Sashe 32
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waro ido waje duka suka yi suna kallon ta, ta kama cikinta tana sakin murmushi ta kalli Saif, ta zame a hankali tana fadiwa k’asa.
Da gudu Saif yayi kanta yana kiran sunanta. “ Radiya!!! Radiya!!! Radiya!!!!”
Mummy ta saki wani ihu tana cillar da bindigar tayo kanta da gudu, da sauri Police din ya d’auke bindigar yana rike Mummy da ta nufi kan Radiya.
Ta lumshe ido ta bude tana kallon shi, cikin kokawa da numfashinta da ya fara daukewa ta ce. “ Saif… ina… sonka!!!” Tana gama fadar haka jikinta yayi nauyi, idanunta suka kafe wuri daya, jikinta yayi sanyi hannunta ya sake.
Mummy ta fashe da kuka mai karfi tana cewa. “ Radiya ki tashi Radiya!!!!”
Ya zuba ma fuskarta ido yana kallon ta, jikinsa yayi sanyi sosai, da fa yanzu shi aka kashe da bata shiga ba, kuma wani kayan kukan a tafin hannunsa ta rasu.
Police din ya ja Mummy da karfi suka fitar da ita, aka bar Saif da police uku.
Ya rufe mata idanunta a hankali, ya cireta daga kan cinyarsa ya ajiyeta a wurin, ya mik’e jiki ba kwari ya fito, ya kalle su an bude musu get, ya daga hannu, kafin ya k’araso wurin yana kallon Mummy ya ce. “ Tsakanina da ke Allah ya isa, bazan taba yafe miki ba duniya da lahira! Allah shi kadai zai min sakayyar abunda kika min!!!” Kafin ya juya ya koma motansa ya shiga ya zauna, gagara tukin yayi sai kawai ya kira daya daga ciki security da suma jikinsu a sanyaye yace yazo ya mayar da shi hospital din.
Mom tana jin duk abunda ke faruwa amma taki fitowa, dan itama yanzu jira take Dad ya dawo ya sallame ta ta tafi, dan itama nata ya k’are.
Ga damfaran da Ashiru ya mata, ga tozarci da kunyar da ya sakata a idanun mutane, ita cutar da yake maganar ta zuba masa ma bata sani ba, kawai ta amsa ne amma bata san ma tana da wani cuta ba.
Kawai ta san tana zubar da wani warin ruwa ne daga k’asarta, amma bata san na menene ba.
Ko da taji harbin da akayi ta d’auka Saif aka kashe ma, shiyasa taji hankalinta ya sake kwanciya akan da, wayanta ma kashe shi tayi dan kiran da ake mata ya wuce na hauka.
*BAFFA POV*
Yana kwance a daki sallah asuba ma yaki fita gudun kar Gunda su tare shi, haka ya shige d’aki yaki fitowa, jikinsa ma yayi tsami sosai dan hannunsa ma da kyar yake d’agawa, yana da kudi amma yaki ya siyawa kansa magani ko abinci me kyau, gashi kwadayi da son abun duniya ya hana shi tashi ya koma sabon gidan da Saifullahi ya bashi.
Inna da Jannah suna d’aki suna jiran suji su Gunda sunzo, Inna tayi tagumi ta ce. “ Yanzu duk tilin kudin nan sai ki bawa wannan mutumin Jannah?”
“ Inna to ya zamuyi? Kina gani jiya haka aka yi wa Baffa duka a gaban jama’a, aka tozarta mu, yana da kudin ba wai bayi dashi ba amma yaki badawa, karshe ma cewa yayi sai dai a kashe shi amma bazai bada ba” Jannah ta karashe da takaicin irin halin Mahaifin nata.
“ Amma yanzu shi Saifullahi da kika amshi kudin nan a hannunsa, gaskiya dole ki aure shi”
“ Inna ba wai auren shi ne bazan iya ba, idan akayi la’akari da wani abu ma shi ya kamata na aura ba kowa ba, sai dai Safeera nake tunani”
“ Ita tayi auren ta ke ce yanzu abun tunani Jannah”
“ Inna ke nan!! Ina jin tausayin Safeera fiye da kowa a duniya, to taya zan auri Mijinta? Ta cancanci zama ita kadai a wurin Mijinta, ko ba ni ba bazan so wata ta auri Saifullahi ba duk da kuwa shi ne first love dina”
Inna tayi shuru, kafin ta ce. “ Ki dai yi tunani Jannah! Za ki iya zama da Safeera da zuciya daya, kuma nasan Saifullahi zaiyi adalci a tsakanin ku”
Har zata yi magana suka ji sallama daga waje, Inna da Jannah suka mik’e suka fito.
Baffa da yaji sallaman yaja bargo ya rufu da shi, dan ya rantse sai dai a kashe shi amma bazai bada wannan kudin ba.
Inna ta ce. “ Waye ne?”
Alhaji ya amsa da cewa. “ Kudi na nazo amsa, idan babu kuma ku fada mana sai muyi saurin kashe ku.”
Jannah ta sako hijab ta fito, hannunta rike da ATM dinta na First Bank, wanda Saif ne ya saka aka bude mata, ta iso tana cewa. “ Ina kwana?”
“ Ina ruwanki da inda na kwana, ki bani kudina kawai ko na saka a muku dan banzar duka yau”
Ta tabe baki tana bashi ATM din, ya bi da kallo yana cewa. “ Mene pin din?”
“ 5676”
Karba yayi yana mik’awa Gunda ya ce. “ Muje idan babu sai mu dawo mu kona musu ahalin su”
Da haka suka tafi, Jannah ta koma gida tana kallon Inna wacce take a tsure ta ce. “ Na basu idan sun cire zasu kawo min ATM din”
“ Allah ya miki albarka Jannah”
“ Amen “
Baffa ya bude bargon ya ce. “ Jannatuwa”
Ta kalli Inna kamar zata yi kuka ta ce. “ Kiji wani suna a wurin Baffa dan Allah” tana nufan bukkan Baffa ta shiga.
“ Ya ake ciki? Naji sun tafi sun yafe ne ko me?”
“ Baffa na biya ne”
“ Kina fakiriya da wani kudin zaki biya? Ni fa harka da munafurci ne banaso”
“ Shikenan tun da baka yarda ba”
Ya dan kalle ta kafin ya ce. “ To ko dai kinsan inda na ajiye kudina ne”
Ta jijjiga kai ta ce. “ Ni fa ba kudinka na dauka ba Baffa”
“ To waya baki kudi dan ubanki”
Ta turo baki gaba ta ce. “ Saifullahi ne ya turamin jiya”
Ba shiri Baffa ya tashi ya zauna, taja baya dan tasan karshen zancen duka ne.
“ Har nawa ya baki? Kuma ina sauran kudin su ke”
“ Ni fa iya wanda zan basu ne ya turo”
“ Amma Allah ya isa Jannatu, ina laifin ki bani kudin shine kika bawa wancan sambajejan gardin” ya mike yayo kanta, da gudu ta fice a dakin tana buya bayan Inna.
Baffa kamar kudinsa ya soma fada yana cewa. “ Ka haifi yaro baka haifi halinka ba, munafukan yarinya ina laifin ta bani kudin shine taki”
“ Baban Jannah ina ga kudin nan da aka basu taimakon ka akayi”
“ A’a taimakon kan ku kukayi, ashe da macizai nake zama ban sani ba, ina laifin ku kawo a siyomin tsire naci ko zan warke”
Inna ta amshe zancen da cewa. “ Kudin naka kuma shi na gado ne”
Ya harare ta yana jan tsuki zai shiga bukkan shi ya ce. “ Ashir naki, kuma sai kin rigani mutuwa In Sha Allah”
Jannah ta ce. “ Ba amen ba” ta shige ciki da gudu.
A hankali ta soma bud’e idanunta da take jin su sun mata nauyi, ta sauke akan drip din dake mak’ale, ta sake lumshewa tana bud’ewa a hankali.
Ta zubawa d’akin ido tana kallo kamar taga sabon abu, tana mamakin yaushe aka kawo ta nan.
K’ofan taji an bud’e, sai ta mayar da idanunta kan shi tana kallon shi, ya iso wurin ta da sauri yana jawo kujera ya zauna, ya rike hannunta yana kallon ta fuskarsa dauke da murmushi.
“ Ya jikin nako?”
Ta lumshe ido ta bud’e, ya kuma cewa. “ Kan naki ya daina ciwo ko?”
Nan ma lumshe ido tayi ta bud’e, ya sumbaci hannun nata yana daura hannunsa akan cikinta, ta kalla tana furta. “ Ina Jannah?”
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 36*
*BOOK TWO*
Nan ma lumshe ido tayi ta bud’e, ya sumbaci hannun nata yana daura hannunsa akan cikinta, tabi hannun da kallo tana furta. “ Ina Jannah?”
“ Jannah!!!”
“ Eh”
“ Yau din kuma!!”
Kau da kai tayi tana sauke numfashi kafin ta ce. “ Munyi da kai zamuje wurin ta ai, kafin aka samu hatsari a hanya”
“ Hatsari kuma?” Ya tambaya da mamaki.
Ta juyo tana kallon shi. “ Ya akayi to ka kawo ni asibiti?”
“ Ohh.. ohh haka, eh… eh hatsari, ai uhm munyi hatsari ne sai muka taho nan”
“ Kamar kana tantama akan maganar naka fa?” Ta zubawa fuskarsa ido.
Murmushi ya sakar mata yana cewa. “ Yanzu dai ba wannan ba! Ya kike jin jikin naki?”
Dan tabe baki tayi tana jan hannunta mai drip din ta ce. “ Da sauki”
Doctor ne ya shigo shi da nurse, yana cewa. “ Har ta farka kenan?”
Saif yayi murmushi yana shafa hannun nata ya ce. “ Eh ta tashi!”
Dubata yayi, ya yi su gwaje-gwajen shi, kafin ya ce. “ Akwai abun da kike ji yake damun ki?”
“ Ciwon kai ne kawai!”
Rubutu yayi akan paper yana cewa. “ Shi ma idan kika yi bacci zai dauke!” Yana kallon Saif ya ce. “ Allah ya karo sauki”
“ Amen!” Ya daura da cewa. “ Ina buk’atar sallama”
Doctor ya dubi Safeera ya ce. “ Jikin nata bai kai a sallame ta ba, tana buk’atar kulawan likita”
Saif ya masa murmushi ya ce. “ Sai a hadamu da nurse tana zuwa tana dubata har ya warke, dan bana son zaman hospital ne”
Ya jinjina kai ya ce. “ Ba matsala, yanda kace kakeso haka za’ayi BAR.SSS, zamu had’a ka da Yusrah sai tana zuwa tana dubata!”
“ Thanks”
“ Never mind” kafin ya basu takardan sallaman yana fita.