Sashe 16
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Idan kunyi comments na muku gobe idan ba kuyi ba na barku ku huta🙌*
*DR TEEMARH✍🏼*
18-
💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_
*Na*
*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 18*
Nufan dakin yayi su Dad na binsa, wasu daga cikin security’s da police suka bishi yayin da sauran suka tsaya a kofar emergency.
Kwantar da ita yayi akan gadon yana zama a gefe, nurse din ta duba ta kafin ta mata allura na hutu, nan da nan bacci ya dauke ta.
Dad na fadin. “ Saif su waye suka kawo maka harin ne?.”
Numfasawa yayi sannan ya ce. “ Dad ya kai 8-9 months ana bibiya na, and bansan wane ne bane, da farko da suka ga mun gane sai suka dauke k’afa, to dazu da zan fita dan siyo mata kayan sawa naga mota baki na bin mu, nan muka canja hanya, a tunanin mu sun tafi, kawai fitowar da zamuyi sai gani mukayi an kawo mana hari.” Ya nunfasa ya ce. “ Dad Wallahi nayi rantsuwa duk wanda na tabbatar da sa hannunsa a lamarin nan sai na yanke masa hunci dai-dai da abun da ya aikata.”
“ Allah ya shige mana gaba kawai.”
“ Amen.”
“ Amma yanzu ana bincike ko?.”
“ Eh an kama guda daya sauran kuma sun gudu, to ta hanyar wannan za’a kama sauran idan har suna cikin garin nan.”
Ummah ta zauna kusa dashi tana rike hannunsa, kallon ta yayi kafin ta ce. “ Saif kana addu’a dan tabbas kana da makiya, kuma kasan irin aikin ka ta iya yiwa akwai masu bibiyarka baka sani ba.”
“ In Sha Allah Ummah, amma ni babu wanda nake zargi gaskiya.”
Doctor ne ya shigo suka juya suna kallob shi.
“ Sir anyi nasaran ciro bullet din, sannan an samu numfashinsa ya dai-daita, sai dai yana buk’atar jini.”
“ Babu a nan ne?.”
“ Akwai amma da tsada dan jinin mai wahalan samu ne.”
“ Don’t worry about the money, ko nawa ne za’a siya ku karbo ku mana aiki bani acc din da zan tura kudin.”
“ Ok.” Nan ya karanto masa Acc number ya tambaye shi nawa ne kudin ya fada masa, nan ya saka har da k’ari ma.
Suna zaune a dakin bayan dr ya fita wani security ya shigo, kallon shi Saif yayi ya tambaya ko lafiya.
“ Sir wata ce take son ganin Oga.”
Dad ya ce. “ Ni kuma?.”
“ Yes Sir.”
Hankalin Ummah ya dawo gare shi ta zuba masa ido.
“ Kace ta shigo.” Cewan Saif yana bin hannun Safeera da kallo dan ya fara motsawa.
A hankali ta soma bud’e idon tana sauke su akan matar da ta shigo da sallama.
A kidime Safeera ta tashi daga kwanciyar tana furta. “ Ummah Fauziyya.”
“ Safeera!!!.” Cewar Fauziyya tana ware ido tare da dafe kirji.
“ Kin santa ne?.”
Gyada masa kai tayi tana nuna ta da hannu ta ce. “ Kishiyar Mamata ne.”
Kallon kallo aka tsaya yi kafin Ummah ta ce. “ Kawar Mummy dinka ce baka gane ta bane Saif?.”
Girgiza kai yayi alaman bai gane ta ba, ya dubi Safeera ya ce. “ To ina Maman taki?.”
Murmushi da yafi kuka ciwo tayi tana cewa. “ Yau zan baka labarina tun daga farko har dalilin da yasa na dawo 20 houses.”
~~~~~~WACECE SAFEERA.
Haifaffiyar garin Borno State ce, Mahaifinta dan nan ne wato Malam Bukar, kanuri ne gaba da baya, matansa uku wato Hajiya, Fauziyya sai Fatima wacce suke kiranta da Mama.
Malam Bukar mai kudi ne ada kafin karayar arziki ta same shi, a wajen uwargidansa yana da yara Biyar mata uku maza biyu, Fauziyya kuma biyu duka mata sai Mama wacce take da yara bakwai namiji daya.
Kausar ce babba sai Falmata kafin Safeera sai Rauda Nabiya Ammi sai Umar, Allah ya bawa Safeera hakuri sai dai bata juran yunwa ko kadan.
Tun bayan da Malam Bukar ya samu karayar arziki ya siyar da gidan da suke ciki ya siya guda uku ya rabawa matan nasa kowa gida, sannan ya danka musu takardun gidan a cewarsa ko bayan mutuwarsa kar kowa tayi fada akan gidan.
Duk inda aka ce mata bin malami to Fauziyya ce gwana kuma ita ce a farko, ta rusa duk wani farin cikin gidan.
Babu asirin da bata yi ba dan Mama ta mutu amma yaki cinta, karshe ma sai ya fada akan Hajiya wacce rana guda aka samu gawarta a daki ta mutu, yaranta sunyi kuka sosai inda Mama ta dauki karamar cikinsu wato Amma zata zauna da ita.
Tun Kausar na karama Fauziyya ta mata asiri wanda ya kamata har yau da bata warke ba, ta haukatar da yarinyar sosai, babu inda Mama bata je ba dan neman magani amma abu yaki ci.
“ Bukar ni fa na gaji da lamarin gidan nan ka sake ni na wuce garin mu.” A cewar Mama a tsakiyar gida.
Kuka kawai su Safeera ke yi dan Kausar ma bata gidan ta tafi yawo tazubar dinta, su Nabiya da Ammi kuma suna kanana haka.
“ Komai na duniyar nan yar hakuri ce, ki cigaba da hakurin da kike yi wata rana sai labari.” Cewan Malam Bukar wanda suke kira da Abba.
“ Ina bazan iya ba kuma ta ishe ni yanzu kam.”
Safeera tazo da gudu tana kama Mama ta ce. “ Mama dan Allah kiyi hakuri.”
Fuzge jikinta tayi a fadace ta ce. “ Idan baki sakeni ba sai naci uwarki a gidan nan, shegiya kawai ai kuna gani Baban ku baya kawo abinci a gidan nan kullum ni nake fita aiki nake samu, gashi aikin ya kare dan ubanku a ina zamu samu.”
Cikin sanyin murya Abba ke fadin. “ Ku bawa Mamarku hakuri, da ai ina kawowa yanzu ne karfina ya kare.”
“ To Bukar tunda karfinka ya kare ai sai ka sauwake min nayi gaba ko? Haba kubi ku haukata mutum.”
“ Kema kinsan inasonki Fati.”
“ Bukar Wallahi sai ka sakeni ko a rasa kwanciyar hankali.”
Falmata ta kama hannun Ammi da Nabiya ta kai su daki ta ce. “ Kar naga kafarku a wajen nan?.”
“ To.” Cewan Nabiya.
Shigowa da gudu Umar yayi yana fadin. “ Falmata, Safeera! Rauda kuzo an kama Kausar a bakin line ana dukarta.”
Ba shiri Safeera ta mike tsaye, da gudu Falmata ta nufi kitchen ta dauko tabarya, janyo mayafinta Safeera tayi ta fita a dari, Rauda na mara mata baya hannunta rike da sanda, da gudu Falmata ta fito ita ma hannunta rike da tabarya.
Mama zata biyo su Abba ya ce. “ Ki zauna ai gidan mata ne, su zasu je su dawo, ki bar su.”
“ Kaga ba? Sana’ar kenan, burinka a kashe min yara sai hankalinka ya kwanta, munafukar matarka tasa babbar y’ata tabi duniya gashi ana can ana dukanta, yanzu suma idan suka je bansan me zai faru ba.”
Abba bai ce komai ba ya shiga dakinsa dake kusa da kitchen wanda mara bansa da kurkukun kadan ne.
A waje kuwa Safeera na isa taga yanda aka rufe Kausar da duka a k’asa har sun fasa mata jiki, tana kuka ta shiga tsakanin su tana basu hakuri, amma sam basu ji ba sai ma cigaba da suka yi da dukan su su biyun.
“ Ku dauko taya ku hada musu, gobe bazata sake yin sata ba ai.” Cewan wani mutum yana tsaye da sanda a hannunsa.
Hango su Falmata da Rauda suka yi suna zuwa da gudu ko wacce rike da abun duka, kai ko mahaukaci ne idan kaga yanda suke zuwa da gudu kawai ka bar gurin.
Kafin suce me tuni Falmata ta kai tabarya kan mutumin dake dukan Kausar. “ Dan kutumar ubaka kai ka yita ne da kake dukanta kamar yarka.”
“ Ni kika kwalawa tabarya.” Bai gama rufe baki ba Rauda ta kai masa sanda a k’afa.
Da sauri Safeera taja Kausar gefe, fada aka shiga yi tsakanin su da mazan, ta ko’ina duka ake kaiwa mutum, kafin su ankara an bugawa Rauda sanda a koshi nan da nan ya fashe sai jini.
“ Wayyo!!! sun kashe ni.”
“ Char uba kanwata zaku fasawa goshi.” Cewan Falmata tana kaiwa wanda ya bugawa Rauda sanda tabarya a ciki.
Gurin ne ya hargitse da mutane ganin ana k’ok’arin yin kisa, wani daga gefe ya kira motar y’an sanda kafin kace me har sun iso.
Kama Kausar Safeera tayi da zummar guduwa, amma aka tare su, saka su aka yi a motar y’an sanda zuwa police station 🚉.
Da gudu Umar ya koma gida yana kuka. “ Amma.” Sunan da yake kiran Mama dashi kenan. “ Amma!!! An tafi da Safeera da su Kausar police station.”
Hijabi ta saka ta fito da gudu suka nufi police station din, duk ta rude lokaci daya ta rame.
“ Ni fa babu wanda zai saka ni a cell tun da ba kisa nayi ba, ai self defense ne naga.” Cewan Falmata tana kama k’ugu tana hararan wanda suka yi fadan dashi.
A tsawace police din ya ce. “ Shut off!!! Kar ki mana raini a nan.”
Murkuda masa baki tayi tana dauke kai, a fusace yayi kanta da sauri Safeera ta shiga tsakiyar su tana cewa. “ Dan Allah kayi hakuri.” Ta hade hannayenta ta durkusa.
“ Haba dan Allah Safeera, kina zubar mana da aji Wallahi to wani laifi muka yi da zaki bashi hakuri.” Cewan Rauda tana hararan police din dan sun gan shi gajere duk sun fishi tsayi.
“ Ke!!! Ubaki shegiya da masifar gida zamuji ko da naku.” Cewan Safeera kamar zata yi kuka.
“ Safeera ki zauna fa, mu gama wannan tukun muje gidan dan Wallahi sai maci uban Kausar tun da ita rayuwarta nema mana magana ko? Shegiyar yarinya dama barinki akayi ba’a haife ki ba, sai yau kin gane kuranki.” Falmata ta fada a fusace.