Sashe 8
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cigaba da cewa ta yi. “ Saifullahi yana zuwa gidan nan su dade suna hira, dan sun kusa shekara uku suna tare, sai dai ko magabatansa bai tab’a turowa ba, ko a gida ma ba’a san shi ba kawai labarinsa nakeji a gurinta; ana haka sai tazo ta sameni da batun cewa zai tafi karatu idan ya dawo zai turo manyansa, na masa fatan alkhairi, bayan tafiyansa sai Bappa ya bijiro da zancen cewa zai aurar da Jannah, nan tace tana da wanda take so shi kuma yaga kudi ya ce sam sai wanda yakeso zata aura;;;; washe gari kawai muka nemi Jannah muka rasa, ashe Bappa ya riga da ya karbi kudi a hannun mutumin da zai aura masa ita mu bamu sani ba, babu inda bamu je nemanta ba amma babu ita babu labarinta har yau da nake baki labari.” Inna ta karashe a raunane dan da alama tana jin zafin abun a ranta.
Numfashi Safeera ta sauke a ranta tana cewa. ‘ Nata da sauki akan nawa.’ A zahiri kuma ta ce. “ Inna kiyi hakuri Allah zai bayyana miki ita.”
“ Addu’ar da muke yi kullum kenan.”
Shuru ne ya biyo baya na dan wasu mintuna kafin Safeera ta ce. “ Inna shi kuma saurayin nata baizo bane tun bayan batawarta?.”
“ Har yau ban sake ganinsa ba.”
Mamaki abun ya bata hakan yasa ta ce. “ Kuma an tabbatar babu sa hannunsa a cikin batawarta?.”
“ Hmmm Safeera kenan, ai su masu kudi lamarin su daban ne, bamu duba ba har yau.” Inna ta fada a sanyaye.
Babu wanda ya sake cewa komai a cikin su, kafin daga bisani Safeera ta tashi tana cewa. “ Inna bari na shiga daga ciki.”
Gyada mata kai tayi, daga haka ta shige.
*BAPPA POV*
Yau ba’a gida ya wuni ba, kasancewar ba sana’a yake yi ba sai zaman banza, hakan yasa ya shirya ya fito kasuwa ko Allah zai sa ya samu na bakin salati.
Tafiya yake yi a kan gwaltan har zuwa post office 🏤 yana tafiya yana magana kamar zararre, photon Safeera yaga a manne a jikin wani signboard an rubuta *MISSED* da babban baki, cak ya tsaya yana kallon hoton me kyau, shuru yayi har zai wuce sai ya dawo ya ga wani mutum kamar dan sanda tsaye da bakin kaya, a dan tsorace ya ce.
“ Ina wuni Yallabai.” Yayi maganar yana dan durkusa masa.
Kallon sa mutumin yayi yana cewa. “ Lafiya Baba ka tashi lafiya?.”
Tashi tsaye yayi, kafin ya ce. “ Dan Allah yarona me wannan hoton yayi aka manna?.” Ya nuna hoton Safeera.
Kallon hoton mutumin yayi kafin ya dubi Bappa yana cewa. “ Baba batawa tayi ana nemanta, kuma duk wanda ya same ta za’a bashi naira million daya tare da mota BMW sannan a kaisa hajji.”
Sakin baki Bappa yayi, cikin k’ok’arin hado magana ya ce. “ Million daya akan wannan kuma da zuwa hajji.”
“ Eh Baba In Sha Allah haka abun yake.”
Wani dariyan hauka Bappa ya tafka yana cewa. “ Ashe harzikina yazo, chaiiiiiiiiii ai ko kashe mutum tayi ta gudu to Wallahi sai na nuna ta.” Kafin ya dubi mutumin yana cewa.
“ Yawwa yarona waye zai bada kudin tukun?.”
Murmushi kawai mutumin ya masa dan ya dauka Bappa bashi da hankali, hakan yasa ya ce. “ Ka san inda take ne? Idan ka sani yanzu zan hada motoci muje mu dauko ta sai a baka kudin ka.”
Tsalle ya buga yana tafa cinyarsa ya ce. “ Alku’an muje, idan baku ganta ba ku kashe ni, bura uba ni da yarinya tana gidana tsawon wata biyu yanzu, muje na nuna maka ita.”
Cikin serious mutumin ya ce. “ Wani unguwa?.”
“ A bulunkutu ne.”
Waya mutumin ya ciro yana danna wani number, bugu daya aka dauka, ta cikin wayan mutumin ya ce. “ Jon any news?.”
Cikin harshen turanci ya ce. “ Eh wani yazo wai ya santa tana bulunkutu, wai a gidansa take tun bayan wata biyu.”
“ Good job, kuna ina gamu zuwa yanzu.”
“ Post office 🏤.”
“ Ok gamu nan zuwa. “ Aka kashe wayan.
Kallon sa Bappa yayi yana cewa. “ Kazo muje mana kuyi sauri ku bani kudin.”
“ Come down.”
“ Ashirrr dinka ni zaka zaga.” Cewan Bappa a fusace.
Murmushi Jon ya masa yana cewa. “ Ba zagin ka nayi ba.”
“ Yooo ai na dauka zagi na kayi.”
“ A’a ni na isa na zagi mai Million daya.” Ya fada dana dariya.
Wani baza riga Bappa yayi yana hura hanci, ya ce. “ To muje.”
“ A’a muna jiran motoci ne su iso sai muje.”
“ Ahh ahh tammm tammm ba matsala ai.”
Sun kai kusan mintuna goma a gurin suna tsaye jiran motoci, duk bayan minti daya Bappa yana cewa muje, tun Jon yana kulasa har ya mantar da shi.
Motoci ne suka tsaya a gaban su guda uku, duk bak’ake yasha tinted glasses, na tsakiyan ne aka bud’e aka fito, Sageer ne shi ma sanye da bak’aken kaya.
Kallon su Bappa yayi yana cewa. “ Muje da wuri mana ni ku bani kudina, zaku rusa min shiri ne fa, inaso na k’ara aure ne dama.”
Sageer ya ce. “ Sannu Baba.”
“ Yawwa sannu yaro.”
“ Kaga kar kasa muje a banza bamu same ta ba.”
Bud’e baki yayi yana kallonsa kafin ya ce. “ Idan baku ganta ba ku kashe ni Wallahi, ko ku kaina gidan gyaran hali.”
Jijjiga kai Sageer yayi yana cewa. “ Muje to.” Kafin ya kallo Jon ya jinjina masa hannu alaman yabo.
Bude masa wajen me zaman banza Sageer yayi ya shiga kafin suka tada motan suka nufi hanyar unguwar Bulunkutu.
Mintuna talatin da uku suka dauka kafin suka iso unguwa, dai-dai line da zai sadaka da gidan suka yi parking, Sageer da Bappa da Jon suka fito, sai mota na gaba security ne guda biyu haka ma na baya, kallon su Sageer yayi yana cewa.
“ Ku ku tsaya a nan kar ku bar kowa ya shigo.” Ya nuna security guda uku, kafin ya kalli Jon da dayan security din ya ce. “ Ku muje.” Dan tuni Bappa yayi gaba.
Yana shiga cikin filin gidan ya d’aga murya ya fara cewa. “ Innar Jannah ki fito da wannan yarinyar anzo daukarta.”
Jin haka yasa su Sageer isowa da wuri, Inna da take daki ta fito ba shirin dan tasan halin mijin nata kila an masa tayin kudi ne shine yazo zai siyar da ita.
Cak Inna ta tsaya tana kallon su, a dan tsorace ta kalli Bappa tana fadin. “ Kai kuma Malam yau da wannan masifar muka tashi.”
“ Ke kimin shuru dalla, ki fito da yarinyar.”
Jiki a sanyaye Inna ta shiga dakin da Safeera take dan fito da ita, kusan minti daya ta fito a burkice ta ce. “ Malam ban ganta ba fa.”
Dai-dai lokacin da Safeera ta fito daga band’aki hannunta rike da buta, taji ana hayaniya ne shiyasa ma ta fito amma bata gama uzurinta ba.
Ajiye butan tayi tana cewa. “ Inna gani na shiga bangida ne dama, naji surutu me ya far……” Maganar ne ya katsai lokacin da ta hada ido da Sageer wanda jin muryanta yasa ya juyo.
*Ni da ku wai waye yake yi wa wani rashin adalci😹 ku bakwa comment yanda ya kamata ni kuma bana typing sosai😹 aje a haka ko zaku canja? Idan kun canja naga comments da ruwan likes anjima ma da dare zan sakar muku update.*
*DR TEEMERH✍🏼*
11-
💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari
Na
Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 11*

Hannu take nunasa da shi cikin k’ok’arin hada kalmomi ta furta. “ Me… zaku… min?.”
A hankali Sageer ya fara tako inda take cikin hikima yana fadin. “ Ki ga babu abunda zamu miki, ki taimakawa rayuwan bawan Allah kizo mu koma, Sir yana dab da rasa ransa akan ki, dan Allah kizo muje.”
Baya ita ma ta fara yi tana cewa. “ Babu inda zanje, sai me idan ya mutu din, ai dama ya cancanci mutuwa, irin mutuwar da ba imani wanda tifa zai taka shi.”
Bappa yayi saurin cewa. “ Kin ga Safeera kike da suna ko Sufi, kizo ki bisu dan a samu a sallame ni, dan gidan nan babu wajen zamanki kuma.”
Jon ya dakatar da shi ta hanyar nunasa da hannu yana cewa. “ Baba ka kama bakinka, ita din Beb din uban gidanmu ne kabi a hankali.”
Tsit Bappa yayi yana zuru zuru da ido, dan yanda Jon ya masa magana kai zaka gane gargadi ya masa, Inna hawaye ta fara dan Safeera tausayi take bata.
Cigaba da magana Safeera tayi tana cewa. “ Kaje ka fada masa cewa har abada bazan zo ba, kuma zan zauna zaman jiran labarin mutuwarsa.”
Hadiye yawu yayi kafin ya ce. “ Sorry dan Allah amma ko sau daya ne kizo muje ki gan shi.”
“ Bazan je ba.”
“ Alkur’an sai kinje, ni zaki tonawa asiri? na miki rana shine kike so kimin dare, ashe baki da mutunci?.” Bappa ya fada kamar zai haukace dan bakin ciki.
Kallon shi Safeera tayi ta kalli Inna, gyada mata kai Inna tayi tana lumshe ido, jinjina kai Safeera tayi dan ta gane maganar, kafin ta kalli Sageer ta ce. “ Shikenan muje na gan shi sai na dawo.”
Da sauri Sageer ya ce. “ Yawwa Thank you Maa.”
Hararan shi tayi, kana ta nufi d’akin da take zama, minti kadan ta fito sanye da hijab blue wanda Inna ta bata, sosai ya mata kyau dan ya karbi fatarta.