Sashe 28
Bakar Kauna Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru tayi ta fada tunani tana dan lumshe ido, kanta taji yana sara mata da sauri ta kama kan tana kama rigar Ammar dan shine kusa da ita, Saif ya bisu da kallo yana fadin. “ Kanta din ko?.” Yayi saurin riketa, ta yanda Ammar bazai fahimci kishi ne yake damunsa ba ya janyeta daga jikinsa.
Ammar ya bude motan yana dauko ruwa a gora ya bawa Saif dan ya bata tasha, ya bude murfin ya kafa mata a baki, sai da tasha rabi kafin ya sauke yana cewa. “ Safeera.”
Ammar ya ce. “ Ku shiga mu bar nan gurin kasan ba security kar wani abu ya faru.” Da haka ya bude musu suka shiga.
Shuru babu wanda yayi magana a motan, can Ammar ya ce. “ Amma Saif sai nake ganin kamar aje hospital dai.”
“ Nima yanzu hankalina yafi tafiya can, dan gaskiya na fara tsorata da lamarin ta, kamar wata cyco.” Ya fada yana kallon Safeera wacce har yanzu idanunta a lumshe.
Ammar ya ce. “ Ato dai.”
Jon ya tambayi Ogan nasa. “ Sir hospital din zamuje ko Bulunkutu?.”
Ammar ya karbe da cewa. “ Hospital.”
Saif kuma ya ce. “ Bulunkutu.”
“ Saif zaka yi adalci kuwa, matarka ba lafiya amma zaka wuce gurin budurwa.”
Hannu ya daga masa alaman ya isa, daga haka babu wanda ya sake cewa komai har suka isa gidan su Jannah.
Suna isowa Baffa yana zuwa, Ammar yayi murmushi ya ce. “ Baffa manya tun da aka samu mota aka hanamu sakat.”
Saif yayi murmushi yana cewa. “ Sirikin nawa kake fadawa haka?.”
“ Ohh haka fa, kaina k’asa.” Suka sauko daga motan, ya dagawa Safeera glass ya kunna mata AC, ta kafa fuskarta a jikin glass din tana kallon su.
Baffa ya iso da wuri yana cewa. “ Alhaji Allah yaja kwana, kaga mutumin kirki.”
Saif ya dan sunkuya yana cewa. “ Ina wuni Baffa.”
“ Ahh lafiya kalau ya gajiyan ku?.”
“ Alhamdulillah.”
“ Ku shigo mana.”
Baffa yayi gaba Saif ya mara masa baya, Ammar ya juyo ya kalli Safeera yanda tayi, tausayinta ya kama shi a ranshi ya ce. ‘ Allah zai kawo miki mafita In Sha Allah, amma bakiyi sa’an miji ba.’ Da haka ya wuce ciki.
Suna shigowa Jannah ta mike da sauri zata shiga ciki, Baffa ya daka mata tsawa da maganar da yasa ta tsaya. “ Idan kika sake taku daya sai na tsine miki.”
Dole tasa ta juyo ta koma ta zauna, Saif ya bita da kallo yana murmushi, ya durkusa ya gaishe da Inna, ta amsa masa ba yabo ba fallasa.
Baffa ya ma Inna magana ta yare nan ta tashi ta kawo musu fura da ruwa, ya amsa yana godiya, suka dan yi hira kadan kafin ya tashi zai tafi ya ajiye musu kudi, ya fito Ammar na mara masa baya.
Ganin sun fita ne ya saka Baffa dauke kudin da wuri ya saka a aljuhu yana cewa. “ Yar kwal uba tashi kije ki same shi.”
Kamar tayi kuka ta dauki hijabinta ta fito.
Yana tsaye ta iso tana hararan shi, yayi murmushi yana cewa. “ Amarya ba kya laifi.”
“ Allah ya kiyaye.” Ta karashe fadan tana sauke ido akan Safeera wacce ta manna fuskarta da glass dib tana kallon duk abunda yake faruwa.
Da sauri ta isa gurin motar tana kallon ta, Jannah ta ce. “ Safeera.”
Murmushi ta mata hawaye na saukowa daga idanunta, Jannah ta girgiza mata kai tana fadin. “ Me ya faru Safeera? Ni dama nasan ba lafiya ba, nasan akwai abunda ya same ki.”
Duk kallon su kawai suke, abun ya daurewa Ammar kai sosai, Saif kuma ya zuba musu ido yana mamakin irin kauanr da yake tsakanin su, dan ita ma Safeeran kullum zancen ta Jannah amma kwana biyun nan ta daina ko magana, daga bacci sai murmushi.
Ammar yazo ya bud’e mata murfin motan ya koma gefe.
Da sauri ta rungume ta tana kuka. “ Safeera ko ya cutar da ke ne? Ko ya miki wani abu ne? Dan Allah kiyi magana.”
Kai kawai ta girgiza ta ce. “ Babu kowa.”
Ta tallafo fuskarta ta ce. “ Ki ga ki fadamin komai kinji, Jannah dinki ne fa.”
Lumshe ido tayi tana tuna sunan, a hankali ta furta. “ Jannah.” Tana kama kanta da karfi.
*SAHIBA CE*✍🏼
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 30*
*END OF BOOK ONE*
Lumshe ido tayi tana tuna sunan, a hankali ta furta. “ Jannah.” Tana kama kanta da ƙarfi wanda taji kamar zai tsage.
Jannah ta rike ta tana fad’in. “ Safeera, ko dai kin manta ni ne?.”
Ta dago kanta ta kalleta ta ce. “ Na manta inda nake jin sunan ne.”
Da mamaki Jannah ta ce. “ Ko dai tayi loosing din memory ni?.” Ta tambayi Saif shi da Ammar.
Ammar ya nuna Saif da hannu alamun ta tambaye shi, Saif ya ce. “ A’a ban dai sani ba, coz kwana biyun nan ta ke nake.”
Cike da haushi ta ce. “ Ita kuma ta mutu ko, ba da ni za’ayi wannan jagaliyancin ba, ka fara samo lafiyar Safeera sannan ka samo hankalina.”
Safeera dai kallon su take wai ita ce bata da lafiya, bayan kuma duk abunda suke fada tana ji.
“ Jannah ki koma ciki abun ki zamu sake dawowa.” Cewan Ammar yana zagayawa ya shiga motan, Saif zaiyi magana Jannah tayi saurin shiga ciki.
Iska ya fuzzar yana bude motan ya shiga, Jon ma ya shiga suka tafi.
Sai da aka sauke Ammar kafin suka wuce gida.
*MOM POV*
Idan ana zancen dan iska na bugawa a jarida to Ashiru ya kai, ya hana Mom sakat, duk bayan awa daya sai ya turo mata da videos yana mata barazana.
Tuni Mom ta zabge ta rame ta fita hankalinta, ta rasa ya zatayi da rayuwarta, kukan ma tayi har ta gaji, ta rasa mafita ta ko’ina.
Tana zaune a tsakiyar dakin taji an bude kofa, a razane ta juya suna hada ido da Radiya.
Toshe hanci Radiya tayi tana fadin. “ Mom lafiya baki fito ba tun jiya?.”
“ Radiya kije kawai, nima yanzu ta kaina nake.” Ta kalli yanda ta rufe hanci tana fadin. “ Kema kina jin warin ko?.”
Ta gyada kai ta juya ta fice dan amai ne ya taso mata.
Mom ta wani fashe da kuka tana ihu, message ne ya shigo mata, taji zuciyarta ya tsinke dan tasan waye ne, hannunta na rawa ta dauki wayan tana kallo. “” Saura kwana daya fa Hajjaju.””
“ Na shiga uku na lalace, na lalace na lalace, wayyo Allah na.” Ta sake fashewa da kuka, number bokanta ta kira, yana dauka ta fashe masa da kuka tana fadin. “ Boka komai ya lalace.”
Ta cikin wayan aka ce. “ Mai wayan yana kwance ba lafiya an saka masa drip.”
“ Kutumar jarr uba… Allah ya isa tsakanina da kai.”
Ta cikin wayan aka ce. “ Ke malama ba fa me wayan bane.” Ya kashe abun shi.
Tabi wayan da kallo tana fadin. “ Ta faru ta k’are, ya cuceni ya kashe ni.” Ta fashe da kuka tana tashi tsaye ta daura hannu a kai.
*MUMMY*
Radiya ce ta shigo da hanzari, tun daga falon ta soma kiran Mummy tana cewa. “ Mummy! Mummy!!.” Mommy da take daki ta fito da sauri tana cewa. “ Radiya uban me ya faru ne, kin san halin da nake ciki kuwa da kike kirana.”
“ Mummy halin da kike ciki kadan ne akan na Mom.” Cewan Radiya tana kama kwankwaso.
Mummy ta matso tana fadin. “ Me ya faru da ita?.”
“ Hmm! Kinsan warin da take yi kuwa, kamar bugaggen nama.”
“ Hahaha 🤣, Allah shi kara, tabi bokan nata ya zuba mata cuta kenan.”
“ Mummy nikam naji tausayin ta ne.”
Tsuki taja tana cewa. “ Nata da sauki ai tunda wari kawai take yi.”
Cike da son jin gulma Radiya ta ce. “ Mummy ke kuma me ya faru?.”
Shuru Mummy tayi kafin ta ce. “ Wanda na tura ya kashe Saif ne aka kama daya daga cikin su, to yanzu yana so ya tona min asiri ne.”
Radiya tsoro fal ranta ta ce. “ Mummy turawa kika yi a kashe shi? Kenan dama ke ce kika tura a kashe shi ba’a same shi ba aka samu Sageer.”
“ Bana son munafurci Radiya, daga fada miki zance dan ki tayani jaje shine zaki min halin naki ko.”
“ Anuty Mummy kenan, ai to Wallahi kadan kuka gani duk taku biyun, yaron da bai tare muku komai ba amma kuna neman rayuwarsa, kin hana matarsa ma sukuni, ku jira sakayya.”
“ Zo ki bar min gidana dan ubanki Radiya, har ni zaki na fadawa duk maganar da yazo bakinki, ba albarkaci na kuke ci ba.”
“ Gida kam zan tafi tun da ba na ubana bane, kuma nikam ba ke kike ciyar da ni ba.” Ta karashe tana murguda baki ta wuce daki dan hada kayanta.
Zama Mummy tayi a kan two seater tana yin tagumi. “ Abu duk yana neman dagule min, na rasa ina ne mafita, gashi Fauziyya yau kusan sati bata amsa kirana.”
*BAFFA*
Yau ma kamar kullum suna tsakiyar gida suna faman masifar su.
Surutu suka ji daga waje alamu fada ake, Baffa yaga Inna, Inna taga Baffa.
Kafin ya ce. “ Ki je ki duba waye ne?.”
“ Kana namiji ina mace, kuma kace naje na duba maka.”
Tsuki Baffa yaja ya tashi yana baza babban riga yayo waje.
Fitan shi ke da wuya suka ji muryansa daga waje yana fadin. “ Dan Allah kayi hakuri ku min rai…
*SAHIBA CE✍🏼*