← Book details Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 39

Sashe 3

Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“ Malam hannuna fa zaka karya min.” Ta fada a kufule tana zaunar da shi ta jingina shi da jikin step, tashi zata yi ya kama hannunta ya furta. “ Ki zauna dani.”

“ Kamar ya? Nifa Malam ka fara takura min billahil lazi, haba dan Allah nifa kwata kwata banyi tunanin zina zanzo na aikata ba, da Wallahi bazan zo ba, dana gwammace na zauna a cikin wahalan da nake da BAKAR KAUNAR da ake nunamin, duk shekarun da suka wuce banyi zina ba sai yanzu, wani wahala ne ban sha ba, duk tanadin da nayi ka rushe su, ka mayar dani tamkar karuwar gida, ka dauko ni kawai dan kayi zina dani ka biya ni, tirr da wani arzikin ma Wallahi, mutum iya mutum amma….” Maganar ne ya katsai lokacin da ta lura yana shirin fadiwa hawaye na bin fuskarsa.

Da sauri ta rike shi ta durkusa tana cewa. “ Kai!!! Kai!!! Ka mayar dani idan yaso sai ka mutum, kar kasa naje prison.” Tana yi tana girgiza shi.

Wayansa ne ya soma ringing, hannu tasa cikin aljuhunsa tana ciro wayan, sunan dake gaban screen din ta gani an rubuta da Sageer Boy, ba tare da wani dogon zance ba ta daga wayan.

Ta cikin wayan aka ce. “ Sir baka fito ba har yanzu, dare yana yi.”

“ Dan Allah ka shigo ya suma fa.” Ta fada tana yasar da wayan ta cigaba da Jijjiga shi, dan yanzu ta gane ba wasa yake mata ba.

Bango kofar akayi aka shigo da gudu, a razane ta juyo tana kallon kofar, mutumin da suka dauko ta ne, da sauri ya iso yana cewa. “ A garin ya? Me ya same shi? Ke kika kashe shi ko? Mutumin da ba lafiya dashi ba shine kika kashe shi ko? Idan ya mutu ke ma sai kin mutu.”

A haukace ta ce. “ Sai dai mu mutu zaka ce, dalla Malam taya zan kashe mutum? Dan yazo fadi na rike shi shikenan ni na kashe shi.”

Cike da takaici Sageer ya ce. “ Ni bansa me Saif ya gani ba ya nace sai ya kwanta dake, karuwa kawai.”

“ Idan ni karuwa ce kai kuma kwarto ne ai, mara hankali kawai.” Ta fada a kule tana hararan shi.

Wani damke hannun da Saif ya mata ne yasa ta dawo da hankalinta kan shi, haka ma Sageer din, da sauri ya ciro waya yana kiran wani number.

Kansa ta daga ta daura akan cinyarta, Sageer ya ce. “ Me ya same shi?.”

“ Ban sani ba fa, kawai muna tsaye dana tambaye shi iyayensa shine ya dafe kai daga nan kuma ya koma haka.” Ta fada a raunane wanda taji lokaci daya tausayinsa ya kama ta.

Gyada kai yayi bai ce komai ba ya nufi kofa jin ana kwankwasawa.

Hannun shi ta rike tana cewa. “ Dan Allah ka tashi.” Ta yi maganar tana goge hawayen da har yanzu suke gangaro masa.

Sageer ne ya dawo da wani Doctor, gurin su suka iso Dr ya ciro kayan gwaji ya fara masa, idanunta na kan su tana karantar yanayin su, dan tsoro take ace ya mutu dan tasan direct prison za’a kai ta.

Dago da kai Dr yayi yana kallon ta wanda ita ma shi take kallo zuciyarta na harbawa, muryan Sageer taji yana cewa. “ Me ya same shi?.”

“ Kai ma kasan condition da yake ciki, kuma sai da nace kuna kulawa da yana yin shi, yana critical condition kai ma shaida ne, to me yasa zaku saka ciwon shi yana tashi?.” Dr ya fada ranshi a bace.

“ Yanzu dai Dr ka mishi alluran da ka saba masa, next time za’a kiyaye.”

Muryan Safeera har rawa ya fara, kamar wacce akace yana da ciwon HIV haka take ji, da kyar ta kwakulo yawu daya bushe ta furta. “ Wani irin cuta ne dashi?.”

Kallon ta Dr din yayi kafin ya ce. “ Matarsa ce?.”

Girgiza kai Sageer yayi ya ce. “ Cousin nasa ce…

*Nikam ko baya muku dadi ne littafin🥹 babu wanda yayi comments fa, idan bayayi ku fadamin sai na bari ku huta 🥹*

DR TEEMERH✍🏼

4-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari

Na

Fatima Isa Manu
DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )

*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪*

*Page 4*

Kallon ta Dr din yayi kafin ya ce. “ Matarsa ce?. Girgiza kai Sageer yayi ya ce. “ Cousin nasa ce.”

“ Ok.”

Kallon ta Sageer yayi ya ce. “ Zamu shigar da shi ciki dan a samu a masa allurai sannan a sa masa drip.”

Gyada kai tayi, Dr Rahuz da Sageer suka kama shi zuwa dakinsa, har suka shiga bata tashi ba sai idon da take bin su dashi, ta dan dade a gurin kafin ta mike ta nufi nata dakin ta shiga.

*MOM POV*

Yau girkin ta ne, dokar Dad ne ya saka duk ranar mai girki a bangaren ta za’a ci abincin dare, hakan yasa aka jera abinci a daining.

Fitowa Mom tayi daga daki tana tafiya tana girgiza jiki, duk suna daining table ita kadai kawai suke jira, kallo daya Ummah ta mata tana dauke kai, Mummy kuma taja tsaki wanda ya fito fili.

Dad da yake zaune ya daga kai ya kalle Mummy yana girgizawa, Radiya kam abun har mamaki yake bata, sun tsufa ma amma basu daina kishi ba, kai kawai ta girgiza tana cigaba da danna waya.

Isowa Mom tayi tana jan kujeran dake kusa da Dad ta zauna, sannan ta zubawa Dad kafin kowa ya zuba abun da zai iya ci aka fara ci.

Cokali biyu Dad yayi ya tsaya yana kallon Ummah ya ce. “ Ina Saif ne?.”

Ajiye cokalin hannunta Ummah tayi kafin ta ce. “ Rabo na dashi tun jiya da safe, wai zai je aiki, dana tambaye shi wani irin aiki ne sai yace ba sai na sani ba.” Ta karashe a raunane.

Gyada kai Dad yayi kafin ya dubi Mummy ya ce. “ Ke fa kinsan inda ya je?.”

Ko a jikinta ta ce. “ Alhaji kai da danka ni kuma ina zan san inda yaje? Ni a su wa.”

“ Ban ce ki min zancen banza ba Jamila, tambayar ki nayi idan baki sani ba ya isa ba sai kin min rashin kunya ba.”

“ Sai ayi hakuri.” Mummy ta fada tana bata fuska.

Kallon Mom yayi yana fadin. “ Ke fa?.”

“ Alhaji ya ce zaiyi tafiya na kusan 1 week ko yafi ma.” Mom ta fada a yanga.

Gyada kai yayi bai ce komai ba, kallon Mom Radiya tayi dan tasan tabbas karya ta fada amma babu damar karyatawa.

Ran Ummah fal tambaya amma tayi shuru dan bata san waye zai amsa mata tambayar ba, hakan yasa ana gama cin abincin ta mike ta nufi part din ta, Mummy ma ta nufi nata , Radiya kuma ta wuce dakinta.

*MUMMY POV*

Tana shiga bangaren ta ta saka key, sauri tayi ta nufi dakinta ta shige.

Wayanta dake ringing tun dazu ta kalla tana danna kiran wanda ya kira ta, ringing biyu ana uku aka dauka, surutu ake ta zubawa ta cikin wayan, ranta a bace ta soma cewa.

“ To uban me kuke jira da baku kashe shi ba, ai sai da nace muku ya fiku wayo kuma idan ya kufce ba lallai ku kama shi ba, ya gane kuna binshi ne shiyasa ya bace muku.”

Banji mai aka ce ta cikin wayan ba sai murmushin da tayi tana cewa. “ Kun kyauta, sai naji sakamako mai kyau, zan baku tukuici mai girma da tsada.” Nan ma magana akayi sai ta kwashe da dariya ta kashe wayan.

*UMMAH POV*

Ko da ta shiga dakinta rufewa tayi ta fashe da kuka mai cin rai da zafi, hoton danta kwalli data tayi tana dauka ta runguma tare da fashewa da wani matsanaicin kuka.

Yaro dayan da take dashi yanzu an raba ta dashi, ko gaishe ta baya yi, baya ma ganin ta a matsayin uwa, ace wai zaiyi tafiya amma bazai zo ya fada mata ba.

Sake sakin kukan tayi tana jin radadi da zafi a zuciyarta, ta dade tana kukan da taga kukan bazai mata komai bane ta tashi ta dauro alwala ta fara nafilfilu da addu’a akan Allah ya kawo mata mafita da sauki, sannan ya kare mata danta da duk sharrin dake tunkaran shi.

*SAFEERA POV*

Tana shiga dakin toilet ta nufa dan sake gasa jikinta, sai da taji dai-dai kafin ta watsa ruwa ta fito amma har yanzu tana dan dingishi sai dai ba sosai ba.

Kwantawa tayi dan ta huta bacci ya dibe ta, ba ita ta farka ba sai kusan eight, tana tashi ta watsa ruwa ta dauro alwala ta gabatar da sallah, kafin ta nufi dakinsa dan dubawa ko ya farka.

Ya dade yana bacci, dan ya kwashi kusan awa uku me kyau yana bacci bai farka ba, sawun ta kusan uku amma yana bacci.

Yanzu ma dawowa tayi dan ta duba ko ya farka, shigowar ta yayi dai-dai da bud’e idon da yayi, sauke su yayi a kanta yana binta da kallo wanda ita ma shi take kallo.

A hankali tayi sallama tana shigowa ciki, a kan bedside ta zauna tana kallon shi tare da cewa. “ Ka farka ya jikin?.”

“ A’a mutuwa nayi ban farka ba.” Ya fada a takaice yana zuro da kafarsa daga kan gadon.

Tabe baki tayi tare da fadin. “ Daga tambaya.”

Bai ce mata komai ba ya mike ya nufi toilet, da ido ta bishi tana kau da kai tare da furta. “ Ga kyau amma ba hali.” Wayansa ta gani a kan gado.

Hannu ta kai ta dauka tana kunnawa, a bude yake ba password hakan yasa ta wuce wajen kira, missed calls sun fi goma aka masa, ba ta bi ta kansu ba ta fara danna wasu number, danna kira tayi tana mikewa da sauri ta nufi hanyar kofa da wayan, tana k’ok’arin bud’e kofan ne ya danne da hannu.

A gigice ta juyo tana kallon shi dan ita bata yi tunanin zai fito yanzu ba, fuskarsa a tamke yake kallon ta cike da zargi, kafin tayi wani magana ya jefa mata tambaya. “ Wacece ke?…

DR TEEMERH✍🏼

5-

💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔
Gajeran labari

Na
Chapter 3 · 0% Book details