← Book details Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 39

Sashe 11

Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“ Eh inagani kam.” Ta fada tana daukan jakarta ta nufi kofa tana cewa. “ Sai kuma gobe.”

“ Yawwa Sugar mommy.” Ya fada yana dariya da shi kadai yasan ma’anarsa.

*MOM POV*

Ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa taya zata bullowa al’amarin kwata kwata, wayanta ta dauka ta kira bokanta a cewarta malami.

Yana dauka ya ce. “ Nasan me ke tafe dake, kawai kizo muyi ta ta k’are.”

Murmushi Mom tayi kafin. “ Gani nan zuwa.” Daga haka ta kashe wayan.

Daki ta nufa ta shirya ta zuba kudi a handbag dinta tana fita, motarta ta shige tana tadawa, tana fita motocin Saif suna shigowa.

Direct gurin parking lot ya nufa yana parking, motar Ammar yayi sai nasu Sageer, zagayowa yayi ya bud’e mata jiki na bari.

Kallon shi take dan lokaci guda taji tausayinsa, tunawa da kalan abun da ya mata tayi sai ta bata rai ta fito daga motar.

Kallon gidan tayi kafin ta maida idanunta kan shi, inda yake cewa. “ Muje Safeera.”

Takawa suka fara yi zuwa part din Ummah wanda yake hannun dama, Ammar ya fara mara musu baya shi da Bappa, suna cikin tafiya Bappa ya rage murya yana cewa Ammar.

“ Amma nan gidan bada bulo akayi ba ko?.”

Kallo daya Ammar ya masa tare da fadin. “ A’a da yashi aka yi.”

“ Mtsw illan kula mara kudi ke nan, da shi wannan attajirin ne mai farin anayi ai da yanzu ya bani amsa, amma da ke ance talaka yana fama dama da busheshen talauci ina yaga ta bayar da amsa me kyau.” Bappa ya fada cikin takaici.

Murmushi kawai Ammar yayi ba tare da ya kula Bappa ba, dai-dai lokacin da Saif yayi sallama a falon Ummah yana saka k’afa shi da Safeera.

Amsa musu Asabe tayi tana kallon Safeera wacce ita ma kallon ta take tana tunanin inda ta san fuskar.

Ganin kallon yayi yawa ne yasa Saif cewa. “ Kee!!!! Me haka kin zuba mata mayun ido kina kallon ta, kin santa ne dalla dauke idanunki daga kanta.” Ya fada a tsawace.

Da sauri Asabe ta furta. “ Ayi hakuri Yallabai.” Kafin ta juya ta koma kitchen da sauri.

Da ido Safeera ta bita kafin ta mayar da idanunta kan kofar da aka bud’e.

Ummah ce ta fito jin kamar hayaniya, kallon Saif da tayi ne a burkice ya tada mata hankali, mayar da dubanta ga Ammar tayi taga shi ma a burkice, kafin ta kalli Safeera wacce hankalinta yake kwance, inda Bappa yake ta gani shi ma hankalinsa a tashe.

A dan rude ta iso gurin Saif tana dafa kafarda ta ce. “ Me ya faru? Kai da wa? Ya naga hankalinka a tashe? Wacece wannan?.” Ta nuna Safeera wacce ta sunkuyar da kai.

Kallon Safeera yayi kafin ya ce. “ Ita zan aura.”

Kallon shi tayi ta kalli Safeera, kafin ta kalli Ammar tana cewa. “ Anya abokinka nan yana lafiya?.”

“ Lafiya kalau nake, kuma babu abunda yake damuna, ko ku aura min ita ko na kashe kaina.”

A razane Ummah tayi baya tana cewa. “ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un! Inna’illahi wa’inna illahi raji’un!! Saif me ya kawo kisa ciki kuma, ance baza’a aura maka ita ba ce.”

“ Bana neman izinin ku ko shawarar ku, umarni kawai nake baku.” Ya fada a burkice kamar wanda yasha kwaya.

Ammar ne ya ce. “ Saif ma Ummah kake bawa umarnin?.”

“ Ammar bana so mu sami matsala da kai, baka san me yake damuna ba na lura, dan haka ka barni kawai.”

“ Saif dole na dawo da kai idan har kana neman hanyar kaucewa.

Matsawa ta danyi daga gefen shi ganin kamar ba kalau yake ba, dan yanda yake magana a tsawace ya fara bata tsoro, ita tama ji cewa zata hakura da auren, abu kadan sai ya fara masifa yana tsawace-tsawace.

Ummah ta dubi Safeera a sanyaye ta ce. “ Yarinya a ina kuka hadu dashi ne? Tun yaushe kuke tare?.”

Muryanta ya fara rawa dan yanda Ummah ta cika mata ido da kwarjini, hakan yasa ta fara cewa. “ Aaa…. dama ba… ban…”

Katsai ta yayi da sauri yana cewa. “ Ummah ina Dad? Ai dama shi yake daura aure bake ba, mantawa dama nayi nazo gurinki, shi idan naje a take zai daura.”

Ya kama hannun Safeera yana ja dan barin gurin, muryan Dad yaji wanda tun dazu da ya shigo yake tsaye a bakin k’ofa. “ Ba sai kaje nema na ba gani nan ma Saif.”

Juyowa yayi yana kallon Dad wanda yake rike da jakarsa na aiki, da sauri ya saki hannun Safeera ya nufi Dad yana kama nasa ya ce. “ Dad aure zaka min yau.”

Numfashi Dad ya sauke yana kallon Ummah wacce ta fara kuka dan lamarin dan nata ya fara bata tsoro, wai akan mace duk ya haukace macen ma yarinya karama wacce bazata wuce k’anwarsa ta takwas ba da sun haihu da wuri.

“ Babana ai idan za’ayi aure sai anyi bincike akan yarinyar, ansan halinta da kuma gidan da ta fito, sannan…” Saurin katsai Dad yayi ta hanyar cewa.

“ A’a bana buk’atar yin bincike ni na gama bincike na tuntuni game da ita, na rigada nasan wacece ita.”

Girgiza kai Dad yayi yana cewa. “ Binciken ka daban namu daban, idan har kai ka yarda to sai muma munyi bincike.”

Wani yawu mai kauri ya hadiye yana duba idon Safeera wanda itama ya kad’a cike da tsoro, kafin ya dubi Ammar wanda shi ma idon ya zuba masa, duban Bappa yayi wanda yake shirin yin magana.

Kafin Saif yayi wani magana tuni Bappa ya furta. “ Yoo Alhaji ai yarinyar bata da wani asali, tsinto ta muka yi a bakin kogi kuma da alama lokacin fyade aka mata…..

Bappa dan kutumar uba ne🥹🥹🥹🥹🥹

*TAKU HAR KULLUM DR TEEMERH✍🏼*

14-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_

*Na*

*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_

Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

*Page 14*

Kafin Saif ya yi wani magana tuni Bappa ya furta. “ Yoo Alhaji ai yarinyar bata da wani asali, tsinto ta muka yi a bakin kogi kuma da alama lokacin fyaɗe aka mata.”

“ Ni na mata fyaden ai.” Saif ya fada yana mik’ewa tsaye.

Sunkuyar da kai tayi wani hawaye mai zafi ya shiga gangaro mata, tamabayar kanta take shin tayi wa mutane wani abu ne? Mai hadin ta da Bappa da yake shirin rusa mata rayuwa? Me ya sa yake son addaba mata ne?.

Dad ya kalli Safeera ya duba inda Saif yake shima, kafin ya d’aga kai ya kalli Ammar wanda shima sunkuyar da kai din yayi.

Jinjina kai Dad yayi yana fadin. “ Saif maganar gaskiya ne ko kawai ka fada ne?.”

Kan shi a sunkuye ya furta. “ Dad bazan taba yi maka karya ba, eh ni ne….”

Saukar mari kake ji hagu da dama, kusan dukansu sai da suka kama baki dan abun mamaki ne ace Dad ya mari Saif, yanda yake son shi kadai ya isa ya sanar da su cewa ko yatsa bazai nuna masa ba.

“ Hauka kake yi zaka aikata babban zunubi haka? Kasan yanda Allah yake fushi da wanda suke aikata zina kuwa? Ka san azaban da Allah ya tana da musu ranar gobe kiyama? Tirr da halinka, ban taba yin tsammanin cewa zaka yi haka ba, ko wani ne ya fadamin karyatasa zanyi, sai dai kash kai da bakinka ka amsa cewa kayi,,,,, Amina kina ganin kayan kunyar da Saifullahi ya jawo mana ba.” Ya karashe yana kallon Ummah wacce take kuka.

Mai da duban shi kan Safeera yayi, yana fadin. “ Ke kuma wani wauta ne ko dadin baki zaisa ki amunta da namiji har ya tabaki? Ga ki yarinya karama amma ya lalata miki rayuwa, shi namiji ne duk inda ya shiga zai yi aure, amma ke fa!!! Kafin a aureki sai wasu sun furta cewa an taba yi mata fyade, tir da kalan rayuwar nan.” Ya karashe da takaici.

Kuka Safeera ta fara tana kankame jikinta, tabbas maganar da Dad ya fada mata gaskiya ne, amma a lokacin bata buk’atar gaskiya har ta kai da ta aikata, burinta kawai ya bata kudi ta samu ta biya buk’atar ta, bata yi tunanin ita mace bace kuma wata rana zatayi aure ta haihu har ta zama uwa, hakan yasa kukan ta ya k’aru fiye da na dazu.

Cike da takaici Dad ya kalli Ammar yana cewa. “ Idan shi bayi da hankali ai kai kana dashi, ko duka taku biyun hankalinku ya gushe? Madadin a samu guda daya daga cikinku ya fahimtar dashi zunubin da zai aikata sai aka samu dukan ku kan kifi gare ku.” Numfashi ya sauke yana cigaba da fadin.

“ Bama sai kazo ka takura na aura maka ita ba, aurenta dole ne dama a gare ka tunda kai ka fara lalata ta ya kamata kai zaka k’arasa ai, kafin jama’an gari su san da cewa d’a daya tilo a gidan Safwan ya yiwa yarinya fyade gwara a daura muku auren.”

Kudi Dad ya ciro daga aljuhunsa dubu biyar yana mik’awa Ammar ya ce. “ Kaje nan bakin titi ka siyomin minti da goro.” Karba Ammar yayi yana fita da sauri.

Ummah ta ce. “ Abban Saif mai kake shirin aikatawa ne?.”

Gyara bunjumansa yayi yana rike hannu ta baya ya ce. “ Ki jira ki gani.”

Babu wanda yayi motsin kirki a cikinsu sai kukan da Safeera take yi wanda ya zuba mata ciwon kai, har ya kai da ta durkusa, Ummah ta bata ruwa tasha, suna cikin haka Ammar ya dawo da goro da minti.

Kallon Bappa Dad yayi ya ce. “ Mu zauna a daura aure.”
Chapter 11 · 0% Book details