Sashe 21
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata rai tayi tare da fadin. “ Sai kuma aka ce miki bazan baki nawa ki saka bane? Ni fa malama ki dauke ni tamkar yar uwarki wacce kuka fito ciki daya.”
Murmushi tayi tare da cewa. “ To Jannah.”
Wajen kayanta dake kulle a zani taje ta dauko ta kawo gaban Safeeran tana cewa. “ Ki zabi wanda zai miki, sai kije ki fara wankan kafin nima nayi.”
Murmushi kawai ta yi tana duba kayan, wani doguwar riga ta dauka na atamfa, sai hijab blue, duk dama sun tsufa sosai amma a tsaftace suke.
Bayan ta ajiye ne itama Jannah ta ciro wanda zata saka ta daure sauran ta komar, kafin suka mike Jannah na daukan bokitin ruwa guda daya suka fito waje Safeera na mara mata baya.
Y’an gidan sai binsu da kallo suke har suka iso band’akin dake zagaye da langa-langa, a bakin band’akin suka tsaya Jannah na mika mata sabulu ta ce. “ Idan kika fito sai na shiga ina jiranki.”
Karba tayi ta dauki ruwan ta shiga, Jannah na tsaye a bakin toilet din tana jiranta, har ta gama kafin ta fito jikinta na digar ruwa, Jannah ta shiga tayi ta fito kafin suka nufa dakinsu suna hira.
Suna zaune a dakin bayan sun dawo daga bara sun samu abinci, tashi Jannah tayi ta rufe kofar ta danne da dutse, Safeera na binta da ido har ta gama ta dawo ta gyara musu wajen kwanciya.
Bayan sun kwanta ne Safeera ta ce. “ Jannah bani labarin ki mana, ina nufin tarihin rayuwarki.”
“ Hmm!!! Safeera a labarina babu komai sai haushi da Allah ya isa, dan labarina yana dauke da sharrin biyewa saurayi ne.”
Da mamaki Safeera ta tashi ta zauna tana lalubo torch din Jannah ta kunna, da mamakin ta sai taga Jannah na zubar da hawaye, da sauri ta jawota jiki tana furta. “ Subhanallah, dan Allah kiyi hakuri banyi tunanin magana ta zai bata miki rai ba.”
Cikin kuka ta ce. “ Safeera ba maganar naki bane ya bata min rai, asali ma tunawa dashi din da nayi ne ya bata min rai.”
“ Kiyi hakuri to.” Safeera ta fada a sanyaye.
Sakin juna sukayi Jannah ta jinginu da jikin bango, yayin da hasken torch yake tsakiya, Safeera kuma tayi zaman masu cin abinci ta zuba mata ido.
“ Hmm! Safeera na zabi zaman kadaici ne.” Cewan Jannah kafin ta cigaba da cewa. “ Sunana Aisha Bukar Muddibo, amma anfi kirana da Jannah dan shine sunan da Innata ta sakamin….
Haifaffiyar garin Maiduguri ne, unguwar bulunkutu, Ni daya iyayena suka haifa daga nan Allah bai sake basu haihuwa ba, tun ina karama nake ganin halayen Mahaifina daban dana Mutane, dan Bappa Allah ya hore masa son kudi na masifa, akan kudi babu wanda bazai siyar ba, ciki kuwa har da ni.
Ya sakani a makaranta na tsangaya wato almajiranci, har na girma, Inna ta dauramin tallan fura da Nono ina fita siyarwa, tun ina da shekara sha biyar nake siyar da Nono har Allah ya hadani da wani saurayina Saifullahi.
Saifullahi Attajirin mai kudi ne kuma yana ji da kuruciya, mun hadu dashi ne a gurin da naje siyar da nono a bakin titi, ya tsayar dani ya siye duka, nayi murna sosai dan ganin da nayi ya min juye duka.
Ai kuwa na tattara komai na koma gida, sai dai bansan yana biyo ni ba har na isa gida, na kaiwa Inna kudinta cas.
Washe gari sai ga Saifullahi yazo wai gurina, da mamaki naje muka gaisa sai yace yazo siyan Nono ne, nayi murna sosai dan yau irin na jiya yamin wato juye.
Har muka tsaya muka dan taba hira kafin ya tafi, tafiyarsa ke da wuya sai Baffa yazo ya kwalamin kira, da dauri na tashi naje na same shi ranshi a bace ya ce. “ Shi wannan yaron da yazo fa?.”
“ Baffa fura yazo siya.”
“ Kun daukeni bani da hankali dake da Innar taki ko? Yazo ya baku kudi shine zaku hanani kice wai fura yazo siya.”
Inna ta fito daga daki tana cewa. “ Muddibo fura fa yazo ya siya kuma ya koma.”
“ Aniyar ku ta biku, masu bakin hali, ai gobe zai dawo sai muga idan kudin yake baku ko kuma furan yake siya, masu bakin aniya kawai, bazaku hadu azo a rufawa juna asiri ba, ina zaune daku ashe da macizai nake zaune.” Ya juya zai tafi yana guna-guni. “ A sannu a hankali kowa halin shi zai fito.”
Jikinmu ni da Inna yayi sanyi na juya na shiga daki.
Washe gari kuwa sai ga motan Saifullahi yazo, na tashi na kai masa fura sai dai bashi bane wani ya aiko wai Sageer, muka gaisa har zai tafi sai Baffa yazo.
Ganin ba kudi ya bani ba yasa Baffa bai ce komai ba juya ya tafi.
Ana haka soyayya mai bala’in karfi ya shiga tsakanina da Saifullahi, sai dai wani abun mamaki duk zuwan da Saifullahi zaiyi bai taba haduwa da Baffa ba sai dai Inna, Innar ma wani lokaci ne, ranar da Baffa yazo sai ya zama Sageer ne, har Baffa ya fara cewa da Sageer muke tare.
Mutanen rugarmu suka fara kananan maganganu, amma dake soyayya ya rufemin ido, idan ya shiga ta nan sai ya fita ta can.
Mun kai kusan watanni muna soyayya da Saifullahi, wata rana yazo da dare.
Muna tsaye a jikin motarsa ya ce. “ Jannah!!.” Na amsa da. “ Na’am.”
Numfashi ya sauke yana cewa. “ Zan tafi karatu Cairo, bazan dade ba idan na dawo zan turo magabatana sai ayi maganar aure.”
Duk da naji ba dadi amma sai nayi murmushi nace. “ Bakomai Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya.”
Ya amsa da. “ Amen, Amma ki rikemin amana, bazan dade ba duka duka bai wuce wata biyu zuwa daya zanyi ba, In Sha Allah idan na dawo za’ayi magana.”
Muka dan taba hira kafin ya tafi, na dawo na sanar da Inna.
Bayan tafiyarsa da wata biyu Baffa ya bijiromin da zancen aure wai ya min miji, nan nace nifah akwai wanda nakeso kuma idan ya dawo zai turo ayi magana.
“ Alkur’an baki isa ba, ni zaki tozarta a idon duniya dan malafar gidanku, ai kuwa gobe Alhaji zaizo a daura muku aure dan ya biya sadaki ma dubu dari, kuma wallahi sai kin aure shi.”
Nan na fara kuka Inna na tayani, cikin dare na sulale na gudu daga gidan ban sanar da kowa ba, kuma babu wanda yasan inda naje har yau.
Ina cikin gudu naji an daukeni, bansan inda nake ba sai washe gari na ganni a kan gado.
Da mamaki nake bin dakin da kallo kafin na sauke idanuna akan shi, yana sakar min murmushin nasa mai daukemin hankali da tunani.
Ya budi baki ya ce. “ Jannah ta!!!.”
Ban amsa ba sai ma cewa da nayi. “ Yaushe ka dawo?.”
Tasowa yayi ya zauna a kusa dani ya kama hannuna ya rike yana cewa. “ Jiya da daddare na shigo garin, kawai sai naji inaso na ganki, ban isa gidanku ba na ganki a hanya kina gudu cikin dare, ina zakije haka?.”
Kuka na fashe masa dashi ina cewa. “ Baffa ne zaimin auren dole, shine na gudu.”
Banga bacin rai a tare dashi ba sai ma cewa da yayi. “ To meyasa baki yarda ba?.”
“ Saboda akwai alkawari a tsakaninmu.”
Murmushi yayi da bangane me yake nufi ba ya ce. “ Haka ne, tashi ki watsa ruwa sai kici abinci.” Daga haka ya fita daga dakin.
Numfashi ta sauke idanunta na zubar kwalla ta kalli Safeera ta ce. “ Safeera kinsan me ya faru?.”
Girgiza kai Safeera tayi alamun tanason cigaba da labarin, Jannah ta ce. “ Zama muke yi a gidan tamkar Miji da Mata.”
Da sauri Safeera ta ce. “ Ban gane ba Jannah? Aure kukayi?.”
Girgiza mata kai tayi ta cigaba da bata labarin. “ Tun lokacin da ya kawoni gidan a daki daya muke kwana muci abinci tare, tun ina nuna masa kar shaidan ya shiga tsakaninmu har na daina damuwa dan naga shi bai dauka a wani abu ba.
Ana haka wata rana Sageer ya shigo dashi ba lafiya, a rude na nufo su ina cewa. “ Me ya faru dashi?.”
Sageer ya ce. “ Ciwon ciki ne yake damunsa ki hada masa tea da lemon tsami idan yasha zai warke bari naje na dawo.”
Gyada kai nayi na nufa kitchen da sauri na hada masa Tea dan dama ya koyamin yanda ake amfani da gas, na hada masa na dauko lemon tsami a fridge na matsa masa na fito.
Sai dai baya falon ya nufi dakinsa, hakan yasa na bisa dakin dan na kai masa.
Yana tsaye daga shi sai gajeran wando, da sauri na ajiye tea din dan tun da nake dashi ban taba ganinsa haka ba, na juya da sauri zan fita ya kirani. “ Jannah ta.”
Cak na tsaya na gagara motsi zuciyata na dukan uku uku, inaji ya tako inda nake ya tsaya dab da ni.
Hannu yasa ya zageye cikina yana daura kansa a kafadata ya fara shinshinar wuyata, da sauri na zame jikina na ce. “ Saif ka manta ba kyau, kuma kamin alkawari bazaka tabani ba har sai munyi aure.”
Bai ce min komai ba ya jawoni jikinsa yana saka hannu ya kashe wutan dakin, a Wannan daren labarin rayuwata ya canja ya tashi daga budurwa zuwa budur bazar, na tashi daga macen da take killace kanta zuwa ballagaza, na tashi daga saliha zuwa karuwa.
A wannan daren nayi kukan da ban tabayi ba, nayi dana sanin guduwa daga gidanmu, nayi Allah wadai dani yafi sau billion.
Bai barni ba har sai da ya zubar da ishinsa sau biyu, kafin ya barni nasha iska.
Ya taimakamin na tsaftace jikina sannan ya bani magani nasha na kwanta baccin azaba.
Tun daga wannan ranar kuma ya mayar dani Matarsa, duk lokacin da ya jiyo ishinsa sai yazo kaina ya sauke, wani lokacin sau uku a rana wani lokacin sai biyu, tun ban saba ba har na saba dashi, dan kullum cewa ya ce. “ Zan aureki, ni ne mijinki ko na kusance ki ba matsala ba ce.”