Sashe 27
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka Asabe ta saka tana komawa kitchen, Ummah ta ce. “ Haba Saif! Matarka ta konawa yar mutane hannu shine kuma kake bin bayanta.”
“ To Ummah ban da shishigi da gutsiri tsoma, uban wa yace ta kawo mata kunun? Ce mata akayi sha zata yi ne, ni fa bana son gulma ne da munahinci.”
“ Amma Saif baka da kirki, kaje ka siyo maganin da za’a shafa a hannun.”
“ Ashe kuwa hannun zai rube, ni nama fasa bar Matata a nan duk inda zanje zanna tafiya da ita kawai, ban isa da wannan makircin na mai aikin naki ba.” Ya juya ya rike hannun Safeera suka fita.
Ummah ta bishi da kallo tana girgiza kai kawai.
Part din Mommy suka je, ya bude suka shigo da sallama, Mommy ta amsa tana zuba musu ido.
Radiya dake zaune ta zubawa Safeera ido tana cewa. “ Ita ce aka auro kenan.”
Wani banzar kallo ya watsa mata nan da nan taja bakinta ta komar da hankalinta kan TV, Mommy na cewa. “ Sai yau kayi niyar kawota kenan.”
Kamar bazai yi magana ba ya ce. “ Mummy busy muke shiyasa.”
“ Ai ka kyauta kuwa.” Ta tabe baki tana kallon Safeera wacce ke makale a jikin Saif ta ce. “ Ita gold din bata iya gaisuwa bane?.”
Yaga Safeera yana mata alama da ta gaishe da Mummy amma ta nuna kamar bata gani ba, sai kawai ya ce. “ Bata jin Hausa sai Larabci.”
Sakin baki Mummy tayi suka hada ido da Radiya. “ Larabci?.”
“ Eh fa.”
“ To taya kuke magana ko kurmaye haka hada?.”
Radiya ta ce. “ Mummy ko kin manta shi ma yana jin Larabcin.”
“ Oh haka fa, to Allah ya kyauta, su Larabci manya.”
Ganin kamar suna son raina masa hankali ne yasa ya juya yaja hannun matarsa suka fice.
Mummy ta tabe baki ta ce. “ Amina dai ta koyawa yaron nan bakin hali, ko wani boka ne ta rike har ya mata aiki akaina ta kwato shi oho.”
Radiya ta ce. “ Mummy boka kuma.”
Filo Mummy ta wurga mata, ta tashi da sauri ta gudu tana fadin. ” Mummy Wallahi Anuty Fauziyya zata kaiki ta baro ki ne.”
“ Uwarki Radiya.”
*BAFFA*
Tsabar iskanci a mota yake kwana, har da bargon shi na rufuwa.
Ya iso cikin gidan yana sababi. “ Jannah idan mutuwa hutu ce a gareki to Allah ya miki rahama, amma auren ki da Alhaji kam an gama, mutumin kwarai wanda yasan darajar mutane, mai kamala.”
Jannah ta ce. “ Shi Saif din?.”
Baffa ya ragumo buta ya jefeta dashi yana fadin. “ Alhaji zaki kira shi dashi dan kutumar kullisuwar gidanku.”
Cikin kuka ta tashi tana fadin. “ Nikam Wallahi bazan aure shi ba, bayan kuma yana auren Safeera kawata.”
“ To ita Safna take da suna ko Safa ni ne na zama alwalin mijin nata, a gidan nan tazo ta zauna, yanda tasha fura da nono ai dole a mata kishiya, dan haka auren ki dashi an daura Wallahi, shi nake jira ma yazo muyi magana dan kar mu tafi gidan can ya zama kuma bai san gidan ba. Kin ga kuwa ana daura miki aure nima zan daura aure da kishiyar mamarki.”
Inna taja tsuki ta ce. “ Kai da son abun duniya kam bansan ya za’ayi ba.”
“ Ina cikin duniyar kuma bazan so abun ciki ba? To idan banso duniyar ba lahira zan so ne Innawuro.”
*SAHIBA CE*✍🏼
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 29*

“ Ina cikin duniyar kuma bazan so abun ciki ba? To idan banso duniyar ba lahira zan so ne Innawuro? Nifa makircin nan naki ne bana so.” Ya maida duban shi ga Jannah yana fad’in.
“ Ko ki so ko karki so aure da Alhaji kam an gama.”
Kuka Jannah ta saka tunawa da irin wulakanci da Saif ya mata, Baffa yaja tsuki yana cewa. “ Arziki ne bakya so naci, kuma sai naci sai dai ki dafa kanki ki soya.”
Inna ta janyo Jannah jiki tana rarrashin ta, Baffa ya kad’a rigarsa ya fice daga gidan yana sababi kan cewa sai anyi auren.
Inna tana rarrashin ta ce. “ Jannah ina ce shine saurayinki, to meyasa yanzu bakya son shi? Ko ya miki wani abu ne?.”
Tsit kake ji tayi shuru, zuciyarta ya soma bugawa uku uku, Inna bata san komai ba game da abunda ya faru a tsakanin su.
Jin tayi shuru ne yasa Inna sake cewa. “ Jannah kinyi shuru?.”
“ Inna kawai bana son shi ne, Inna na tsane shi tsana mafi muni a rayuwa, Inna ni da shi bazamu iya zama inuwa daya ba.” Ta sake sakin kuka.
*MOM*~~~~~~~~~~~~
Wunin ranar a daki tayi ta gagara fita ko falo, saboda irin warin da gabanta ke yi, taje tayi gwaji amma duk amsa daya cewa wai lafiyarta kalau.
Maganar da Ashiru ya fada mata ta tuna. < Hajjaju ya kamata dai kije asibiti a duba lafiyarki>, shuru tayi a fili ta ce. “ Taya yasan bani da lafiya?.”
Wani zuciyar ya ce. ‘ Taya bazai sani ba kina karuwarsa.’ Wayanta ta lalubo ta danna masa kira, bai gama ringing na farko ba ya dauka, ya soma magana a fada ce.
“ Makira, ashe cuta gare ki ban sani ba kika shafa min, yar kutumar uba ni kika shafawa cutar kanjamo, to billahil lazi sai na rama kuma ki jira zuwa na gidanki.”
Tsabar firgice har gagara magana tayi, da kyar ta hado kalmomi tana cewa. “ Me kake nufi Ashiru?.”
“ Zaki san abunda nake nufi idan nazo gidan naki.”
Da sauri Mom ta ce. “ A’a ka rufamin asiri inason zama a gidan mijina.”
Dariyar rainin hankali ya mata yana cewa. “ Ni na rufa miki naki ke ki tona min nawa? Ai baki isa ba Wallahi har shi sai na fadawa kuma ki duba WhatsApp naki na tura miki abu.” Daga haka ya kashe wayan.
Hannunta na rawa ta duba WhatsApp nata, ba shiri ta mike tana daura hannu a kai. “ Na mutu na lalace.” Sassarfa ta soma yi a dakin.
Number shi ta dannawa kira yana dauka ta fashe da kuka. “ Ka yiwa Allah ka yiwa Annabi kayi hakuri, na tuba karka tonamin asiri…”
Ya katsai ta yana cewa. “ Oh dama kinsan Allah da Annabi kenan kuma kike zuwa gurina muke aikata alfasha?.”
“ Na tuba, dan Allah ka goge.”
Ya kwashe da dariya yana cewa. “ Sai kin biya makudan kudade masu lasisis.”
Hawayen fuskarta da majinan ta goge ta ce. “ Shikenan nawa kakeso?.”
“ Hahaha!!! Da dollar 💵 zaki biya.”
“ Eh naji nawa?.”
“ Uhmm ki kawo ko 5,000 USD dollars ma is ok.”
A razane ta ce. “ Har 5,000 USD dollars Ashiru, da ni dashi wa ya ajiye wani?.”
“ Owk kar ki kawo ki jira sakamako.” Ya fada yana shirin kashe wayan.
Da sauri ta ce. “ Shikenan zan kawo amma dan Allah ka goge.”
“ Yaushe zaki tura?.”
“ Idan na samu.”
Tsuki yaja yana cewa. “ Baki shirya bane, kawai ki jira.” Ya kashe wayan.
Ihu ta saka tana daura hannu a kai ta cigaba da kuka, tana cikin kukan ne message ya shigo mata, tana dubawa taga Ashiru ne ya turo mata Acc number a k’asan ya rubuta *Ki sakamin kafin nan da kwana uku dan ba haka ba social media zasu sha kallo*. Tana gama karantawa ta fashe da kuka.
Ita ciwon da yake magana ta shafa masa ma bai dameta kamar yanda videos din nan suka dame ta ba.
Yanzu ma tukun a ina zata samu 5,000 USD wanda yanzu a Nigeria 7,162,667.34 NG.
*SAIFULLAHI*
Sun je sun duba Sageer wanda yanzu ya dan fara samun sauki, kafin suka nufi hanyar gidan su Jannah.
Ammar ya ce. “ Amma Saif matarkan nan kamar akwai matsala fa, ka dubi yanda tayi shuru take bin kowa da ido, anya harbin da aka tayi ranar bai taba mata kwakwalwa ba.”
Ya dubi Safeeran da tayi shuru tana kallon titi, kafin ya komar da hankalinsa kan Ammar yana cewa. “ To dai ina ga idan na gama da lamarin Jannah sai na dawo nata.”
“ Ya kamata dai ka gama da na matarka kafin ka koma na budurwa.”
“ A’a sai na gama dana Jannah.”
Ammar bai kuma cewa wani abu ba, amma maganar bai masa dadi ba sam, sai dai bayi da ta cewa.
Idanunta ne suka sauka akan shi yana tsaye a gefen motansa yana murmushi, ta zuba masa ido tana fadin. “ Shi ne.”
Saif ya dube ta da mamaki ya ce. “ Waye?.”
Ta nuna masa inda yake tsaye da hannu tana fadin. “ Gashi can.”
Tsayawa Jon yayi Ammar yayi saurin fitowa shi da Saif, sai dai basu ga komai ba, ta sauko tana kallon inda motar nasa yabi tana murmushi tana masa bye bye.
Saif ya ce. “ Ka gani ba, na fada maka ta zare amma baka yarda ba, dubi fa motar da take yiwa bye bye.”
Ammar yabi inda Safeeran take kallo yaga motar tana shan kwana, kafin ya dubi Safeeran cikin ido yana cewa. “ Kinsan shi ne?.”
Gyada masa kai tayi tana murmushi, har yanzu idanunta na kan hanyar da yabi, Ammar ya kuma cewa. “ Waye ne?.”