Sashe 15
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru tayi, tunawa da zamanta da tayi a 20 houses tayi, lokacin da take magana da kawarta. < Ni ma Bappa na ne zai min auren dole shi ne na gudu nazo gurin saurayina>…. <Sunana Jannah ke fa Safeera>… < Ya koreni bayan munyi mu’amala da shi>… < Yau watan mu zai yi biyar rabona da shi har da iyayena>… < Na zabi rayuwar takaici ne kawai>.
Ganin kamar bata hankalinta ne yasa ya tabata, a firgice ta juyo tana kallon shi, idanunta ya dan ciko da kwalla ga tsoron da taji lokaci daya ya kama ta.
Da mamaki ya ce. “ Akwai wani abu ne? Me ya same ki?.”
Girgiza masa kai tayi kafin ta mike tsaye tana fadin. “ Inason zan je 20 houses.”
Mikewa ya yi yana fadin. “ Ba zaiyu ki fita ba ai, yau fa aka daura mana aure, kuma me zakije yi a wannan gidan?.”
Girgiza masa kai tayi ta ce. “ Dan Allah kar ka hanani zuwa, akwai abun da nakeson yi ne na roke ka?.” Ta hade hannayen ta kamar zata yi kuka.
Shuru ya yi kafin ya zaunar da ita ya ce. “ Ki kwantar da hankalinki kinji, zan barki kije ko ince zamu je tare amma ba yau ba.”
“ Yau ne karo na farko da na nemi alfarma a gurinka, dan Allah fa.”
Iska ya furzar kafin ya ce. “ Shikenan tashi ki shirya sai muje.” Bai gama rufe baki ba ta mike da sauri, ta nufi daki.
Da ido yabi bayanta kafin ya tattare kayakin da ya siyo mata ya nufi dakin.
Ciro mata jan abaya yayi da mayafinsa ya bata ta saka, bra da pant da underwear duk ya ciro mata ya mika mata, dauka tayi zata nufi toilet ya ce. “ A nan din bazaki iya shiryawa bane?.”
Sunkuyar da kai tayi tana kallon yatsunta, tabe baki yayi ya ce. “ Sai kiyi sauri it almost 5 o’clock.” Gyada masa kai tayi ta nufi toilet, sauri-sauri tayi ta shirya, abayan ya mata kyau sosai tayi roiling din veil din ta fito.
Murmushi ya sakar mata ya ce. “ Kinyi kyau.”
“ Nagode.” Tashi yayi suka fito tana biye dashi a baya.
Gurin parking lot suka nufa Sageer yayi sauri ya taso, bud’e musu baya yayi suka shiga shi kuma ya shiga mazaunin driver, aka wangale musu get mota na gaba na security sai nasu na baya ma na security’s.
Shuru motar yayi kowa da tunanin da yake yi, katsai shuru yayita hanyar tambayar Sageer. “ Kun gano wadan da suke binmu ne?.”
“ Sir ba’a gano komai game da su ba, amma…” burki ya danna da karfi sakamokon motan gabansun da ya kaucewa wani mota fari.
Kafin su ankara aka fara kai musu harbi ta ko’ina, da sauri Sageer ya ce. “ Ku sunkuya k’asa.” Janyo Safeera Saif yayi suka zube k’asa.
Motar da su Saif suke ciki suka nufa da gudu suna harbi, wasu mutane ne kusan su biyar ko wannen su hannunsa da bindiga yana harbi, motar Saif suka nufo gadan gadon, security’s nasa ne suka fito suma suka fara kai musu harbi, bindiga Sageer ya ciro ya saka harsashi a ciki zai fita Saif ya ce.
“ Sageer ka kula.”
Jijjiga kai yayi ya fita da gudu daga motar yana harbi, kuka Safeera ta fashe da shi tana toshe kunne, jawota jikinsa yayi yana rungume ta tsam.
Jiniyar motar yan sanda ne ya kewaye gurin da ambulance 🚑, ajiyar zuciya Saif ya sauke ya ce. “ Kukan ya isa haka. Numfashi ta fara saukewa tana rage kukan nata.
A waje kuwa harbi suke kaiwa junansu ko tausayi babu, an kashe security’s guda uku yayin da aka kama daya daga cikin yan ta’addan.
Sageer kuma an harbe shi a ciki ta gefe, sai jini yake zubarwa.
Y’an sanda suna zuwa yan ta’addan suka gudu, mota daya ya bisu na sojoji har hanyar da suka yi.
Motar Saif dan sandan ya bud’e yana sara mishi, fitowa yayi hannunsa rike da nata, ganin Sageer a kwance cikin jini ne yayi mugun d’aga masa hankali, da gudu ya saki hannun Safeera ya nufi inda Sageer yake kwance.
Fito da gadon daukar mara lafiya akayi, inda Sageer yake kwance suka nufa suna daurasa akan gadon, suka shigar da shi Ambulance aka wuce da shi asibiti.
Komawa gurinta yayi ya ja hannunta suka shiga mota suka bi su.
Direct emergency aka wuce dashi ganin yanda jini yake zuba.
Zama Saif yayi yana jawo Safeera kusa da shi, duk ta rude ta kidime kana tabata zata furgita.
*DAD POV*
Yana zaune a falo kusan karfe bakwai da rabi yana kallon labarai, nan aka manna hoton Saif ana fadar yan ta’adda sun tare shi a hanya har anyi asarar sara rai uku, sannan an kai mutum daya asibiti.
Da sauri Dad ya mike yana furta. “ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un.!!!”
Ummah da shigowarta kenan taga labarin ta fashe da kuka tana fadin. “ Sun kashe min yaro.”
Da sauri Dad ya danna number Sageer amma ba’a dauka, number security wanda yake bin Saif yayi shima ba’a dauka ba. “ Hasbunallaha wani’iman wakil!!!!!!!!. “ Abun da ya ta maimaitawa kenan.
Ummah kuma sai kuka ta rasa me ke mata dadi, number Saif Dad ya kira amma yana ta ringing ba’a dauka ba, sau biyar yana kira ba’a dauka ba.
Number Ammar ya kira, ko ringing bai gama yi ba Ammar ya dauka, Dad ya fara fadin. “ Ammar kuna tare ne?.”
Ammar da yake tuki shima a rikice zai je asibitin ya ce. “ Dad yanzu nake hanyar zuwa gurinsa.”
“ Wani hospital ne?.”
“ TH ne.” Ammar ya fada yana kashe wayan, a 360 ya tafi zuwa hospital din.
Bai tsaya jiran komai ba Dad ya nufi hanyar fita da sauri Ummah ta shiga ta dauko hijab ta biyo shi, security’s duk sunji abunda ya faru hakan yasa da Dad da Ummah zasu fita mota hudu ne ya musu rakiya.
*MUMMY POV*
Ta kasa zaune ta kasa tsugunne, number wayansu take ta kira amma ba’a picking.
Cilli tayi da wayar ta koma ta zauna, Radiya ce ta shigo da gudu tana kuka tana fadin. “ Mummy sun kashe Saif.”
Da sauri Mummy ta mike tsaye tana cewa. “ Ina gawarsa din to?.”
“ Mummy yana asibiti yanzu su Dad suka tafi Ummah tana ta kuka.”
“ Ayya!!! Abun tausayi.” Mummy ta fada tana dan murmushi.
Da kallo Radiya ta bita ta ce. “ Mummy nasan da sa hannunki a ciki, amma bakomai akwai Allah, ki jira sakayya.” Ta karashe tana fita daga parlon.
Tabe baki Mummy ta yi ta bude fridge ta dauko rufaida da ruwan sanyi ta zauna ta fara sha tana lumshe ido, wayanta da tayi cilli dashi ta dauko ta dannawa kawarta kira wato Fauziyya.
Tana dauka ta ce. “ Yanzu nake ganin labarai wai Saif ya mutu?.”
Dariya mai sauti Mummy tayi ta ce. “ Eh haka ne.”
“ Kawata ke kika kashe shi ko?.”
“ Tabbas ni ne nan na kashe dan banza, kisa me kyau ma.”
“ To yanzu ribar me kika samu?.”
“ Ribar raba gado mana, kinga dai-dai gadonmu zai zama da ita uwarsa din.”
“ Hhhhh kawata kenan.” Fauziyya ta fada tana kashe wayan.
Da ido Mummy tabi wayan tana tabe baki.
*FAUZIYYA POV*
Dariya ta kyalkyale dashi tana fadin. “ Yanzu zaki gane shayi ruwa ne, hhhh ki jira zuwana kawai dan sai na kaiwa Safwan voice din nan yaji, idan yaso ya sake ki ni ya aure ni.”
*MOM POV*
Tun bayan barowanta bangaren Saif take jin wani wari yana tashi a jikinta, ga gabanta din da take jin yana fitar da ruwa da bata gane kansa ba.
Toilet ta shiga ta cire kaya dan duba meke tafiya.
Ihu ta saka lokacin da idanunta ya sauka akan tsutsotsin da suke jikin pant dinta. “ Na shiga uku na mutu na lalace, wai meke faruwa da ni ne.”
Ruwa ta zuba ta fara wankewa amma baya raguwa sai ma sake fitowan da yake yi.
Ga dauri ta saka pad ta saka doguwar riga ta nufi hospital a haukace.
Tana shiga taga motocin su Dad da Saif, bangaren female ta nufa da sauri dan kar su ganta, tana shiga ta samu likitan da take zuwa gurinsa karban maganin abotion.
Yana ganinta ya fara washe baki dan yasan yana samun kudi a gurinta. “ Hajjaju makkatin.” Cewan Dr Ubaidu.
“ Bata wannan nake ba Dr ka duba lafiyata tun daga sama har k’asa, ka min general checkup.” Ta fada a rikice tana zama a kujera.
“ Ok.” Ya fada kafin ya dauko syringe 💉 ya dibi jininta.
Abun ka da kudi tuni ya kai lap aka fara gwaje-gwaje dan tace a take take son result.
*SAIF SAF POV*
Ko motsin kirki bata yi, tuni zazzabi mai zafi ya rufeta, ko matsawa daga jikinsa ta gagara.
Dubanta yayi ya ce. “ Zazzabi ya kama ki.”
Bata ce komai ba sai sake shiga jikinsa din da take yi tana fitar da zazzafar numfashi, hannu ya daura a wuyanta jin zafi yasa ya furta. “ Subhanallah.”
Daukarta yayi cak zai nufi emergency da ita, dai-dai lokacin da Ummah da Dad suka shigo.
Har da dan gudu Dad ya saka ya iso gurinsa, kallon su yayi ya ce. “ Dad Ummah me ya fito daku a wannan yanayin?.”
Ummah ta kalle shi ta ce. “ Saif cewa akayi fa ka mutu.”
“ Ummah idan ma na mutu ai sai ku jira a kawo muku gawata, amma a wannan yanayin zaku fito da ba’a san wadan da suka aikata laifin nan ba.” Ya karashe a fusace.
Cike da tausayi Dad ya ce. “ Saif Ubanka, ko baka ji ba?.”
Kau da kai yayi yana k’ok’arin shiga emergency din.
Wani Doctor ne ya iso yana cewa. “ Sir ba zaiyu ka shiga ba.”
Wani kallo ya masa ya ce. “ Ita da bata da lafiya fa?.”
“ Sorry Sir amma ga daki a gefen nan za’a iya kwantar da ita a duba lafiyarta.”
Nufan dakin yayi su Dad na binsa, wasu daga cikin security’s da police suka bishi yayin da sauran suka tsaya a kofar emergency.