Sashe 20
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanciya tayi akan kujeran bacci yana daukarta, cikin barcin tayi mafarkin suna ihu suna neman taimakon ta, Raudah tana mik’a mata hannu tana kiran sunanta, sai dai duk gudun da take yi bata iya zuwa gurin su, Falmata tana kiran sunanta tana kuka.
A furgice ta farka tana saka ihu, da gudu ya fito daga dakin yazo inda take yana rike ta.
“ Suna kuka ka barni naje gurinsu, Raudah tana kuka zanje na taimake ta, Nabila Falmata!!!!!! Wayyo Allah.” Ta fada tana kuka tana k’ok’arin kwace kanta zata mike.
Jijjigata yayi yana cewa. “ Tsaya!!!.”
Cak ta tsaya tana zuba masa ido na wasu seconds, cike da lallashi ya ce. “ Su waye Falmata din?.”
Kuka ta fashe dashi tana kallon fuskarsa ta ce. “ Y’an uwana ne.”
“ Me ya same su?.” Ya tambaya yana share mata hawaye.
“ Bansan inda suke ba, a gudun boko haram muka rabu dasu.”
Shuru yayi yana binta da ido kafin ya ce. “ Kar ki damu zamu nemo miki su.”
“ A ina? Ka sansu ne?.” Tayi tambayan tana zubawa tattoo din hannunsa ido, zanen maciji ne wanda yayi kyau sosai.
Ji tayi yana cewa. “ Idan aka kira mai zane zaki iya masa bayanin yanda suke ko?.”
Da sauri ta ce. “ Eh zan iya a kira shi.”
“ To kiyi shuru kinji Kanwar Yayanta.” Ya fada yana goge mata kwallan da suke zubowa.
Murmushi tayi tana cewa. “ To Yaya.”
Duba agogo yayi yaga karfe biyu da minti goma na rana, kafin ya ce. “ Tashi muje mu nemo mai zanen.”
Girgiza kai tayi tana cewa. “ Yaya nagaji kaje ka dawo.”
Tabe baki yayi ya tashi ya nufi hanyar fita, sai yaji ta ce. “ Yaya bansan sunanka ba.”
“ Haris.” Ya fada yana murmushi ya juyo ya ganta.
Hannu ta d’aga tana masa bye bye, murmushi ya kuma yi ya fita da sauri dan yaje ya dawo.
Ta kusa mintuna ashirin a zaune bai dawo ba, tashi tayi ta nufi inda taga ya shiga d’azu, tana shiga ta kalli babban frame 🖼 din hotonsa yana sanye da kayan sojoji, yana murmushi wanda ya zama masa dabi’a.
Fita tayi ta dawo falon ta zauna, tana zama aka fara harbi ta ko’ina, a razane ta tashi ta nufi windows ta lek’a, sojoji taga suna ta guduwa ga harbi da ko’ina.
“ Na shiga uku ni Safeera…..” Bata gama fada ba taji boma-bomai suna tashi, ihu ta saka tana fita daga falon da gudu, hanyar da mutane suke bi tabi tana kuka tana toshe kunne, tuni gurin ya bade da hayaki da kura, bom kawai yake tashi, tana gudu mutum ya fado gabanta a muce.
Ihu ta kurma da karfi tana cigaba da gudu.
Tuni garin ya sake rikicewa, hankalin mutane suka tashi ta ko’ina kowa so yake ya tsere da rayuwarsa, sojoji basu shirya ba aka kawo musu attack, jinin da aka zubar yafi wanda aka zubar a watannin biyun da suka wuce.
Ba tare da tasan inda zata nufa ba ta shiga cikin kwalbati ta buya, tana ji motocin boko haram suna wucewa suna harbi, a cikin wajen ta kwana washe gari ta cigaba da gudu.
Sai da aka dibi kwanaki ana kashe rai kafin Allah ya kawo taimako abun ya lafa.
Sosai Safeera ta fita hayyacinta, dan yanzu babu marabanta da namiji, kirjin ya koma kamar kwalta haba ma bayan babu komai, ta rame ta lalace ga rashin kwanciyar hankali da nutsuwa.
Watanta daya tana yawon inda zata kwana, duk inda taga dare ya sameta zata kwanta, washe gari ta cigaba da tafiya, idan taga masu abinci ta rokesu sai su bata taci, haka rayuwarta ya cigaba da tafiya.
Bayan garin Borno ya samu lafiya, Wata rana tana tafiya ta shigo unguwar 20houses, wajen gida dari ta shiga, kowa yana binta da kallo, wata yarinya ta hanga wacce za suyi sa’a da ita.
Yarinyar ta taso tana murmushi ta ce. “ Sannu da zuwa.”
Murmushin yak’e Safeera ta mata tana cewa. “ Sannu.”
“ Sunana Jannah, ga can dakina.” Ta nuna mata dakin dake kusa da band’aki.
“ Ni kuma Safeera.”
Kama hannunta Jannah tayi ta janta zuwa dakinta, daki ne babu katifa ko akwati, kawai zannuwa ne aka shimfida a k’asa, sai kayan sawanta dake kulle a tsumma, sai kula guda biyu. nuna mata gurin zama tayi tana cewa. “ Ki zauna Safeera.” Kafin itama ta zauna.
Ganin yanda bakinta ke a bushe ne ya saka Jannah cewa. “ Na kawo miki abinci?.”
Da sauri ta ce. “ Eh. Eh.”
Murmushi tayi tana tashi ta dauko mata daya daga cikin kulan ta bata, hannu na rawa Safeera ta bud’e, shinkafa ce jollop babu mai sai magi da shima ba wani ji yayi ba.
Ci ta farayi hannu baka hannu kwarya, Jannah na mata murmushi.
Har sai da ta gama ci tas kafin ta dago ta kalle ta, kunya taji tana cewa. “ Kiyi hakuri na cinye miki abinci.”
“ Bakomai, ai mun zama y’an uwa.” Cewan Jannah tana daukar kulan ta ajiye, kafin ta dawo ta zauna kusa da ita, muryanta ta rage tana cewa. “ Ki saurare ni.”
Mai do da hankalinta Safeera tayi duka zuwa gurin Jannah ta ce. “ Ina ji.”
“ Kin ga gidan nan tamkar gidan karuwai ne, sai kinyi karuwanci kafin zaki samu abinci ko ruwa, idan ba haka ba shikenan kin goma baiwa.”
“ Ke ma karuwancin kike?.”
Girgiza kai Jannah tayi ta cigaba da magana da muryan da bataso ajisu. “ A’a fita bara nake, da kuma aikin wanke-wanke a shaguna, sai na samu abinci da kuma kudin da zan siya ruwa jar 🫙 daya.”
Jinjina kai Safeera tayi tana cewa. “ Da yaushe kike fita?.”
“ Da dare nake fita bara saboda lokacin kwaratan nasu suke zuwa, kuma duk d’akin da suka tarar da mace suke shiga… da rana kuma sai na fita aikin wanke-wanke dan shima lokacin kwaratan suna zuwa, kuma idan suka ganki ko ke kikayi kanki baki isa ki gudu ba.”
“ Na shiga uku.” Cewan Safeera hawaye na saukowa.
“ Baki shiga ba tukun zaki shiga dai.” Jannah ta fada cikin zolaya tana dariya.
“ Dariya kike min?.”
“ A’a kuka nake.” Ta sake fashewa da dariya, sai kuma tayi saurin rufe bakinta ta fada a hankali. “ Kiyi shuru kar a san muna ciki a shigo, dan nikam bani da karfin guduwa.”
“ To.” Safeera ta fada a tsure, sai kuma ta ce. “ Me ya sa yau baki fita ba?.”
“ Allah yayi zamu hadu da ke ne.” Ta fada tana d’aga mata gira.
Murmushi itama ta mata, Jannah ta ce. “ Sai kin zama gwaska fa, dan ba haka ba kin shiga uku, nima da kike gani karamar yar hau din kanta ce, babu wacce ta isa ta takani a gidan nan na barta.”
“ Chabbb.” Cewan Safeera tana murmushi.
“ Ke tashi mu fita kafin a shigo dan naji kamar ana son shigowa.” Ta karashe tana kama hannun Safeera suka mike tsaye, kallon kallo suka tsaya yi kafin ta ce. “ Ki dibi takalminki a hannu mu fita a sand’a, duk abunda kunnanki suka jiyo miki kar kiyi ihu dan Allah Safeera, Wallahi ban shirya mutuwa ba.”
Jijjiga kai tayi tana daukan takalminta kamar yanda Jannah ta fad’a, a hankali suka bud’e kofar dakin suka fara sand’a suna tafiya.
Sun zo giftawa ta kofan wani d’aki Safeera taga abunda ya goge mata hadda, mace da namiji ne haihuwar uwarsu suna iskanci sai ihu take.
Cak ta tsaya ta gagara tafiya, Jannah sai janta take amma taki motsi, juyawa tayi tana ganinta, hannu Safeera ta d’aga tana nuna mata abunda ta gani bakinta na rawa ta kurma ihu…
*Kuyi comments dayawa na muku typing dayawa😊*
*SAHIBA✍🏼*
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Comments section
https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP?mode=ac_t
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 22*
Cak ta tsaya ta gagara tafiya, Jannah sai janta take amma taki motsi, juyawa tayi tana ganinta, hannu Safeera ta d’aga tana nuna mata abunda ta gani bakinta na rawa zata kurma ihu.
Da sauri Jannah ta rufe mata baki tana janta da karfi suka fito waje kafin ta sakar mata hannu tana cewa. “ Safeeera ashe baki da wayo? Sai da na gama miki wa’azi akan kar kiyi motsi ko magana, sai gashi ihu ma kike son yi Allah ya cece ni na rufe miki baki, da yanzu abunda ake yiwa wancan shi za’a mana.”
“ Jannah tsoro naji Wallahi, kin ga yanda na kalle su ne abun kyama.” Safeera ta fada tana tufar da yawu.
Dariya Jannah tayi tana jan hannunta suka fara tafiya suna hira har suka iso inda Jannah ke zuwa wanke-wanke.
Cikin minti kadan suka gama wanke kwanukan, matar ta basu kudi dari biyu suka dawo, a hanyar dawowan su Safeera ta ce. “ Jannah nikam ina iyayenki ne?.”
“ Hmm!!! Suna can gida.” Tayi maganar da alama abun yana damunta.
Shuru Safeera tayi ganin yanda ta bata amsa din, ya tabbatar mata da abun yana damunta.
Har suka iso gida babu wanda ya sake magana.
Yanda suka fita a sand’a haka suka koma a sand’a babu wanda ya gansu har suka shige d’akin Jannah.
Bayan sun zauna ne Safeera ta ce. “ Jannah a ina zamu samu ruwa?.”
“ Dibowa zamuyi a rijiya, dana sha dana wanka, ga bokiti na.” Ta karashe tana nuna mata farin bokitin, tashi sukayi suka fito lokacin karfe hudu, gurin rijiyar gidan suka je suka bada naira hamsin suka dibo ruwa bokiti biyu, kafin suka dawo.
Ganin Safeera ta kwanta ne yasa ta ce. “ Safeera bazaki watsa ruwa bane? Naga kayan jikinki duk sun yage kuma sunyi datti, ko zaki canja?.”
Murmushi ta mata tana tashi ta zauna kafin ta ce. “ Jannah bani da wanda zan saka ko na canja fa.”