Sashe 10
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru Safeera tayi tana kallon abun da yake yi tana mamaki, bata yarda ya zauce ba sai da taji yana cewa. “ Ki taimaki rayuwata kizo ki zauna da ni, Safeera kiyi hakuri da duk abubbuwan da na miki nasan ni butulu ne, ni kaina na sani, amma ki taimaka min ki yafe min.” Ya karashe yana kama kafarta.
Ammar kamar yayi kuka ya ce. “ Saif ko dai ka zare ne? Kuka kake yiwa mace? mace fa!!!.”
Bai kula shi ba, ya cigaba da fadin. “ Dan Allah ki yarda ki aure ni.” Ya fad’a yana damke kafafuwanta.
“ Ni?.” Ta tambaya da mamaki tare da al-ajabi.
Ammar ya ce. “ Uhm 😶.” Yana harde hannayensa a kirji.
“ Ni karuwar ce kakeso da aure? Ko ka manta da maganganun da ka fadamin? Cewa kayi wai cutar da kai nazo yi, sannan kace ni ba mutumiyar arziki ba ce, har da cemin anyi asarar haihuwata, sannan ka ce ko iyayena basu bani tarbiya bane, a cewarka ai yaran talakawa ba’a musu halalci sai sun mayar maka da sharri.”
Mikewa tsaye yayi yana fadin. “ Eh eh nasan na fadi haka amma ai…”
“ Amma me Saif? Korana kayi daga gidanka kana fadin ga hanya daga nan har lahira, ko shima ka manta?.”
“ A’a duk a cikin rashin hankalina nayi, kar sanadiyarki na mutu.” Ya fada a wani irin yanayi da bazai misaltu ba.
Gyara tsayuwa tayi tana jinjina kai take cewa. “ Me yasa maza baku da kunya ne? Kai ba kaji kunyar idanuna ba kake cewa zaka iya mutu dan ni? Hmmm to albishirin ka ko da kai ne autan maza to na hakura gwara na mutu ba aure dana zauna da kai a matsayin miji.”
Da kyar ya isa jawo numfashin nasa yana fadin. “ Safeera kar ki min haka.”
A hassale Ammar ya kalle ta ya cewa. “ Ke wai ana rokon ki kina rainawa mutane hankali, har yau Saif ne zai durkusa a gaban mace yana bata hakuri kuma taki, ke wacece da bazaki iya yin yafiya ba, idan ta arziki bai sa kin aure shi ta tsiya zai saka kije kayan ki.”
Kama Ammar yayi yana girgiza kai kamar yaro yana kallon ta yana fadin. “ A’a babu inda zata je, Ammar ni na cuceta koma me tayi zan dauka, amma kar tayi nisa dani.”
“ Kai dalla ka barta ai ba ita ce farau ba, aikin banza da wofi ka dubi yanda ka koma akan wannan yarinyar.”
Kallon Ammar take wanda yake zuba mata banzan kallo me dauke da harara, a ranta ta ce. ‘ wato shi adawa ma yake da ni, kenan so yake na tafi lallai hmm to babu inda zanje kuwa da kai da shi din duk sai na rama abun da kuka min, dan kuna ganina karama yar shekara sha takwas shi yasa kukemin wulakanci ai.’ Murkud’a masa baki tayi tana hararan Saif, kafin ta ce.
“ Shikenan zan zauna da kai, yaushe zaka aure ni din?.”
A bazata maganar ya diro masa, bashi kadai ba har Ammar, Bappa da yake zaune ya mik’e tsaye ba shiri, kamar zai haukace ya ce. “ Arziki har gida, ashe da rabon zanyi kudi, Masha Allah, yawwa idan bata da iyaye ni zan tsaya mata a matsayin uba.”
Kallo daya ta yiwa Bappa tana dauke kai, a zuciya ta furta. ‘ Iyayena ma sun fika hankali ai, duk da jirgi daya ya dibo su amma su akwai dan hankali a tattare da su.’
Maganar Saif ne ya dawo da ita jin yana cewa. “ Yanzu muje a daura auren.” Ya kama hannunta zai tafi, jin bata motsa bane yasa ya juyo yana ganin ta.
“ Sakar min hannu malam, ba makauniya bace ni da zaka min jagora.” Ta fada a kausashe.
Sakin hannun yayi yana kallon ta, kamar mai koyan magana ya ce. “ Me kuma ya faru?.”
Ammar da lamarin ya isheshi ne ya ce. “ Ka komar da kanka kamar yaro akan yarinyar nan Wallahi, Mtsw.”
Saif bai kula shi ba sai ma cigaba da tambayan Safeeran da yayi, bata kuma cewa komai ba ta nufi hanyar fita, da sauri ya biyo bayanta yana cewa. “ Ina zaki je.”
Bappa ma ya mara musu baya yana fadin. “ Ba’a biyani hakkina ba za’a tafi, kudina zaku bani da motana.”
Ammar ya ce. “ Ni zan baka bashi zai baka ba.”
Tun daga sama har k’asa ya karewa Ammar kallo, wani tsuki yaja yana cewa. “ Me na sama yaci da zai bawa na k’asa? Da ni da kai din waye yafi wani arziki? Gwanda shi yana da hasken kudi da kwarjini irin na samu kudi amma kai fa sammakal babu ko daya.”
Dariya kawai Ammar ya masa yana cewa. “ Bismillah ka bishi idan zaka samu.”
Tsuki Bappa yaja yana fita daga falon, Ammar ya mara musu baya yana jinjina al’amarin Allah ta yanda ya jarabce Saif da son Safeera cikin k’ankanin lokaci, yayin da ita kuma take wahalal dashi ta yanda taso.
Yana fitowa ya hango su sun shiga mota, da sauri ya iso gurin yana cewa. “ Saif ina zaka kai ta?.”
“ Aure za’a daura mana yau, dan yanzu ma gurin Ummah zan kai ta…
*TAKU HAR KULLUM DR TEEMERH✍🏼*
13-
💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_
*Na*
*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 13*

“ Aure za’a daura mana yau, dan yanzu ma gurin Ummah zan kai ta.”
“ Ban tabbatar baka da hankali ba sai yau, ashe kai wawa ne, idan kaje sai kace ga matar da zaka aura wanda ka yiwa fyade kenan.”
Runtse idonta tayi tana jin zafin kalmar, kafin ta kalli Ammar tana tana dauke kai.
Saif ya ce. “ Kar ka samu, ai dadin abun ni na mata ba wani bane, kaga kuwa dole ni ne zan aure ta.” Ya karashe yana daga glass din motan, ya tada motan yana fita daga gidan da gudu.
Mota Ammar ya shiga shima ya tada, da gudu Bappa ya shiga yana kallon Ammar wanda shi ma kallon shi yake, bai ce komai ba ya fita daga gudu daga gidan Bappa na masifan cewa ya rage gudu, amma ko sauraran shi bai yi ba sai ma k’ara gudun da yayi.
*UMMAH POV*
Ta gama girkin rana kenan ta dawo falo dan ta huta, wayanta ta dauka tana kallon videos na social media, da labaran abun da yake faruwa.
Sallama aka yi ta daga ido tana kallon kofan kafin ta amsa, shigowa Mom tayi tana rangwada tana wani toshe hanci.
A tsakiyar falon ta tsaya tana fadin. “ Amina kike da suna ko wace.”
Ummah bata ce komai ba sai kallon ta din da take yi, cigaba da cewa tayi. “ Inaso na gargade ki, daga yau sai yau kar ki bari na sake ganin Saif yazo bangaren ki, idan kunne yaji gangar jiki ya tsira.”
Da mamaki kawai take kallon ta kafin ta ce. “ Naji.”
“ Good, dadina da ke kina daukar magana ai, da kinyi musu da na gwada miki ta yanda zaki fahimta ai, banza kawai.”
Murmushi kawai Ummah tayi bata kuma tanka mata ba, sai ma cigaba da danna wayanta da tayi.
“ Ina magana kin mantar dani.” Ta fad’a a tsawace.
“ Hafsat bana son hayaniya ki fice min daga falo.” Cewar Ummah cikin rashin son damuwa.
Kama k’ugu tayi tana fadin. “ Iyeee, lallai wuyanki ya kai yanka, ni zaki kalla kice na fita daga kazantar gurin nan?.”
Tashi tsaye Ummah tayi tana cewa. “ Bazan tsaya ina sa’in sa dake ba, dan bansan me bokan ki ya fada miki ba, sannan inaso in fada miki cewa idan ke da boka kika dogara ni kuma da Allah ne, sannan d’a nawa ne kuma ya dawo gurina da taimakon Ubangiji, saboda haka inaso tun cikin mutunci da kamala ki dice min daga falo kafin na sauya miki kamanni, dan jiya ba yau bane, idan kinci tuwo da miya a kaina jiya yau ko ruwa bazaki sha ba.”
Duk ta rude ganin yanda Ummah ke zuba mata zallan magana, ga kuma tsoronta din da ya kamata na lokaci daya, amma sai ta kafse tana jan tsaki tare da juyawa ta fice a falon.
Nauyayyar ajiyar zuciya Ummah ta sauke a fili tana cewa. “ Yau ni nayi magana har haka?.”
Muryan mai aikinta Asabe taji tana cewa. “ Ummah tura ce takai bango shiyasa kika mayar da murtani.”
Juyawa tayi taga Asabe din tana murmushi ta ce. “ Kina jin mu kenan?.”
“ Hmm Ummah ina jinku duka, Matar Wallahi bata da mutunci ko kad’an, ke da yaronki wai tazo tana miki gargadi fa, Allah ya kyauta kawai.”
“ Ameen. “ Ummah ta fad’a tana wucewa d’akinta.
*MUMMY POV*
Ita bama zama take a gidan ba balle ayi tunanin zata shiga sabgar su, amma idan tana gidan ranar sai kowa yasan Mummy bata fita ba.
Bata zama kullum tana hanyar hotel, yara kanana take kulawa wanda a gida ma sai sun roke sabulun wanka a gurin iyayensu kafin suke yin wanka har su fita.
Akwao wani saurayinta mai suna Shamsu, wanda Fauziyya ta hada ta dashi, a fadarta zai iya kashe Saif, kullum suna tare dashi a hotel, yaro ne karami dan duka-duka shekaransa bazai wuce ashirin da shida ba dan Saif ma zai girme shi.
Amma ta makalewa yaron, shi kuma kudinta yake ci, ita tana tunanin ita kadai yake mu’amala, sai dai bata san cewa yana kula y’an mata dayawa ba, dan idan ta barshi a hotel ta koma gida sai ya kawo wata.
Yau ma a chan ta wuni suka gama cin karansu ba babbaka, karshe ta mika masa kudade masu yawa tana tashi, kafin ta ce. “ Baby nifa kwana biyun nan bana jin dadin jikina, ko kaima kana jin wani abu ne?.”
Girgiza kai yayi yana fadin. “ Nikam klau nake, ko zaki je asibiti ne.”