa duk wani farin ciki.”
Buge hannayensa din tayi tana cewa. “ Kai kake daukarsa aure, amma a nawa ganin wannan ba aure bane.”
“ Eh naji koma me zaki iya cewa amma ba yanzu ba hilis, mu wuce bangaren mu kafin mu koma gidanmu.”
Bud’e baki tayi da niyar yin magana suka ji ihun Bappa, kallon juna suka yi kafin da sauri Saif ya nufi kofa tana biyo shi suka fita da sauri.
Ihu Bappa yake zubawa tsakaninsa da Allah yana yiwo kan su, ganin karnuka ne yasa Safeera zurma ihu tana dalewa bayan Saif, Bappa kuma ya rungume shi.
Dariya Sageer yake yi yana dakatar da karen ganin ubangidan nasa ya fito, security’s da suke tsaye ya saka suka bayar da karnukan zuwa cell, kafin ya iso gurin su.
Dariya Saif yake kamar cikinsa zai fashe, duk sun wani mamaye shi ba damar ya d’aga k’afa.
Sageer ne ya taba Bappa yana cewa. “ Baba ka sauko mana.”
Har hawaye sai da Bappa yayi kafin ya saki Saif yana kallon Sageer ya ce. “ Aniyarka ta bika, baki mai bakin aniya, kai da ganin haske a rayuwarka ya k’are, makiri.” Ya karashe yana goge hawayen fuskarsa.
A hankali Safeera ta sauka daga bayan shi tana sunkuyar da kai, ta gefe Saif ya ganta yana dariya, Sageer na fadin. “ Bakinka bazai bini ba Wallahi.”
Duba hannunsa yayi yaga ba kudin, wani ihu ya kuma kurmawa yana cewa. “ Kudinaaaaaa.” Dariya Sageer ya masa yana cewa. “ Gashi nan.” Ya mika masa, da sauri ya karbe yana cewa. “ Muje ka bani ko wani mota ne ma ni zan tafi.”
Sageer ya ce. “ Ai Baba baka iya ba sai na koya maka.”
Hararan shi yayi yana cewa. “ Ni din nan da kake gani tsohon driver ne, ko wani irin mota na iya tuk’awa ba manual ba, ba Otho ba, kawai muje ka bani motana.” Da haka suka wuce Sageer na cigaba da neman tsokanan Bappa.