← Book details Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 39

Sashe 17

Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa police din yayi gurin sauran yan uwansa yana magana k’asa k’asa. “ Wadan nan fa sun fimu hauka kuma daga gani babu kudin da zamu samu a gurin su, the early the better mu bar su tunda Oga bai dawo ba.”

Jijjiga kai suka yi kafin suka dubi inda suke sun zuba musu ido, a tsawace officer ya ce. “ Ku kira ayi billing naku sai ku tafi.”

Nuna musu jikin bango Falmata tayi ta ce. “ Billing is free, ko ka dauka bama jin turancin ne? Mu fa idan da sabo mun saba zuwa gurin nan, infact gida ne ma a gurin mu.”

“ Ke baki da kunya ku tashi ku tafi.”

Tabe baki tayi tana mike ta harari Kausar tayi kwafa, mayafinta ta gyara tayi gaba, Rauda ta rike goshinta wanda ke zubar da jini ta fita tana Allah-Allah a isa gida, kama Kausar Safeera tayi suka fito daga police station din.

Suna fito suka hadu da Mama ta sauko a machine ita da Umar fuskarta duk kwalla, tausayinta Safeera taji.

Da sauri ta iso gurin su taga Kausar ba shiri ta fara kai mata duka, ko motsi su Falmata basuyi ba, da kyar Safeera ta kwace ta a hannun Mama.

“ Ku kashe ni ku huta kawai.”

Babu wanda yayi magana machine din da ta taho dashi suka shiga suka koma a hanya aka tsaya a chemist aka yiwa Rauda dressing na goshinta aka manna mata bandeji suak cigaba da tafiya zuwa gida.

Mama ta biya kudin machine suka shigo ciki, kafin kace me tuni Falmata da Rauda sun fara dukan Kausar, Mama bata kula su ba ta nufi dakinta.

“ To ku kasheni ku huta mana haba.” Cewar Kausar tana daga hannu sama, dan dama muryanta ya fita daman a gidan saboda yayi kama da namiji.

“ Dan uwarki zamu kashe ki kuwa, kullum kina cikin jawo mana fada, kije kiyi yawon karuwancin ki ki dawo ki jawo mana fada.” Cewan Falmata.

Safeera ta zauna ta fara kuka ta ce. “ Ku ko tausayin Mama bakwa ji sam, duk kun zama yan iska, ita wannan sai yawo tazubar kamar busuru.” Ta wurgawa Kausar kofin dake kusa da ita.

“ Ke kam kika tabani sai na sauya miki kamannin fuskarki.” Cewan Kausar tana kallon Safeera.

“ Au haba ni din?.” Ta nuna kanta kafin ta tashi ta tsinka igiyar sanya tayo kanta a haukace, tana zabga mata igiyara tana fadin. “ Dama na gaji dake a gidan nan, ni ce dama ke tausayinki amma tun da zaki sauya min kamanni bari na gwada sumar dake kadan.” Ta fada tana buga kanta da jikin bango.

Sai da su Falmata suka raba su kafin taje ta zauan tana huci.

“ Bar muku gidan zanyi kowa ma ya huta.” Ta mike zata fita.

Safeera ta mike a fusace ta wurgar da dankwali ta soma cewa. “ Wallahi Kausar idan kika fita sai na miki tsindir a gaban yaran nan naci ubanki, sai suga nonon da kike zuwa karuwanci dashi….

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_

*Na*

*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_

Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP?mode=ems_copy_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

*Page 19*

Sai da su Falmata suka raba su kafin taje ta zauan tana huci.

“ Bar muku gidan zanyi kowa ma ya huta.” Ta mike zata fita.

Safeera ta mike a fusace ta wurgar da dankwalin kanta ta soma cewa. “ Wallahi Kausar idan kika fita sai na miki tsindir a gaban yaran nan naci ubanki, sai suga nonon da kike zuwa karuwanci dashi.”

Komawa tayi ta zauna dan duk haukarta tana tsoron Safeera idan ta burkice.

~~~Washe gari~~~

Da sassafe kafin kowa ya farka Kausar ta fita daga gidan, ko da suka farka basu ganta ba idan da sabo sun saba hakan yasa masu aiki suka fara yi.

Cikin mintina kadan aka gyara gidan abun ka da gidan mata, rub da ciki duk suka yi yunwa na damun su.

Mama ta fito cikin shirinta na tafiya aiki ta gan su tare da cewa. “ Ku karbo ko garin kwaki da sugar a shagon Alai bana idan na samo wani abun daga aikin sai na biya shi.”

Tashi Safeera tayi ta dauko hijab din ta. “ To Mama bari naje Allah ma yasa ya bamu dan yana bin mu bashin dubu biyu.”

“ To Amen, ina Kausar ne?.”

Falmata ta ce. “ Hmm!!! Ta fita yawon nata tun asuba.”

“ Allah ya kyauta, ya jikin naki Rauda?.”

“ Alhamdulillah kan ya dena ciwo ma.”

Daga haka ta fita bayan ta musu fada kan cewa ko Kausar ta nemo tsokana kar su tare mata.

“ Dan Allah Alai bana ka bamu bashin Wallahi idan muka samu kudi zamu baka ka taimaka.” Cewan Safeera kamar zata yi kuka.

Matso da bakinsa yayi kusa da kunnenta ya ce. “ Idan kin yarda kullum zan na baku abinci amma da sharadi.”

“ Ina ji koma menene zanyi.”

“ Kullum za ki na zuwa shagona kina kwana da safe sai ki koma.”

Baya tayi tana girgiza kai. “ Ni ba yar iska bace kuma bazan koma yar iska ba.”

Kamar zai hauta da masifa ya ce. “ Iskanci na nawa kuma? Ke da uwarki take fita yawon karuwanci Yayarki kuma ta zama karuwa.”

Kuka ta fashe da shi ta koma gida da gudu tana shiga.

Da sauri Falmata ta nufeta. “ Me ya faru waya tabaki?.”

Cikin kuka ta soma cewa. “ Falmata kowa kallon karuwai yake mana a unguwar nan! Kausar ta bata mana suna.” Ta karashe cikin kuka.

“ Yanzu wa ya zage ki?.” Cewan Rauda tana zama.

“ Alai bana ne nace ya bani bashin gari shine ya soma cewa wai Mamata yawo karuwanci take haka ma Yayata saboda haka kawai nazo shagon shi zai na bamu abinci idan har zan dinga kwana.”

“ Kutumar jar uba.” Cewan Falmata tana tashi tsaye.

“ Dawo ki zauna! Dawo ai ba yanzu zamu rama ba sam!!.” Rauda ta fada tana koran yaran a falo kafin ta kalle su ta ce. “ Kun san Allah babu abun da zai hana yau bamu masa tabargaza a shago ba.”

Safeera ta ce. “ Rauda ban gane ba? Nifa banason hayaniya ko masifa.”

“ Dakata Malama, ke dama an saba zaginki ki hakura amma nikam sai na tabbata na masa wani dan illa kadan a zuciya.”

“ Nagodeeee!.” Cewan Falmata tana sakin dariya.

Ita dai Safeera da ido ta bisu.

Wunin ranar haka suka yi shi duk yunwa, idan da sabo sun saba, Abba ma yana kwance a daki ya rasa ina zaije ya samu aiki, suna haka har aka kira sallan mangarib, koran Umar suka yi zuwa masallaci suka saka yaran a gaba suka yi salla.

Duban agogon dake manne a jikin bango Safeera tayi ta ce. “ Yau Mama har karfe Takwas bata dawo ba.”

“ Ai ba sabon abu bane Safeera, ko kin manta kowa zaman kansa yake a gidan nan?.” Cewan Rauda.

Wutan Nepa aka kawo, tashi suka yi suka yiwa Nabila, Ammi da Amma shimfidi, kwanciya Safeera tayi tana kallon yanda suka saka riga da wando kamar masu zuwa tsalle, kafin ta ce. “ Ina zaku je ne?.”

“ Ki zuba ido kawai ki gani, kafin mu dawo idan Kausar tazo kar ki bari ta kwanta kusa da su Nabila kar ta shafa musu wani cutan, sannan duk bura uban da zakiji ana yi kija bakinki kiyi shuru.” Cewan Falmata.

“ Hmm!! Zaku nemo wata masifar kenan, sai kun dawo to.” Ta karashe tana jan bargo ta rufe jikinta.

Fita Rauda da Falmata suka yi suna ja musu kofar dakin.

Har sai da suka jira Alai Bana ya kulle shago ya tafi gida, mutane sun watse a wajen ya zama shuru baka jin komai.

Nufan shagon suka yi Falmata na daukar dutsi ta buga a jikin kwadon, nan ya bud’e da sauri suka shiga cikin shagon suna dan jan kofar ta yanda baza’a gane da mutane ba.

Duk abunda suka samu kawai diba suke, sun masa ta’adi sosai da sosai, shikafa kwano biyar suka diba haka ma wake, madara da milo ba’a magana sun kwasa na kwasa.

Bayan sun gama tattare komai ne suka tsaya kallon kayan, Rauda na fadin. “ Yanzu taya zamu fara divar kayan nan?.”

“ Ai mun gama mai wahalan, ki zage ki diba kawai mu tafi kafin a kama mu.”

Kwalin fridge dake ajiye suka gani, daukowa Falmata tayi suka fara zuba kayan a ciki, har zasu tafi suka ga mayonnaise da sauri Raudah ta dauka ta saka kafin suka ja kwalin da kyar suka fita a shagon.

Da kyar suke ja har zuwa kofar gida, tura kofar Raudah tayi taji a bud’e, kafin suka daga kwalin da kyar zuwa ciki dai-dai lokacin da Abba ya fito yin mitsari.

Had’a ido suka yi ya kalle su ya kalli kwalin. “ Wannan fa a ina kuka samu?.”

Babu wanda ya kula shi suka ja zuwa d’akin su, da ido ya bisu kafin ya wuce band’aki dan a matse yake.

Bayan sun kai daki ne Falmata ta ce. “ Raudah ya zamuyi? Abba fa ya gani.”

“ Sai me idan ya gani din? Ai naga shi baya bamu abinci sannan baya kula damu a bangaren karatun mu? Mama ne kawai ke k’ok’ari ita ma yanzu ta fara gajiyawa, idan bamu taimaki k’annen mu ba waye zaizo ya taimake su?.”

Jinjina kai Falmata tayi kafin suka kai sa can lungu suka zuba kaya a kai ta yanda bazaka taba ganewa ba, jan kofar dakin suka yi suka danna kwado, get ma suka saka mata kwado kafin suka nufi dakin Mama.

Hada ido suka yi da Safeera wacce ta tashi ta zauna tana jiran dawowar su.

“ Sai yanzu kuka dawo har karfe daya ta rufa?.”

“ To ke waya hanaki bacci?.” Falmata ta tambaya yayin da take kwanciya kusa da Safeeran.

“ Na tsaya jiran dawowar ku ne.”
Chapter 17 · 0% Book details