← Book details Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 39

Sashe 7

Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“ Bani wayana sai ka tafi.”

Mika masa yayi yana tausayin shi, dan yasan yanzu ya fara dan akwai hakkin Jannah ma ga kuma na Safeera, idan har bai nemo su ba ba lallai ya samu sukuni ba.

*UMMAH POV*

Tana zaune akan sallaya tana addu’o’i, hannu ta d’aga sama tana addu’a hawaye na gangaro mata. “ Allah ka fini sanin komai, Allah kai kasan me ke faruwa da dana, ya Allah na roke ka ka dawo min dashi gare ni, Allah ka kare shi a duk abubbuwan da yake yi, Allah ka shiga lamarinsa…. Amen.”

Hawayen ta goge tana tashi ta nade sallayan ta fito falo, yau girkinta ne amma Dad tun da safe ya fita a gidan kuma kafin ya dawo sai dare kusan goma.

Abincin dare ta dafa tuwo miyan egusi, dan favorite din Saif ne, tana gamawa ta had’a a kula ta saka a basket 🧺 ta nufi bangaren shi da addu’ar Allah yasa kar ya mata wulakanci.

Ko da ta isa bangaren a bud’e tun bayan fitan Ammar ba’a rufe ba, sallama tayi ta shiga falon zuciyarta na harbawa cike da tsoron dan nata.

A inda Ammar ya bar shi a nan yake bai tashi ba, yaji sallaman sarai amma bai amsa ba kuma bai daga kai ya kalle ta ba.

Inda yake ta iso tana kallon yanda ya koma, kwalla taji yana k’ok’arin zubo mata tayi saurin saka hannu ta goge tana cewa. “ Saif.”

Bai kulata ba ya cigaba da kallon wayansa, sake kiran sunansa tayi a karo na biyu, nan ma bai amsa ba.

Zama tayi a kusa dashi, da sauri ya tashi tsaye zai tafi, hannunsa ta kama hawaye na zarya akan fuskarta tana fadin. “ Ka saurere ni mana ko sau daya ne yarona, ni fa Mahaifiyarka ce.”

Lumshe ido yayi yana jin wani iri a zuciyarsa game da kukan nata, kuma ya gagara kwace hannunsa daga nata sannan ya gagara tafiya, haka kawai ya tsinci kansa da zama a gefenta din.

Numfashi ta sauke tana cewa. “ Saif kaci abinci dan Allah ba dan ni ba.”

Gyada mata kai yayi duk da kuwa bai juyo ya ganta ba, sake cewa tayi. “ Dubi yanda ka rame kamar ba kai ba me ya same ka ne?.”

Muryansa chan kasa ya furta. “ Babu komai.”

Sanyi taji a ranta jin cewa ya mata magana, hakan yasa ta ce. “ Bari na zuba maka abinci ko.”

“ Ba yanzu zanci ba, idan ina buk’ata anjima zan diba ki tashi ki tafi kaina yana ciwo.” Ya fad’a yana lumshe ido.

Gyada kai tayi tana tashi da sauri ta nufi kofa, tana tafiya tana juyowa tana ganinsa har ta fita.

Tashi yayi ya rufe kofar ya koma ya kwanta.

*DR.TEEMERH✍🏼*

9-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari

Na

Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*

Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

*Page 9*

Tashi yayi ya rufe kofar ya koma ya kwanta.

Kwanciya ya yi amma sai dai ba bacci yake yi ba, idanunsa ne kawai a rufe amma zuciyarsa a bud’e take, tunaninta yake ko a zaune ko a kwance, ya rasa ta ina zai samota.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tashi yana bud’e abincin da Ummah ta kawo masa, duk da yasan favorite dinsa ne amma ba a lokacin nan yake buk’ata ba.

Tsakura ya yi yana rufewa, kana ya tashi ya nufi dakinsa.

*MUMMY POV*

Yau hankalinta kwata-kwata baya jikinta, tun da aka kirata a waya aka ce Saif baya fita kullum yana gida, ta rasa ta wani hanya zata bi dan a kashe mata shi, ga shi bama zuwa gurinta yake ba balle ta saka masa ko poison a abinci.

Tana cikin tunanin zucin ne aka yi sallama, dago da kai tayi tana kallon matar da ta shigo, tuluk’a ce kuma bak’a, ba wani kyau ne da ita ba, sannan bata da tsayi, kawar Mummy ce wacce suke kullawa tare wato Fauziyya.

Murmushi Mummy ta mata tana tashi tsaye, rungumar junansu suka yi Fauziyya na cewa. “ Me ya faru naganki duk cikin damuwa? Akwai wani abu ne?.”

“ Ai gwara da kika zo Fauziyya, zauna tukun na kawo miki ruwa da abinci sai mu fara.” Mummy ta fad’a tana wucewa kitchen dan samo mata abun da zata ci.

Kallon falon Fauziyya ta fara yi tana tabe baki, tare da bacin rai wanda lokaci daya ya bayyana akan fuskarta, a ranta ta ce. ‘ Idan ban fitar dake daga gidan nan ba hankalina bazai kwanta ba sam, kina cikin daula ni kuma ina chan ina neman abun da zan ci, hmmm.’

Isowa Mummy tayi da tray a hannunta ciki dauke da drinks da abinci, ajiye mata tayi tana cewa. “ Ki ci kafin mu daura.”

“ To.” Cewar Fauziyya ta fara cin abincin tana sauri, dan yunwa dama take ji.

Sai da ta gama cinyewa tas kafin ta dago kai ta kalli Mummy tana fadin. “ Ina sauraranki kawata me yake gudana?..”

Gyara zama Mummy tayi tana cewa. “ Fauziyya sanin kanki ne cewa tun da Alhaji ya auro ni ban taba haihuwa ba ko?.”

“ Gwaraii ni ce shaida.”

“ Yawwa, kuma kinsan bada mahaifana nayi kafin har aka min aiki akan Alhaji dan duk na samu na mallake shi.”

“ Uhm me ya faru to ai naga kin mallake shi din, dan aikin malamin nan baya fadi k’asa banza.”

“ Eh tabbas na mallaki Alhaji sai dai ba kalan yanda nakeso ba Fauziyya, na mallake shi ne na wucen gadi kafin wancan kafurar matar tasa tayi aika-aikanta ta kwace shi.”

“ Gaskiya Lubuna kinyi sake, wai har a kwace miki mijinki mtswww.”

“ To Fauziyya ya zanyi ne? Ni yanzu wannan dan iskan yaron nashi nakeson kashewa ma, na saka a kashe shi wai ya bace musu.”

“ Kina nufin Saif wai?.”

“ Eh shi nake nufi.”

“ To muje wajen bokanmun mana ai kinsan karamin aiki ne inde kashe mutum ne.” Cewar Fauziyya tana washe mata baki.

Jijjiga kai tayi tana cewa. “ To bari na dauko mayafi sai muje ko.”

“ Eh maza tashi kiyi sauri dan zaune bata kamaki ba.” Tayi maganar tana nuna abun ya dame ta, Mummy na shiga ciki Fauziyya ta kwashe da dariya tana bude gorar 5alive ta kifa a baki.

*SAFEERA POV*

Fitowa tayi daga cikin bukkan tana kallon gurin, gida ne a zagaye da wajen sai bukka guda ukun da suke wajen, ga mishiyoyi nashan iska har da bishiyar mango wanda ya zubo k’asa kuma ya nuna, gefe kuma ga na lemon.

Murmushi tayi tana gyara rigar da yake jikinta wanda Inna ta bata, doguwar riga ce matso mai ratsin ja da blue, tsayin ya mata rawa sosai amma rigar cib-cib dinta, dan har saman kirjinta daya matsa yana nunawa, ta danyi haske sai dai ba sosai ba kuma fuskarta ya dan cika, hancin nan ya fito ga ido gwanin ban sha’awa, sai karamin lips 👄 nata da yake nan pink kullum.

Gyale baki ne irin ma abaya a kanta, gashin kanta ya dan fito kad’an, ana kallon bakin gashin.

Takowa ta fara yi zuwa gurin bishiyar mango 🥭 tana murmushi, zama tayi a kujeran da yake gurin tana tsinko guda daya, butan da yake gabanta ta dauka sai taji da ruwa, wanke mangon tayi kafin tayi bismillah ta fara sha har da wani lumshe ido dan mangon ya nuna sosai kuma zaiyi zak’i.

Inna da fitowarta daga band’aki kenan hannunta rike da buta ta tsaya kallon ta, murmushi ita ma tayi tana isowa gurin da take ta zauna.

Bud’e ido Safeera tayi tana kallon Inna, kunya taji hakan yasa ta sunkuyar da kai tana fadin. “ Inna yaushe kika iso?.”

Murmushi Inna ta mata tana cewa. “ Ina zaki sani kuwa tunda kin lumshe ido kina jin dadin mangoro.”

Dariya ta mata wanda ya bayyanar da asalin kyau dinta, hakoranta da suke farare tas suka bayyana wushiryanta ya nuna, karamin dimple dinta ya lotsa.

Inna a zuciya ta furta . ‘ Tabbas Allah yayi halilta, Masha Allah.’

Muryanta taji tana cewa. “ Inna ba mangaro ake cewa ba fa, Mango ake fadi.” Ta karashe da dariya.

“ Yoo ni ina nasani, dama Jannah ce mai wannan takuran dole sai ta gyaramin, ke ma gashi kinzo.”

“ Inna wacece kuma Jannah?.”

Numfashi ta sauke kafin ta ce. “Jannah diyata ce, sai dai kwanaki biyu baya an nemeta an rasa sakamakon abun da Bappa ya mata.”

Mai do da hankalinta tayi tana fadin. “ Inna me Bappan ya mata?.”

“ Safeera kenan Bappa akan kudi zai iya aikata komai, ciki kuwa har da siyar da yarsa….

More comments more typing 👌🏻🫤

*DR TEEMERH✍🏼*

10-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari

Na

Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*

Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

*Page 10*

Mai do da hankalinta ta yi tana fad’in. “ Inna me Bappan ya mata?.”

“ Safeera kenan Bappa akan kudi zai iya aikata komai, ciki kuwa har da siyar da y’arsa.”

A razane Safeeera ta ajiye mangon da yake hannunta tana fad’in. “ Inna bangane ba sam, kina nufin na gudu ban tsira ba? Ita Jannah tana ina?.”

Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tana cewa. “ Ina ga yau zai yi kusan wata bakwai ko takwas rabona da saka ta a ido.”

“ Me ya faru da ita to?.”

“ Dogon labari ne.” Cewar Inna.

“ Koman tsayinsa zan saurara, burina kawai naji me ya faru.”

Gyara zama Inna tayi tare da cewa. “ Jannah tun tana da shekara sha shida suke tare da wani saurayinta Mai suna Saifullahi….”

“ Saifullahi!!!.” Safeera ta maimaita sunan.

Dago kai Inna tayi ta ce. “ Kin san shi ne?.”

Saurin girgiza mata kai tayi ta ce. “ A’a sunan ne kawai na tuna da mai shi, amma ina jinki sai ya akayi?.”
Chapter 7 · 0% Book details